69&70

356 25 7
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*
   

                    69&70

        A cikin ƙasa da abinda baifi  kwana uku ba Alhaji Kabeer yasa aka gyara masa gidansa da ke cikin unguwar Karkasara, duk wani wanke-wanke da goge-goge yasa anyi shi dama gidan sabo ne ba'a taɓa tarewa acikinsa ba, kasancewar haka yasa gidan yayi ƙura da datti  harsai da yasa aka sake fenti, koma da komai sabo ya sa acikin gidan haka zalika ɓangaren ƴan aiki ma anyi musu shi dai-dai misali, kafin su tare sai da akayi saukar Ƙur'ani sannan suka tare cikin kwanciyar hankali, Su Inna Furaira baki yaƙi rufuwa saboda wannan gidan da suka koma yafi wadata akan wancen kuma yafi kayan alatu dukda wancen ɗinma ba baya ba.

       Alhaji Kabeer tun bayan rasuwar Abokinsa bashida wata nutsuwa gaba ɗaya ya rame ya zabge kamar wanda ya yayi jinya, gaba ɗaya abun duniya ya isheshi duk da ya daina ganin abubuwan tsoratarwa da kawo farmaki amma hakan baisan ya samu nutsuwa acikin zuciyarsa ba, ita kanta Kaleesat damuwar maigidanta ba ƙaramin damuwa take sata ba, sai dai ta kauda tata damuwar ta shiga rarrashinsa tana bashi baki har ta samu ya ɗan fara walwala.

     Wata rana suna zaune suna hira amma mafiyawan hirar tasu sai dai yace mata eh, a'a, cikin damuwa ta kalleshi ta ce, " Haba Habeebee har yanxu bazaka cirewa ranka damuwa ba, wanda ya mutu ya mutu sai dai muyi ta yi masa addu'a amma damuwa zata iya haifar mana da wata damuwar " ajiyar zuciya ya sauke yace.

      " Hmmmm Habeebty kenan ni kaɗai nasan abunda yake damuwa, har yanxu rasuwar Alhaji Habibu tana nan tsaye cikin zuciya, ninasan ba shi ne ya kashe Alhaji Abdurrahman ba amma babu yanda ya iya akan dole aka tilasta masa kuma gashi ya amsa a idanun duniya, kin kinsan irin zagin cin mutumcin da mutane suke yi masa bayan ɓullar faruwar wannan Al'amarin, Iyalansa sun zama abun ƙyamata duk inda suka je banda habaici babu abinda ake musu, kaico rayuwa kaico duniya  wai yanxu babu Alhaji Habibu da Alhaji Abdurrahman kaico abinda muka aikata na zunubi da dana sani, yanxu ga duniya da kayan more rayuwarta amma sam babu kwanciyar Hankali, yanxu meye amfanin cigaba da rayuwa inama ace na amince da abinda na aikata da tuni anyankemun hukunci dai-dai da abinda na shuka, kaico babu amfanin rayuwata amma san zuciya yayi tasiri akaina na gwammaci kunyar lahira akan ta duniya " Ya ƙarasa faɗa yana goge hawayen idanunsa.

       Hajiya Kaleesat tuni jikinta yayi sanyi kwantar da Aseela tayi agefen ta cikin sanyin jiki ta ce, " Daddyn Aseela dan Allah ka daina zancen Mutuwa idan kanayi jikina sanyi yake yi, amma ni kaina na gagara yarda da zaɓin da muka zaɓarwa kanmu, ni kaɗai idan na zauna inajin babu daɗin azuciyata amma bazan iya jure rashinka azuciyata ba, Kasan yanda nake ƙaunarka, karka manta ƙaunarka acikin jinin jikina take, gani nake bazan taɓa iya rayuwa idan babu kai ba, amma tabbas bamu aikata dai-dai ba Daddyn Aseela " ita ɗinma goge hawayen fuskarta tayi tana jin yanda zuciyarta take ƙara dagule mata.

    " Banida mafita Habeebty banida wani zaɓi da ya rage mun, ni akaran kaina inajin kunyar sanar da ke wasu ɓoyayyun sirraka na da bakisan dasu ba, sai dai ya zama dole na furta su kodan samun kwanciyar hankalina, *KALEESAT* " Alhaji Kabeer ya ambaci sunanta cikin wata iriyar murya da ita kanta sai da ta juyo ta kalleshi.

     Sakin baki tayi tana kallansa domin idan bata manta ba sun shafe sama da shekara da shekaru bai ambaci sunanta kai tsaye ba, murya na rawa ta ɗaga laɓɓan bakinta ta ce.

      " Lallai na yarda akwai wani muhimmin abu a tattare da kai Daddyn Aseela, amma yanxu a zamantakewa ta da kai akwai wani babban sirri da zaka ɓoye mun wanda bansan shi ba, me yasa? Me yasa zakamun haka? Me yasa zaka ɓoyemun idan kasan duk daren daɗewa dole na san faruwarsa? Yanxu ka mun Adalci kenan a yanayin zamantakewarmu? Dan Allah ka barshi bana buƙatar sauraran komai daga gareka dan ina tunanin rashin jinsa yafi mun alkairi tunda ka kasa gayamun tun farko " Ta ƙarasa faɗa hawaye bibbiyu na zuba daga cikin idanunta.

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now