29&30

436 37 3
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    29&30

        Zaro idanu Alhaji Kabeer yayi cikin tashin hankali ya yana bin bayanta da kallo sai dai tana fita ta ɓace ɓat daga gurin, cen daga bayansa sai ji yayi ankece da wata irin mahaukaciyar dariya mai ban tsoro, ilahirin jikinsa rawa yake a ta ke tsoro ya mamaye cikin zuciyarsa a hankali ya fara karanto duk wasu addu'oin kariya da sani, wayar dake jikinsa ta ko'in kirane ke shigowa danma ya sata a silient amma lokacin daya duba misscall babu adadi ya gani haka nan numbers kala-kala yaci karo dasu, babu kiran da yabi ta kai saboda ba wannan ne damuwarsa ba, gefe ya samu kan wata kujera ya zauna ya rafka tagumi abin duniya gaba ɗaya yabi ya addabi rayuwarsa, cikin zuciyarsa yake faɗin, " dama wanda ya mutu yana iya dawowa ko kuma aljanune suke san haukatani " kamar wanda ya faɗa afili sai ji yayi ance, " tabbas duk wanda ya mutu baya dawowa amma RUHINMU na nan sai ya tabbatar da ya ɗauki FANSA " a firgice ya kuma juyawa sam bai ga kowa ba runtse idanun sa yayi saboda wasu abubuwa da yaga suna gilma masa, yana rufe idanunsa kukan ƙaramar yarinyar ne ya fara dawo masa cikin idanun sa, hakanan sautin muryar tsohuwar na masa amsa kuwwa cikin dodon kunnensa, sai kuma fuskar matsahiyar budurwa dake gilma masa a take wasu abubuwan da suka faru sama da wasu shekaru suka fara masa kai kawo acikin ƙwaƙwalwarsa, yana cikin wannan tunanin yaji wata siriyar murya ta ƙaramar yarinya tana faɗin, " Babban kuskuren kun tafkashi kaida Makusantanka sai dai mun fara ɗaukan fansa daga kan Abokinka kuma Amininka, da sannu RUHIN FANSA zai cigaba da ɗaukan FANSAR zalincin da aka wanzar dashi agaremu kun yanke mana jindaɗin rayuwarmu domin taku rayuwar kun cutar damu cutarwa mai muni, Babban kuskuren da kukayi na ƙara haifo RUHIN FANSA nan da wasu shekaru Ahlinku kuma jininku zasu ɗau matakin da ya dace akanku, koda ka fita daga wannan zargin bazamu ƙyaleku haka ba harsai kun furta abunda kuka shuka da hannunku, Kuma mun bijiro da ƙarfinmu babu wani ɗan Adam da zai iya dagakatar damu, biyu daga cikin RUHINMU sun bayyana ku jira cikon ta ukunmu na nan tafe " ana gama faɗa yaji anƙyaƙyace da wata irin dariya mara daɗin sauraro, da sauri yasa hannu ya rufe kunnuwansa saboda ji yake kamar dodon kunnenshi zai mutu, duk wata addu'a da ya taɓa saninta sai da taxo bakinsa saboda yanda ya tsorata da jin maƙasudin abinda ya sanya shi cikin wannan taskun, sai da yaji komai ya lafa sannan ya cire hannunsa yana dube-duben gefe da gefe, wani irin tashin hankali ne ya shige shi baisan lokacin da ƙwallah ta fara gangaro masa daga idanunsa, yana nan zaune wani police yazo wucewa ta gurin sai da yayi ɗan waige-waige sannan ya zura kansa bakin ƙofar Cell ɗin yana faɗin, " Ranka shi daɗe nace ko kana da lauyan da zai tsaya maka ne?? idan babu akwai wani cousin Brother na yasan aikinsa sai inyi masa magana " Alhaji Kabeer da abin duniya ya isheshi ko kallansa baiyi ba, sai ma cigaba da runtse idanun sa yayi yana zubda hawayen nadama da dana sani, ganin haka yasa Police ɗin sumi-sumi ya wuce dan yana gudun wani daga abokan aikinsu ya ganshi, kamar wanda Aka zabura da sauri ya ɗauko wayarsa wata number yayi dialing sai da ta kusa tsinkewa sannan aka ɗauka daga wancen ɓangaren aka fara magana, " Ur Excellency Ashe kuma haka tsautsayi ya faru wannan lamarin fa sai dai mubi ta ƙarƙashin........ " azafafe Alhaji Kabeer ya katse da, " ka cuceni kai ba Aboki nagari bane Allah ya isa tsakanina da kai ka ɓata mun rayuwata ka ɗorani akan lilan keken ɓera, ka ingizani nayi abunda nake nadamarsa yanxu ashe dama rayuwa zata iya juyamun haka?? Gaskiyar malam bahaushe da yace duk abunda ka shuka shi zaka girba, gashi yanxu fatalwar bayin Allah nan ta fara bibiyar rayuwata har sun fara jefani cikin tasku da tashin hankali, na biyewa san zuciya da ƙwadayin rayuwar duniya na aikata aika-aika mara amfani kaicona tir da abota irin taka tir da kai Allah wadaranka..... " daga cen ɓangaren Abokin nasa ya katseshi cikin jin haushi, " da wani ne ya ingiza ka ko na janyo ka ta ƙarfi da yaji ne?? Inace har gida har cikin Muhallina kazo ka kawo mun kukan akan intaimaka maka, sai yanxu zaka kawo mun maganar banza da wofi kaga Kabeeru kowa yayi ta kansa kaji da bala'in kisan kan da kake ciki, kowa ya iya allonsa ya wanke dan haka kowa tashi ta fishshe shi " yana ƙarasa maganar ƙit ya kashe wayarsa, gaba ɗaya ran Alhaji Kabeer adagule yake dana sani haɗe da nadama ne suka mamaye zuciyarsa, atake yaji tsanar kansa da ta Abokinsa ta mamaye zuciyarsa, lokaci guda kuma yaji tausayin Matarsa da na ƴarsa guda ɗaya gudan jininsa ya mamaye zuciyarsa, tunanin mafarkinsa ne ya faɗo masa zuciyarsa, a raunane ta fara magana, " tabbas gaba ɗayanmu munyi wannan kuskuren amma dan Allah ku gafarce mu dan Allah karku kashemun Khaleesat ita ɗin jinina ce rayuwa ta ce farin cikina ce, ku kasheni ku barta karku maida mun ASEELA marainiyar gaba da baya, Khaleesat ta biyewa buƙata ta ne saboda tana gudun karta rasani dan Allah ku barmun ita Karku kashe ta " yana ƙarasa maganar yana zubda wata irin ƙwallah mai ɗumi, ya jima ahaka yana surutai da hawayen abubuwan da suka aikata, lokaci guda ya fara kai kukansa gurin Ubangiji yana tuba bisa ga abubuwan da ya aikata arayuwarsa wanda ya sani da wanda bai sani ba.

ASEELA COMPLETEKde žijí příběhy. Začni objevovat