25&26

401 31 4
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    25&26

  _ZAKU SHA KURA-KURAI BAN TA CE BA_
           Bayan sallamar su kai tsaye gida kawai suka wuce banda azalzalar Hjy Kaleesat babu abinda yake yi akan su yi su wuce, saboda duk ƙarin awa guda ji yake kamar yankar naman jikinsa akeyi, hankali Alhaji Kabeer bai kwanta ba har sai da yaga sun shiga cikin jirgi, suna nan zaune yaga waɗansu irin halittu na shigowa ta ƙasan jirgin masu mummunar halitta kowanne yazo zai wuce ta sai yasa hannunsa akan bakinsa 🤫 suna yi masa alamar gargaɗi da jan kunne, banda gyaɗa kai ba abinda Alhaji Kabeer yakeyi tun Hajiya Kaleesat bata lura ba har ta kalli Alhaji cikin mamaki ta ce, " Daddyn Aseela lafiya kuwa kodai jikin ne??" baibi ta kanta ba sai ma cigaba da yayi da amsa musu cikin bin umarninsu, mutanen da hallinsu masu rabi ƙwarangwal rabi abin tsoro sun wuce iya tunaninsa, ko kaɗan ya gaza ganin adadinsu ganin abunda Alhaji yakeyi kamar ba na hankali bane ya sa Hajiya Kaleesat ta fara karanto masa ayatulkursiyyu, wani irin bacci ne yaji yazo masa har baisan lokacin da ya jingina da kujera ba tuni bacci yayi awon gaba dashi.

            Ya ɗan ɗauki lokaci mai tsayi yana bacci cikin baccinsa ne yayi mafarkin waɗansu irin ayarin ƙwarangwal sun tunkaro shi shi da Hajiya Kaleesat da wata ƴar matashiyar yarinya da baza wuce shekara huɗu zuwa biyar ba, jan hannunta ya farayi da niyyar guduwa amma sam yaƙi taƙi motsawa daga gurin har ayarin ƙwarangwal ɗin nan suka ƙaraso suka kusa cimmusu, suna daf da ƙarasowa gurinsu shugabannin cikinsu guda biyu suka shata wani layi agaban su Alh Kabeer, wata irin iska suka fara hurowa daga bakinsu wani irin abu na fitowa yana zaftare ƙasar gurin, kafin wani lokaci tuni gurin ya wawake ya zama uban ramin gaske, da sauri yayi ƙoƙarin jan hannun ta dan su gudu, cikin wata irin magana mara daɗin sauraro ƙaramar yarinyar nan ta ce, " Babuuuu wani taimako da zaka iya yi mata domin ita ɗin RUHINMU CE " tana gama faɗa idanunta suka juye zuwa fari tass waɗansu irin surutai ta fara yi ba'a ɗau lokaci ba sai gani yayi Hajiya Kaleesat ta fisge daga hannun sa, cikin ramin ta tunkara gadan-gadan ta faɗa ciki ta kwanta tana rufe idanunta, kamar haɗin baki yaji sun ɗauki wani irin yare har ƙaramar yarinyar kamar masu biya karasu, suna cikin biyawa ƙasar da kanta take gangarowa tana rufe Hajiya Kaleesat, ganin haka yasa ya yunƙura zai faɗa cikin ramin sai ji yayi anƙadandane shi kamar  wanda aka sa sasari aka ɗaure har ƙasar ta gama rufe ta, yana gani haka cikin tashin hankali ya ƙwalla mata kira, " KHALEESATTTT " firgit ya buɗe idanunsa gaba ɗaya hankalin ƴan jirgin yayo kansu, ita kanta Hajiya Kaleesat ta tsorata da yanda taji ya kira sunanta, da sauri rungume mai gidan nata duk atunaninta ko ciwonsa ne yake san tashi, saboda ta lura tunda ya yayi wannan ciwon na farko gaba ɗaya duk a rikice yake, cikin tashin hankali ya fara mata magana yana kuma riƙe ta sosai kamar wani zai ƙwace ta ya ce, " Dan Allah Dear karki tafi ki barni wallahi ke ce ni idan babu ke nima mutuwa zanyi, karki yarda su cutar mun da ke duk wanda ya baki umarni karki bi akan idona suka ce ki shiga rami kika shiga har binneki suka yi......" tunda ya fara magana ta zurawa mai ido ita abun na Alhaji ma ya fara ba tsoro shiyasa ma ta sa hannu ta katse mai maganar da ke fitowa daga bakinsa, batayi aune ba sai hi tayi dumin hawayensa na sauka akan hannunta da ke kan bakin sa, hankalinta ne yayi mummunan tashi asanyaye ta ɗaga kai tana kallan mijin nata muryar ta na rawa ta ce, " Daddyn Aseela hawaye kuma?? idan akwai abinda yake damunka Dan Allah ka gayamun domin na samu nutsuwa,  tabbas na lura kana cikin damuwa haka kawai baza dinga zubda hawaye ba " ta ƙarasa maganar itama tana sha re ƙwallar idonta, yana kallanta yaji ƙaunarta, tausayinta da soyayyarta ba kuma azalzalar zuciyarsa saboda ya kwantar mata da hankali ya ce, " Dear babu komai kawai idan na tuna ko yaushe mutuwa zata iya rabamu sai inji jikina yayi sanyi " sauraren sa ta ke badan ta yarda da abinda yake gaya mata ba, amma shima dan ta kwantar masa da hankali sai ta ce, " akoda yaushe na gaya maka mutuwar bazata zo ta ɗauki ɗayanmu ba, sai dai ta ɗauke mu alokaci ɗaya zan rayu da kai zan mutu da kai muyi rayuwarmu har gidan Aljanna Habeebee " ta ƙarasa maganar tana masa murmushi, Inna Furaira dake kujerar bayansu tana jinsu murmushi tayi saboda soyayya da kulawar da Hajiya da Alhaji Kabeer sukewa junanta yana matuƙar birge ta, kowanne na ƙoƙarin ganin ya faranta ran ɗan uwansa, da haka hirar gari suka shiga shi dai Alhaji binta yake da hirar amma cikin zuciyar sa jinta yake ba daɗi, musamman inyatuno sanda ƙasa ta rufe matarsa har ji yake gabansa na faɗuwa.

          Basu suka sauka a ƙasa Nigeria ba sai kimanin ƙarfe goma sha biyu na rana, tuni dama Alhaji ya sanarwa da Driver dawowar su dan haka suna kauna suka ci karo dashi ya kwashe su sukayi gida, murna gurin Inna Furaira taƙi boyuwa saboda ƴan kwana biyun da tayi har taji kewar su Rakiya da Binta, ita kanta Hajiya Kaleesat wani irin annushuwa take ji na dawowarsu gida Nigeria, agajiya suka fito daga mota aykuwa su Binta cikin murna suka tarbesu suna, " ga Hajiya ga Hajiya Inna Furaira mutanen India ya kuka baro su Ashwariya?? " hararar wasa ta ke binsu da shi tana musu murmushi, Hajiya saboda tsabar gajiya bata bi ta kansu Binta ba tunda ta amsa musu ta wuce cikin gidan, tsaf suka sameshi agyare kamar basuyi tafiya ba, banda ƙamshi ba abinda yake ta shi, kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce ta fara rage kayan jikinta sannan ta shiga ta watsa ruwa, bayan fitowarta Alhaji ta samu zaune abakin gado ya rafka uban tagumi, tashi yayi jiki ba ƙwari ya faɗa toilet ɗin, bayan wani lokaci fito wa yayi lokacin har Hajiya Kaleesat ta fara rama sallolin kanta, shima dadduma ya janyo sai ji yayi daga cen bayan labulen ɗakin ance, " Kabi umarni na farko ka tsallake wannan siraɗin, umarni na biyu zamu baka yanxu, karka sake ga kuma gayawa wani ko wata abinda kaji ko ka gani inba haka ba zamu ɗauke ka daga duniyarku kuma har abada babu kai babu ƙara dawowa hahahahahaha " murya na rawa ya ce, " nabi wallahi nabi babh wanda zaiji " Hajiya Kaleesat dake gefensa ta ce, " Habeebee kai da wa kuka wa kakewa magana?? " wayan cewa yayi ya ce mata, " am dama amm eh dama tunowa nayi da maganar da mukayi da Alhaji Habib to shi ne maganar ta faɗo mun " jinjina kai tayi tana ƙare masa kallo sannan ta ce, " Bansan ka da ɓoyemun komai ba, kuma bansan ka da karya ba amma babu koma Allah ya shige mana gaba " jiki a sanyaye ya ce, " Ameen Dear " duk sai yaji ba daɗi saboda ba halinsa bane komai nasan ta sani babu abinda yake iya ɓoye mata, amma da ya tuno gargaɗin da akayi masa sai ya basar kawai ya tada sallah.

             *BAYAN KWANA BIYU*

     Ƴan uwa har sunji labarin dawowarsu daga India, aykuwa sai turuwa ake ana zuwa duba Aseela da jiki, kusan kullin idan basuyi baƙi huɗu ba mutum shida zasu xo ahaka har suka haure sati guda da dawowa, Alhaji Mamaki ne ya kama shi musammam da yaga Abokinsa har zuwa wannan lokacin bai zo bare ya duba Aseela, wayarsa ya ciro ya kira shi sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauke murna babu walwala, " Hello ya akayi?? " murmushi Alh Kabeer yayi ya ce, " lafiya klau karanka nayi ince lafiya yau satinmu guda da dawowa daga india amma baka koda zo ka duba Aseela ba...... " azafafe Alhaji Abdurrahmam ya katse shi, " ni zaka rainawa hankali ka maidani bi ta cen, ba India ba Allah sa Amitabatchan ka ɗauko, ka manta zambo cikin amincin da kamun ko ka manta yanda muka rabu da kai har kana sai ka kashe ni, ko ka ɗauka banyi report bane shi ne har zaka kirani kamun daɗin baki mtswwwww " sai da ya biga uban tsaki sannam ya kashe.

           Sororo Alhaji Kabeer yayi shi Hajiya Kaleesat suna mamakin kalaman Alhaji Abdurrahman, wani tunani yayi sannan yasa wayar a aljihu ya ɗauki key ɗin mota ya ce wa Hajiya Kaleesat, " bari na je gidan mutumin nawa inji kan zance danni ban fahimci inda maganarsa ta dosa " bai jira cewarta ba ya fice daga fice daga falon.
         Bayan awa biyu da fita Alhaji Kabeer sai gashi ya dawo agajiye ya zaune Hajiya Kaleesat na masa barka da dawowa sannan ta ce masa, " ya kukayi da Abokin naka " idanunsa alumshi ya ce, " wallahi ni banma je gurinsa ba ina fita na haɗu da Alhaji Yaseer muka je gidan gonarsa sai yanxi muka dawo...... " maganarsa ce ta maƙale sakamakon wani bugun tashin hankali da suka ji anayi da sauri ya tashi ya fita zuwa Gate, gaba ɗaya securities ɗin saita bi dugogin su suka yi sannan suka buɗe ƙofar, da fudu suka ga ƴan sanda na shigowa ciki suna Arba da Alhaji Kabeer suka kalli wani matashi da suka shigo tare suna faɗin, " wannan ne " goge hawayensa yaron yayi ya ce, " eh shi ne wallahi shi ya kashe mana mahaifin mu" kafin Alhaji yayi magana tuni sun cacumo shi suna ƙoƙarin sa masa Anƙwa.

    *ALHAJI KABEER KANA RUWA🤣 INAJIN DAƊIN COMMENTS ƊINKU ALLAH YA BAR ƘAUNA.*🥰❤️

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETEOù les histoires vivent. Découvrez maintenant