73&74

356 33 9
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*
   

                    73&74

           Mutumin da ke tsaye mamaki ne ya kamashi najin kalaman Aljani gunguru jikan kunkuru, kallan Alhaji Kabeer yayi yace.

    " Alhaji gaskiya ne abinda wannan hatsabibin ya faɗa? "

    Alhaji Kabeer waigowa yayi yana kallan Aseela suna haɗa ido cikin ƙwayar idanunta yaga fuskar Muneerat a ɗayan ƙwayar idon kuma fuskar   Inna Larai yayi tozali da ita, sunkuyar da kansa ƙasa yayi sannan yace.

     " Tabbas abinda ya faɗa haka ne laifina ne nina biyewa san zuciya gashi yamzu ya kaini ga dana sani "

     Hajiya Kaleesat kallansa tayi da mamaki tace, " Daddyn Aseela kaina ya kulle wai me yake faruwa ne? "

      Alhaji Kabeer da gaba ɗaya jikinsa ya jiƙe da gumi ya ce, " Abinda nake ɓoyewa ne dole ya fito sarari kaico rayuwa "

     Mutumin da ke tsaye ya jinjina kai yace, " Tabbas na fahimci inda zancenka ya dosa, amma ka sani muddin kana tare da gunguru wallahi bazai taɓa barinka ba komin daren daɗewa  sai ya aiwatar da abinda aka turoshi yi gurunku, nayi mamaki da har ya jima daku haka ba tare da ya cutar da ku ba cutarwa mai muni kuwa, idan kuna ganin babu damuwa zan iya taimaka muku da iya abinda ya hore mu na daga sani, amma babu takura inbkwa buƙata shikenan amma ninasan waye Gunguru "

     Cikin sauri hajiya Kaleesat tace, " Dan Allah Malam ka duba girman Allah ka taimaka mana " Alhaji Kabeer ma cikin fuskar tausayi yace, " Malam na tabbata haɗuwarmu akwai wani babban al'amari dan Allah ka taimaka mana " Inna Furaira dake kujerar baya zuru tayi tana kallan ikon Allah, cikin zuciyarta tace.

    " Wallahi dama nasan biri zaiyi kama da mutum abinda nake gani sam basa ganinsa amma gaba ɗaya babu mai lura, to shi kuma Alhaji ko me ya shuka oho? Allah sa dai ba kawunan mutane ya dinga saidawa ba har ya tara wannan uwar dukiyar yauni Furaira dana shiga uku ace ina cin kuɗin haramun na ƴan yankan kai " ta ƙarasa zancen zucin wata ƙwallah na biyo fuskarta.

     Mutumin ba musu ya amsa musu da, " Babu komai amma gaskiya bazan iya binku cen mahallinku ba ƙa'idata duk wani abu da zanyi sai dai ku bi cen muhallina idan ya muku shikenan, ni ina zaune acen ɗan ƙauye ne mai suna Ɗangwauro cen gaban na'ibawa " Alhaji Kabeer najin haka yayi farat yace, " Mun amince zamu bika shigo mu tafi "

      Hajiya Kaleesat jim tayi sannan ta kalli mijinta cikin ƙasa da murya ta ce.

     " Daddyn Aseela anya bamuyi gaggawar amincewa da mutumin nan ba kuwa? karfa yaje ya cutar da mu " mutumin ya amshe zancen da, " Idan har kuna da shakku akaina gwara ku haƙuri tunda ba tilasta muku nayi ba " Hajiya Kaleesat cikin kunya ta ce, " A'a ba haka bane  muje ba damuwa "

   Mutumin baya ya zauna kusa da kujerar Inna Furaira, yana shiga Aseela ta takure guri guda ta hau karkawa take jini ya fara fita dag idanunta da kunnenta Hajiya Kaleesat na shirin taɓa ta mutumin nan yace.

        Ƙyaleshi guduwa zaiyi yanxu zai dawo muku da taku ƴar ta asali, yasan haɗuwarmu dashi bazatayi daɗi ba amma hakanma da yayi ba tsira yayi ba " Aseela ta jima tana ta fuffuka da siddabaru iri-iri sai data jima tana yi sannanta yanke jiki ta faɗi, tafiya suka cigaba da yai mutumin na kwatanta musu hanyar da zata sada su da Ɗan gwauro, har suka kusa ƙarasawa Aseela bata farka ba harsai da suka fara shiga cikin ƙauyikan kwazabniyar hanya ta tasheta, tana tashi ta juyo ta kalli Inna Furaira tai mata murmushi sannan ta kalli mahaifiyarta ta ce, "Mommy ina zamu haka jikin naki yayi sauƙi ne ? " har zuwa lokacin Hajiya Kaleesat a tsorace take amma saita basar ta ce, "  Eh unguwa zamu "

ASEELA COMPLETEΌπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα