57&58

326 31 2
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    57&58

          Ƴan uwan Hajiya Saratu ne suka taso da sauri suka yo kanta yayinda Alhaji Kabeer ya taho da sauri ta tallaɓo Abokinsa Alhaji Habibu, cikin wahalalliyar murya ƙasa-ƙasa ya cewa Alhaji Kabeer, "  Ka isar da wasiyyata ga ƴan uwana da Iyalina domin babu ɗaya daga cikin dangina da yasan nazo ƙasarnan ku sanar dasu mutuwa tun......." maganarsa ce ta maƙale idanunsa suka firfito take jikinsa ya daina numfashi, Alhaji Kabeer rungumeshi yayi yana wani irin gunjin kuka kamar ƙaramin yaro duk wanda yake gurin sai da jikinsa yayi sanyi harda masu goge ƙwallah saboda tsananin tausayin halin da suka ga su Alhaji Habibu sun shiga.

       A ɓangaren Hajiya Saratu kuwa lokacin da ƴan uwanta suka riƙeta kallan ƴarta Sumayya tayi tana hawaye sannan ta ce, " Ni tawa ta ƙare Sumayya nasan duk daren daɗewa Mai Ifritu bazai barmu ba, sai yanzu na fahimci sune suka kashe mahaifinku, ku duba cikin Drower kayana akwai wani ɗan ƙaramin diary zaku samu duk amsar da kuke buƙa.......ta.....da...." daga nan harshen ta ya sarƙe idanunta suka kakkafen jikinta ya saki ta ce ga garinku nan.

        Cikin Kotun nan lokaci guda ta rikiɗa ta koma kamar gidan makoki, banda sautin kuka babu abinda yake tashi, securities ne suka shigo da ƙyar suka yage Alhaji Kabeer daga jikin Gawar Alhaji Habibu, haka suka koma ɓangaren Hajiya Saratu suka ɗauke gawarsu, kai tsaye Asibitin Murtula aka wuce dasu basu wani jima ba akayi duk gwaje-gwajen da ya kamata domin tabbatar da mutuwarsu, bayan wani lokaci aka bawa dangin Hajiya Saratu gawarta.

        Lokacin da aka fita da gawarwakinsu Khaleesat ce ta ƙarasa ta kamo maigidan ta tana lallashinsa har ta samu ta shawo kansa, kai tsaye harbar kotun suka fita kowa da ya dubi yanayin mutanen da suke fitowa daga cikin kotun zai tabbatar da babu walwala afuskokinsu, Kai tsaye gidansu Kaleesat suka wuce gaba ɗaya banda hawaye babu abinda Alhaji Kabeer yakeyi, suna ƙarasawa gida ya ɗauko wayar Alhaji Habibu ya kira abokinsa mai aiki a airport ya sanar dashi halin da ake ciki sai dai yaja kunnensa akan karya sanarwa da iyalinsa, sannan ya ɗora da cewa ya samu yayi musu duk wani abu daya kamata daga wunin ranar zuwa safiyar washegari, Number Yayan Alhaji habibu ya kira cikin damuwa ya sanar dashi mutuwar Alhaji Habibu, sun so suje su amso gawarsa Alhaji Kabeer yace su dakata abari mai ɗakinsa da ƴarsa su ƙaraso inyaso sai ayi masa sutura, da wannan shawara suka tsaya suna tsammanin zuwan Hajiya Aisha Matar marigayi Alhaji Habibu.

           Labarin faruwar al'amarin babu inda bai je ba daga cikin garin kano har sauran maƙotanta, kowa da irin abinda yake faɗa akan Alhaji Habibu da Hajiya Saratu, nan da nan ko'ina ya ɗauka akan cewar Alhaji Kabeer bashi yayi kisa ba sharri akayi masa, bayan sallar la'asar Alhaji Kabeer ne zaune gaban mahaifan Kaleesat suna jajanta masa, bayan sun gama abinda zasuyi cen sashen da aka gyarawa Kaleesat suka koma shima da ƙyar Alhaji Kabeer ya yarda acewarsa ba dacewa bane ya zauna har ya kwana acikin gidan surukansa, su Inna Furaira zuciyarsu fes saboda suma sunji labarin fitowar Alhaji Kabeer hakan ne yasa suke jin farin ciki musamman da kotu ta wanke shi daga zargin kisan kan da ake masa.

       Ƴan uwansa da suka zo domin halartar shari'ar a ranar suka bi jirgi suka wuce cikin farinciki, domin ko ba komai sun huta da fargabar halin da suka tsinci kansu aciki.

        Hajara lokacin da labarin yaje mata tayi farin ciki ƙwarai da gaske atake ta kira number Kaleesat tayi mata murna sannan suka gaisa da Yayan nata, bayan sun gama Kaleesat ce ta kuma karɓar wayar tana mata tsiya akan guduwar da tayi, cikin zolaya Kaleesat ta tambayeta yaushe zata zo, aykuwa tanaji tayi farat tace ita da garin Kano sai bayan wani lokaci, sun ɗan jima suna hirarsu sannan sukayi sallama, waya ba ƙaƙƙautawa haka ta dinga shigowa cikin wayarta haɗe da saƙonnin jaje dana ta'aziyya.

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now