KASAR WAJE 54

994 45 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 107/108

Yusuf na zaune kwata-kwata duniya kamar ta kife masa kira ya shigo wayarsa ya kalla cikin Tsananin takaici ya ansa ganin manajan supermarket ne suka gaisa manaja yace key d'in store d'in qasa kama kai Yusuf yayi sam ya manta bai bawa Sebastian ba muryar manaja ya jiyo yana cemasa maza ka kawo yanzun nan ai badon ka d'auka hutu shine bazamu buqaci abubuwa a store d'inba ya tsinke wayar sanin halin rashin mutuncin manaja yasa shi miqewa ya maida wayar aljihunsa ya nufi gida tabbas key d'in na saman shoglass a palo ya hau taxi ya nufi gidan

Armando suna aiki ya d'an keb'e ganin zuwa yanzu yasan queen ta dad'e da shigowa Toronto ya jefa layinta saidai wayar nata ringing a jakarta shiru ba ansa sau biyu kafin ya hakura ya nufi gurin aikin na Liliana da ke sanye da wani la'anannen rigar bacci da kad'an ya wuce gaban ta ba bra nonon da komai ma gani akeyi tanata banbanqarewa ana d'aukar hoto da video shi kansa Armando wani fitinannen sha'awarta yaji yana fisgarsa ya had'uyi yawu yana kallon tsakanin cinyarta da kamar babu komai tsabar sharasharan da rigar takedashi

Bayan Kamal ya tallafeta kujera ya kwantar da ita ya fara yayyafa mata ruwa a hankali har tayi ajiyar zuciya tana bud'e idanunta akan Kamal hawaye suka sake dawowa tace ka taimakamin muje namasa bayani wlh bazan iya rabuwa dashi ba mutuwa zanyi, yawun baqin ciki kamal ya had'iya lallai abin mamaki hayfa ke maganar zata mutu a kan wani.? Muryarta ya dawo dashi tana furta nasan inda zan iya samunsa ka kiramin taxi pls inje ajiyar zuciya yayi ya miqe zai fita Yusuf da ya iso ganin qofar a bud'e ya qaraso domin sam baima tuna zata dawo gidan da wuri haka ba saidai yana shigowa suka yi karo da kamal da ke miqewa daga gaban hayfa da ke kwance wani irin sukwana zuciyar Yusuf ta qara yi ya kalli hayfa da ke kwance a baje ya d'ago ya kalli Kamal a hankali ya fara takawa zuwa cikin falon hayfa har ta miqe ta tsaya Kamal ya kalleshi ya kalli hayfa yace ki zauna kada ki... Ya kasa qarasawa sakamakon d'an kartawa da Yusuf yayi ta gefensa ya d'an bugeshi kad'an ya qarasa wajen shoglass ya d'auka key ya juya zai fita tayi sauri binsa tana riqoshi tsabar baqin ciki da sabon tsanarta da yaji baisan sanda ya sheqa mata mari ba ya tureta daga jikinsa cikin sa'a ta fad'a kujera tana sakin kuka. Kamal cikin Zafin rai shima ya d'aga hannu zai mari Yusuf, Yusuf ya riqe hannunsa ya sharara masa mai lafiya, Kamal cikin mugun tsana da kishin Yusuf d'in ya furta kasani dacan ni naga dama nabarka ka aureta kuma domin bana cikin hayyacina ne lokacin aurenku amma ina tabbatar maka yanzu bazan sake barin wannan damar ba shiasa na biyota kuma ni zan aureta inbarta tayi aiknta domin aiki aiki ne nagode Allah ko da baka saketa ba yanzu tnda ka furta cewa "kada ta tab'a biyoka koda tasan inda take" wanda hakan ma sakine so ina shirye da aurenta da zarar tagama idda, cikin tsananin takaici da nutsuwa Yusuf ya kalleshi kafin ya kalli hayfa da ke zaune kujera tanata hawaye ya furta " nima yanzu zanyi clearing domin na sauqaqa muku hanyar yin abinda  kuka dad'e kuna so" cikin mugun tashin hankali hayfa ta taso tana riqe qafarsa tace ka saurareni don Allah kar kace komai pls ta qara sakin kuka, kallon kamal yayi kafin yayi ajiyar zuciya yace "kije na sakeki saki d'aya" ya sunkuya ya b'anb'areta a qafarsa ya bar gidan zucuyarsa kamar ta tarwatse wani irin qara ta saki ta kuka da duk qarfinta kamar mahaukaciya ta miqe da gudu tabi bayansa yana shirin shiga taxi ta riqe qofar tana kuka ture hannunta yayi ya kullo mai taxi yaja suka tafi tana gurin tanata kuka kamar ranta zai fita abinka da turai babu wanda ya damu da ita kamal ne ya qaraso ya sunkuya ya tsuguna yana kallon yadda tazama kamar mahaukaciya sam tunda yasanta bai tab'a ganinta cikin tashin hankali haka ba a y'en awanni kawai tazama kamar mahaukaciya sabon kamu a hankali ya furta "hayfa pls is OK kada kisawa kanki wani ciwo" kallomsa tayi da idanunta da suka gama rinewa tace pls kaje inason kasancewa ni kad'ai yanzu, OK yace zan wuce hotel dina amma sai bayan naga kin koma gida tukuna a hankali ta miqe bata masa musu ba ya rakota har gida ta kulle ya yafi badon yaso ba tunani ma yayi zai dawo ya kama masauki nan kusa da gidanta tunda ta kulle qofar sabon kuka ta dire kamar zata mutu hawaye ma ya fara bushewa tana danasanin ranar da tafara ma had'uwa da Armando har tafara aikin model.
Kwanciya tayi lamoo a kujerar tana tariyo komai tanajin tabbas yau ranar tashin duniyarta ne babu rana mafi muni a rayiwarta kamar ranar yau taji qirjinta na wani irin nauyi

KASAR WAJEWo Geschichten leben. Entdecke jetzt