KASAR WAJE 14

1K 46 2
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  27/28

Haka ammah ta daure ta mik'e taje tayi wanka tana fitowa yara na dawowa makaranta laraba tanata hidimarsu

Yaran suka shigo ganin yanayin mamansu suka ce mominmu bakyada lafiya ne?

Murmushi tayi tace ah ah ciwon farin ciki ne nake yi kunji maza kuje kuyi shirin islamiyya sai da yamma zan baku labari mai dad'i

Nan suka fito suna tsalle suka nufi kiching gurin laraba

Tana shiryawa ta sallami laraba ta wuce kabala

Hayfa na aiki duk hankalinta na kan tunanin Yusuf yau sam ya kasa barin k'wak'walwarta

Tanbayar kanta take mai yasa? Yanada mutunci sosai, mai yasa za tayi masa haka? nayi karatun addini na sani a yanzu a rayuwa Shi yafi kowa alhaki da hakkin sani da yanke hukuncin komai a kaina

kiching d'in café ta shiga ta b'oye fara kuka sosai ita bata san ya za tayi ba gaskiya

Yusuf bayan tafiyar hayfa café suka yi waya da aliy yake jaddada masa wlh shima abbansu ya dad's masa jikin na alhaji shamsu sam babu dad'i

Yusuf yace Wlh Aliy na fi kowa jin ciwon alhaji..!

Aliy yace na sani amma kada ka damu IA zai samu lafiya, wai ma nawa ne yanzu ya rage?

kasan ni ko kayi aike ba tanbayar lawyer na ke ba saidai nayi signing kawai

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace 8M ne da 368k..

Aliy yayi ajiyar zuciya yace kayi hakuri Yusuf da abinda zan fad'a amma gsky ne wlh don auren da kayi ne da tuni ka gama biyan naka har ka fara tara kadara a Nigeria

Bawai babu kyaw ba ne auren amma kayi gaggawa...

Ajiyar zuciya Yusuf yayi sam bayaso yaji koda innarsa na kushe aurensa da hayfa Yasir kusan ko yaushe sai yace yayi gaggawa aliy ma haka, shi yana son hayfa kuma ko bashin duniya ya d'auka ba zai tab'a dana sanin yin haka ba sabida ya mallaki hayfa

Aliy ne ya dawo dashi tunaninsa yace kada kasa damuwa kaddara ta riga fata Allah ya tashi kafad'ar alhaji ya baka ikon biyansa kaima ka fara yiwa kanka

Yusuf yace amin na gode Aliy ka gaidamin su Abba

Aliy yace za suji suka yi sallama Yusuf ya kashe wayar ya fad'a tunani

Shi burinsa ma yayi ya sama musu gida su fara rayiwa sosai shi da hayfa tunda yanzu ta sauko su gina rayuwarsu tare

d'an ajiyar zuciya ma yayi yaji yana son ganinta kafin su wuce club dama kuma zaiyi shopping na gida mik'ewa yayi yasa takalminsa ya fito ya nufi café

Koda ammah taga gida sosai gidan ya burgeta su kad'ai babu yawan mak'ota kamar a gidansu na kawo

Sorry na samu mistake na lissafin kid'in da hayfa ta aikowa ammah.

Kallon Luba ammah tayi tace yayi kiyiwa baban walid magana

Luba tace toh masha Allah suka fito yana mota shi da agent d'in gidan

Nan aka gama komai ammah ta biya gida da agency fees Luba na ta mamaki saidai sanin halin zurfin cikin amma luba tace maybe tuni suka samu kudin sayan gidan

KASAR WAJEМесто, где живут истории. Откройте их для себя