KASAR WAJE. 40

1K 48 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 79/80

Bayan sunyi asuba Yusuf yace su d'anyi bacci shi 6:30 zai tashi zuwa aiki.. "Toh" tace cikin yanayin damuwa.. Kallonta yayi a hankali yace karki damu masallaci sai gobe yau ina gida kuma masallaci ma daga next week zan daina kwana sai bayan sallah sabida mutane zasu shiga ittiqaf.. Ajiyar zuciya tayi.. Janyota yayi yai kissing d'inta a kumatu suka kwanta...

Kallon Abdulmalik Kamal yayi yace "Man ka manta dole muna buqatar alls information d'in su ko kuma na shi baturen.. Kama kai kamal yayi yace haka ne ay a akwai web side d'in kamfaninsu a documents d'in ka sake dubawa da kyaw.. Kamal yace "OK" Abdulmalik yace kamar agent ne shi na models kuma manager duka..

Fad'uwa gaban kamal yayi.. Ya kalli abdulmalik yace agent a Toronto d'in? Abdul yace "eh" domin babban manager ne ma international sabida yana aiki har Italy america France da nan Canada inda yake zaune..

Ajiyar zuciya kamal yayi tabbas dole yayi bincike akan lamarin sosai.. Abdul ya dawo dashi tunaninsa yace man bari na koma office akwai documents da zan bawa manager anjuma sai mun had'u latter

Kamal ya ce "OK" latter su kayi salllama.. Kamal ya koma tunaninsa jawo system d'insa yayi ya shiga google ya shigar da sunan "Armando Martinez"..! Ya fara karanta biography d'in Armando inda yaga suna kamfaninsu Armando ya shiga ya fara karantawa yawu na bushewa a bakinsa inda ya gano yaran da Armando ke managing d'insu ya fara karanta sunayensu gabansa ne yayi mugun fad'uwa ganin sunan Hayfa wace da farko tayi register ne da su Armando da ainihin sunanta wato "Khadija Khalid"..! K'urawa hotonta ido yayi hoton wani aiki ne da tayi na Ontario da kayan summer yadda kasan y'ar turawa tayi kyaw tasha laggins da takalminta mai gashi a samansa ya wuce gwiwar k'afarta ga rigar sanyin bai kai gwiwa ba  tasa hula mai kyaw ta sanyi tana zaune kan wani k'aton dutse

Wani irin ajiyar zuciya ya saki ya shiga biography d'inta itama inda kansa ya k'ara d'aukar zafi ganin ansa "single" kama kansa yayi ya fara tunani tabbas hayfa ta tashi da girman kai da buri na domin yasha nunawa Ammah bai gane abinda suke ba  sabida burinsa kawai ya mallaki hayfa har abada shiasa amma ya dad'e da gane yayarya na hayfa ta auri attajiri

Toh amma tanbayar anan shine "shin waye mijin na ta.? Sun rabu ne taje take aikin model..? Ajiyar zuciya yayi tabbas akwai alamar tanbaya a arzikin da gidansu hayfan su kayi domin babu namijin da zai sakarwa mace kud'i haka daga yin aure a jst 2yrs koma 2yrs basu cika da auren ba

Numfashi yaja zuwa Canada ya kamashi yace a ransa yana rufe system d'in bayan ya kwashe information d'in kamfanin su hayfan na Toronto

Tunani ya sake fad'awa dole zai je ya fara bincike akan hayfa da mijinta shi ba  abin farin cikinsa ma rabuwar da suka yi domin baida matsala da aikin dukda yana kishinta amma shima in suka yi aure ci gabansa ne zai shahara a matsayinsa na mijinta murmushi yayi yana godewa Allah da abin ma zaizo masa cikin sauk'i iyayensa dai idan suka ga hayfan ta dawo masa ba makawa zasu hak'ura su k'yalesu.
Murmushi yayi tare da godewa Allah da yayi hak'uri gashi komai yazo cikin sauqi yanzu ya gane wato sun rabu sabida aikinta take zaune Toronto kuma k'ila ta koma karatu tunani yayi ko ya sake neman wasu information gun auntynsa luba sai ya fasa da ya tuna luban na yawan complain na zurfin cikin Ammah cewa ba komai nasu Amman ke fad'a mata ba.. Murmushi ya k'ara shi da ma zaije har can in suka shirya shi da hayfa ya dawo ya sanarwa iyayensa ay musu aurensu baida damuwa idan can take so taci gaba da zama da wannan tunanin ya sake bud'e system d'insa yana duba information na shiga Canada..

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now