KASAR WAJE. 26

947 54 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 51/52

Cikin jin dad'i yace to Bari Salisu ya shigo zai turo Allah ya saka an gode sosai

Tace babu komai a gaida goggon da sauran mutane suka yi salllama

Nan ta Kira Aliy shima tace yazo dama d'akuna uku ne a jere a gidan sai tsakar gida d'aya nata da yara mata d'aya na su Yusuf d'aya na babansu da yana Raye shi take so a gyara a siyowa goggo yalwati katifa da ledar d'aki ayi penti

Aliy ya iso ta masa bayani yace babu damuwa Inna da tun ranar da akayi pentin kika fada da gaba daya akayi ranar ma sabida pentin ya saura

Toh tace suka je d'akin suka gyara ita da aliy da layla

Kafin aliy ya je siyo katifa da carfet jin ance tsohuwa ce shi yanason tsofaffi sannan ta bashi 30k da wayarta tace za a turo accnt ya tura da 30k din.

Tun 7:am Yusuf ya gama shirinsa cikin pencil jeans dark blue da cover shoe da t.shirt na supermarket yana zaune yana cin bread d'in da hayfa ta had'a masa sandwich ta fito da d'an akwatinta a hannu ta zauna gefensa tana kallonsa har ya gama karyawa ta kwashe kayan shi ko kula ma da akwatin baiyi ba ta dawo

d'an kallonsa tayi cike da fargaba ta mik'a masa akwatin dukda ta yage d'an takardar da ke manne da kudin agogon

Kallonta yayi saidai duk ta gama tsurewa sosai ta dake tace gift ne sabida ka rik'a dawowa gareni akan lokaci

Kallonta yake bai gane ba itama ta kasa qara magana...

A hankali ya bud'e ya ga agogon maidawa yayi ya rufe ya mik'e

Rik'oshi tayi tace pls mamana ta bani kuma sai naga yafi kyaw da maza...

Kallonta yayi yace "No" kiyi anfani da abinki...!

d'an rungumoshi tayi cikin salon jan ra'ayinsa tace kenan mamana ba mamarka bace?

Shiru yayi....

Tace shikenna ni mamana tana yawan cemin abin miji na matarsa ne haka nata nasa ne amma tunda b.... Yace is OK

d'an murmushi tayi ta d'auko agogon ta saka masa a hannunsa ya masa bala'en kyaw rungumeta yayi yace "Nagode"!

Itama sosai ta qara rungume shi tace "I love u"..!

Yace "me too much baby"..!

Ya qara mata peck a goshi yace ki kula sosai da kanki in kuka tafi aikin kinji?  
Eh tace tana masa peck a kumatu itama ya wuce domin kuwa ya makara cewa akayi 7:am ta sameshi a gun aiki

Bayan fitarsa ta fara aikin gida da ta dawo aikin Bahrain zata d'auka made tace

Itama 10:am ta gama shiri driver yazo suka wuce.

A kamfani tanata shan harara ta bayan ido a gun Liliana da raudha saidai da sun had'a ido su yi mata murmushi har aka gama launch su da basuda aiki suka wuce gida ita kuma suka fara shirin Wucewa Ontario.

A supermarket an nunawa Yusuf kantar sa ta aiki inda daga customers sun shigo zai mik'e ya d'auka kwandon turawa yaje cashier ya bashi list d'in su yaje ya zab'ar musu kayansu yazo ya zuba ledoji ya raka su dashi har mota ko taxi..

Babban baqin cikin Yusuf shine domin kudinsa yayi auki dole ya haqura da pool yana full tym a supermarket wato 7:am to 9:pm

Inda ya kira Yasir da ke ta jiransa a pool ya masa bayani inda yacewa yasir kada ya bari a d'auki wani ya daure ya had'a duka yana yi sabida kud'insa ya qaru shima

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now