KASAR WAJE. 30

1K 47 1
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

page. 59/60.

Wai duk wannan dad'ewar a b'angaren kayan maza kike...? d'an kunya taji dukda zuwa yanzu ta fara sabawa da tsokanar da ya kanyi mata akan Yusuf..

Kallonta yayi jin tayi shiru yace ni fa tunda naji ki shiru na zab'i kaya da kaina iya abinda zan iya kin gama kema mu wuce..?

Eh tace suka fito suna ci gaba da tattaunawa inda yake tanvayarta wane tym su Yusuf zasu wuce..? Tace kamar 6:am gobe

Yace OK mu zan yankar mana ticket d'in yamma, "toh" tace suka ci gaba da fitowa saida suka shiga mota driver ya kawo hayfa ta d'an kalleshi tace "Ni zan sauka ne a gidanmu"...

Dariya ya d'an saki yace OK queen ni zan sauka a hotel amma dai kada kije kina shagala gida ki manta abinda ya kawo mu.. Dariya tayi itama kafin tace
Ah ah ba  zanyi haka ba..

Yace gud ba'a hada aiki da komai kullum abinda na ke so ki gane kenan sai ki samu nasara mai ban mamaki a rayuwarki ki maida hankali kina aiki tukuru

Ita hayfa dai shiru domin ta rigada ta saba kullum maganar Armando kenan "aiki tukuru"..

Saida suka tsaya kamfani suka k'ara y'an ayyukansu wajejen 5:pm ta fito kamfanin inda tama ki driver ya maidata sanin zasu iya haduwa da Yusuf tana cikin taxi msg d'insa ya shigo..

Hi Baby

Pls tuwo na ke so miyar kuka hop gimbiyata za tamin..? Nagode

Murmushi tayi ba zata masa reply ba sabida yau tanaso suyi dare na musamman na bankwanar Tafiyarsu duka..

Saidai tun kan ta iso gida wani mummunan ciwon mara mai had'e da zazzafa ciwon kai ya Kawo mata farmaki kamar wasa ta fara wani irin numfashi sama-sama a taxi inda shima mai taxi ya d'an tsorata yana tanbayarta ta ma kasa amsa masa har suka kawo k'ofar gidanta da k'yar ta iya fitowa taxi d'in domin mai taxin yaso rik'eta ya taimaka mata ta k'i a dole ya k'yaleta ya kwaso kayanta ya shigar mata har falonta ta sallameshi ya wuce nan ta zube falon wani jiri da taji mai k'arfi ko k'ofar bata rufe ba

Numfashi take fitarwa sosai cikinta na wani irin azababen murd'awa na fitina nan ta fara kuka sosai tana murk'ususu tsakar falon..

Yusuf da suka gama magana da manager da Albert akan gobe ma Albert zai fara sabida yau zaiyi shirin tafiya ya kamo hanyar gida bayan sunyi waya da yasir wai sai after Ishaa zai k'araso ya tsaya ana party a pool zaici bulus

Yusuf na taxi ma Hamzad ya kirashi cewa ya kwana yau gida yayi shiri da kyaw sai ya fito 6:am zuwa masallaci abokan tafiyar na jiransa da motoci sosai Yusuf yayi farin ciki at least za suyi kyakykyawan sallama da gimbiyarsa cike da murna ya iso gida

Sai dai tun kan ya fita taxi hankalinsa ya tashi ganin k'ofar a bude da sauri ya sallami mai taxi ya fito hankalinsa ya gama tashi

Ganin hayfa a sume ga jini da take kwance da sauri ya k'arasa ya rik'ota yana jijjigata yana kiran sunanta ya ma rasa mai zaiyi sai kawai ya ciccib'eta a haka ya nufi waje ya jawo k'ofar yayi sa'a ga wani taxi ya tsaida ya bud'e baya ya kwantar da ita ya shiga ya d'aga kanta ya d'ora cinyarsa yacewa mai taxi ya kaisu asibiti ko inane

Ba  b'ata lokaci a k'arshen layinsu ma ya ajiyesu wani private clinic inda aka shiga da hayfa cikin gaggawa Yusuf ya zauna bencin hankalinsa duk ya gama tashi

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now