KASAR WAJE. 12

1.2K 55 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.   23/24

d'an tsayuwa tayi gefen kujerar da yake ta ce "zan wuce"

Jin shiru ta d'an juya tana kallonsa taga idanunsa a runtse kamar dai bacci ya keyi

d'an k'ara maimaitawa tayi "zan wuce"...

"Toh" yace cikin wata irin murya da ita kanta bata san sanda ta juya sosai tana kallonsa ba sai yanzu ta lura kamar bayada lafiya

d'an k'arawa tayi gabansa tace "baka da lafiya"?

cikin muryarsa mai gard'i kamar ba namiji ba yace "no bacci ke damuna"

"OK" tace ta juya zata fita taji muryarsa "pls ki rik'a kula da kanki"...

"Toh" tace cikin sanyi murya ta wuce cike da tunani

A taxi tunani take sosai ta rasa inda aurensu ya ke dosa ta sani bata sonsa amma ta fara jin alhakinsa na rashin bashi hakkinsa duk kuwa da har yanzu tanada burin rabuwa da shi ta samu shiga jami'a ta gama ta koma Nigeria a lokacin koda anji bata da aure babu wanda yasan yaushe auren ya mutu...

Bayan fitarta Yusuf ya kira Ahmad suka yi fira da shi da qassim sosai akan karutunsu da rayuwarsu a Kaduna.

Koda hayfa ta isa aiki yau tana shiga tsabar hamkalinta baya jikinta ganin ta kusa lati tayi karo da wani bature da ke shirin fita cafen

Tanata bashi hak'uri shi kuma ya shagala kallonta tun daga sama har k'asa

Sai da ta gama bashi hak'uri ta wuce ya dawo hayyacinsa ya juya tuni har ta fara aikinta zai k'arasa shiga ciki yaji wayarsa na k'ara ya d'aga

OK" ganinan zuwa yanzu kuma da albishir mai dad'i da nasara ya tsinke wayar ya bar cafen cike da farin ciki...

Haka hayfa ta gama aiki ta wuce gida su Yusuf da yasir na ta shirin wucewa café ta gaishesu ta wuce d'aki

Yusuf ne ya bita ya shiga tana k'ok'arin cire rigar jikinta ya tsaya bayanta ya zuge mata zip d'in rigar ta fad'i k'asa ya fara shafa mata bayan

Wani mugun numfashi ta ja ta runtse idanunta bata motsa ba yaci gaba har ya d'ora hannayensa kan hips d'inta yana shafawa

Janyota yayi jikinsa yana jan numfashi yana shafa k'irjinta ya kama nipples d'in ta cikin brasia yana wasa da shi

Sun d'an fara nisa Yasir ya fita Yusuf yaji motsin fitarsa ya juyo hayfa yana kallonta idanunsa duk sun canza ita kanta ta d'an rud'e

Had'a kansa yayi da na ta hancinsu na gugan juna yana kallon idanunta yace "Ina sonki" ya mata peck a kumatu ya fito ya yasa takalmi suka wuce

Tunda ya fita hayfa ta zauna gefen gadon ta fara hawaye mai yasa haka yake faruwa da ita? Saidai kamar a mafarki zuciyarta ta tunano mata maganar Yusuf "in kina yawan k'orafi akan tsarin ubangiji zaiyi fushi da ke"...

Shiru tayi tana tanbayar kanta shin waye "Yusuf Suleiman"?

Mai ya kawo shi Canada? 

********

Paolo Santiago Dasilva and Nawfal Fareed Fation Canada..

Armando Martinez ya kalli Bunil Farhan yace

Yarinyar in ka ganta tayi ne kawai ita ce new face d'in da muke nema tun last year

Bunil yace amma kace bak'a k'arama ce baka ganin ba zata iya biya mana buk'atarmu na yanzu ba saidai ko mu d'auketa sabida gaba?

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now