KASAR WAJE. 58

972 56 22
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

*NA*

*Maryam Abubakar Datti*

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 115/116

Kallonsa tayi da kyaw taga kayan cleaners ne jikinsa wato abinda ya kawoshi kenan wani irin qwallah ne ya cika mata idanu ba Yusuf ba har Tiffun da Yasir sosai yanayin ya d'aga musu hankali saidai ga mamakinsu matar da ke yiwa su hayfa hidimar gida ta qaraso tana nuna musu ayyukansu Yusuf ne farkon wanda yabi matar tana nuna masa ya kuwa fara aikinsa sab'anin su yasir da ke tsaye suna kallon hayfa da ta sunkwi da kanta tanata hawaye, Fabiola ta kalli tiffun tace bakusan aikinku bane kuka maidamu TV.? Hararta tiffun yayi ya wuce yasir kam sosai jikinsa ya mutu domin yayi tsammanin da yadda rigima ta kwab'e tsakaninsu tama wuce Nageria lallai yarinyar duniya ce kawai gabanta ya wuce shima suka fara aikinsu babu wanda yake wata magana cikinsu har suka gama hayfa kamar an kafeta tana kujerar tanata hawaye dukda Fabiola na ta rarrashinta da nuna mata koda basu samu matsala ba Yusuf naima yake so zai iyayin aiki ko inama a hankali hayfa ta miqe ta nufi balcony ta zauna ta saki kukan da take ta had'iyewa bayan sun gama aikinsu suka fito suka nufi sauran appartmn wanda daga ciki harda Na su Liliana suma da Raudha saidai anyi sa'a raudha da liliana basunan har sun shiga gari sai wasu su biyu da basusan su Yusuf ba bayan fitarsu fabiola ta bita balcony zata fara magana Hayfa tace kanta na ciwo zata kwanta a dole Fabiola ta hakura ta barta ta fito ta nufi b'angaren su Raudha inda tayiwa mai aikinsu magana suka fito ta bata abu ta fito ta bar appartemn d'in ta shiga gari itama anjuma sunada meeting da manyansu ga auditions sunada shi

Sosai hayfa ke kuka ganin komai take kamar mafarki wai ita da Yusuf ne a wannan matsayin.? Ana gama Gala zata koma Nageria ta sanar musu komai kafin Kamal yaje ya fad'a batasan mai zai fad'a ba suba da yadda yake binta kamar mara abinyi a duniya, kallon Yusuf Tiffun yayi yace "dude ba madam d'inka bace".? Yusuf ko kallonsa baiyi ba yasir ya buge kafad'ar Tiffun yana hararsa domin yasan yaga komai a labarai na rigimar amma yanason sani a gain ganin haka yaja yayi shiru Yasir ya fara masa magana da hausa yace ko dai mu fasa aikin ne wlh ni agent d'in cemin yayi aikin na taro ne A Milan sam ban d'auka na Gala bane kuma naji biyan nasu dayawa zai taimakaw... Yusuf ya kalleshi yayi d'an murnushi yace is OK wa yace maka zai bar aikin.? Yasir shima ya d'anyi nurmushin yace "babu" Yusuf ya miqe yace aiki har qarshe ai ban tab'a b'oyewa wani duk wani aikin da zanyi domin neman halak d'ina ba ajiyar zuciya yasir yayi yana jawo rigar Tiffun suka bat gurin zuwa masaukinsu inda shi tuffun so yake lokacin launch yayi suje aiki ko zaiyi kamu a gurin

Armando ya kalli Kamal yace ya kamata kaje ka duba queen tasan kazo kodai sai anjuma a gun launch.? Murmushi Kamal yayi yace yea mun had'u acan ni kaina ina buqatar hutu tunda na bar Nigeria ban samu hutawa ba , OK Armando yace mu munada international meeting da su yaran after ne launch so da anfara launch zan kiraka OK Kamal yace su kayi sallama kamal ya wuce.

Sai daf da meeting Fabiola ta koma tana lift su Raudha da liliana suna dawowa suka harari juna kowa ya kama gabansa, Lilina ta kalli raudha race tace da gaske sai munyi maganin shegiyarnan mai jan gashi naga sosai tanason saka kanta cikin sabgar da bai shafeta ba tsabar munafunci, ajiyar zuciya raudha tayi tace karki damu ita qaramar alhaki CE ce tunda mungama da uwar gayyar ma ita mai sauqi ce Liliana ta kalleta cikin rashin fahimta tace kamar yaya mungama da uwar gayya.? Raudha tace mai aikina akan Kk ya zo yau da daddare zai sace mana Ita bazai sake ta ba sai bayan Gala babu kuma wanda zai tab'a zarginmu sabida na shafe duk hanyar da hakan zai faru, dariya liliana ta saki tace da kyaw domin in bakiga bayanta ba itace zataga bayanki suna magana suka shiga gurinsu saidai duk abin nan Raudha batasan Yusuf yana cikin cleaners ba domin koda suka iso Milan tanata kiran layinsa da no Milan baya shiga a dole ta hakura taci gaba da sabgoginta

KASAR WAJEWo Geschichten leben. Entdecke jetzt