KASAR WAJE. 39

998 51 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 77/78

Wlh da nine da na huta!.. Kallon fallonsa ya cigaba da yi sai yanzu ya kuma hango kwalin tv can gefe inda da akwatinan hayfa suke da sauri ya k'arasa gurin ya tsuguna ya fara yage kwalin yana mamaki tv ubansu mai kyaw qirar "Samsung" ya fara yaga kwalin yana zaro TVn ya ajiye yana kallo yana k'ara mamakin halin yarinyar gaskiya tana son Yusuf sosai domin wannan duk ta nayi ne domin soyayyar Yusuf d'in.. Zaro wayarsa yayi ya jefa wani number.. Daga d'ayan b'angaren aka ansa

Yasir yace "Albert kace nawa ake had'a Americans Sat.."?

Albert yace $1500..!

Yasir yace OK bari na turo address kamin komai a zo a had'amin..

Albert yace OK kace yau gidanka zan kwana akwai k'wallo 

Yasir yace ina jiranka yau ma party za muyi mun dad'e ba  muyi ba tun na buffday d'in Alexia..

Albert yace haka ne ka kyawta sosai daga supermarket zan biyo kawai domin dama gobe Yusuf zai koma aiki

Yasir yace OK sai ka shigo su kayi sallama.. Yasir ya kira Tiffun ma ya fad'a masa yau party a gidansa ya sake kiran wasu abokansu biyu duk na club..

Yana shirin shiga toilet masu had'a masa satlite suka iso suka fara aikinsu..

Sun gama komai Clara ma ta ci na ta sun fito Hayfa za ta raka ta Yusuf na isowa shima yayi mata godiya suka raka ta tare ta shiga taxi suka juyo suna shigowa falon Yusuf ya bushe yana kallon falon yadda ya cika alhalin shi yasan falon daga 3sitters d'insu sai carfet sai jantar kiching wacce yaga yanzu an saka dinning gefenta juyawa yayi yana kallon had'add'en siririn shoglass d'in mai d'an kwantaccen dogon tv stan an d'ora tvn a kai ya k'ara juyowa yana kallon hayfa da ta d'an tsorata da yadda taga walwala ta k'are masa tunda ya shigo falon saidai ta daure ta b'oye tsoron ta dayawa juyawa yayi ya shiga bdrm rm d'in nan ma mamaki yayi ganin yadda nan ma mak'il ya cika juyowa yayi yana kallnta saidai yanzu ta sunkwi da kai gashi magrib ta kusa kada yayi fushi yaqi cin abinci

d'an zama yayi gefen gadon ya kama kansa.. Yayi shiru.. A hankali ta k'arasa ta shige tsakanin k'afafunsa ta zauna ta kwantar da kanta kan gwiwarsa tana sakin ajiyar zuciya domin har zuciyarta ta tsara mata k'aryar da zata masa ta fara magana.." Kayan gara na nasa wata k'awata ta saidamin wasu ta turomin kud'in shine na maida kayan anan.. Ajiyar zuciya yayi shima kafin yace "mai yasa kafin kiyi haka baki nemi shawarata ba"..? Ba  kya tunanin mutuncina idan kina yin irin abubuwa haka. ? Idan iyayenki suka san kina yin haka mai zasu yi tunani game da ni..?  d'an d'agowa tayi tana kallonsa cikin yanayin son karya masa zuciya tace "pls 4give me dama surprise na so yi maka and ina ina cikin tsananin farin cikin samun gidanmu shiasa..! Shima kallonta yake da tsigar jikinta ya fara tashi gashi ana azumi lol..  k'ara narkar da fuska tayi cikin shagwab'a ta shigar da yatsunta cikin nasa tana kallon kyawawan fararen yatsunsa dogaye ta d'ago tana kallonsa da fuskar yaji neman afuwa tace "pls" ajiyar zuciya yayi kafin yace " zan yafe amma bisa sharad'in daga yanzu duk abinda za kiyi da ya shafi rayuwarmu ki sanar da ni kafin kiyi kin amince"..? A hankali ta girgiza kai, yace "gud" ya d'agota zuwa jikinsa ya rungume ta yana lumshe Idanunsa yana jin yau kamar da ita zai fara bud'a baki ba da abinci ba lol.. Suna gun agogon wayrsa ya fara kiran sallah ay kuwa d'ago ta Yusuf yayi ya fara kissing kamar zai had'iye ta suka ji Yasir na k'wank'wasa k'ofa a hankali ya d'ago har idanunsa sun canza a yace kiyi wanka kiyi alwala ki fito muyi sallah.. "Toh" tace ta mik'e itama duk ya saka mata kasala..

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now