KASAR WAJE. 18

1K 47 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  35/36

Tunani tayi a karon farko bari tayiwa mijinta wani abu special da zai ci da wannan tunanin ta mik'e ta jefa abaya ta yane kanta tayiwa Yusuf text cewa zata je café amma ba zata dad'e ba

Ya mata reply ki kulamin da kanki....!

Koda ta isa café Clara ta samu tana had'a cake da ke ita Clara full tym take aiki suka gaisa

Clara tace "khadija Oga yace wai yau ba zaki zo aiki ba"..

Khadija tace eh na zo karb'an sak'ona ne..

Clara tace ay nayi miki msg nace zanzo gidanki na kawo miki wato bakya so nazo ko?

Hayfa ta d'anyi murmushi tace No ba haka bane zanyi shopping ne shiasa..

Clara tace OK tace ki duba drawer na envelope d'in yana ciki

Hayfa taje ta jawo ta d'auka ta kalli Clara tace tnx zanje ina sauri mu yi waya anjuma

Clara tace OK bye..

Shopping hayfa tayi musu sosai da duk kud'in aikinta bata san ma nawa bane sai dai inta d'iba kaya taga ta biya kud'in ya saura ta koma haka tayi ta yi har kud'in suka k'are duka

Ta saya Irish da d'anyen nama da vegetables ma ta nufi gida

Taxi na ajiyeta Yusuf da Yasir na isowa suma tsayiwa suka yi duka suna mamakin ganinta da ledoji dayawa na cefane

Yasir ya d'an kalli Yusuf yace bari na duba Amjad wani mak'ocin yasir ne balarabe yayi haka ne don ya bawa hayfa da Yusuf sarari

Yusuf yace "OK" kawai idanunsa na kan hayfa da itama na ta na kansa..

a hankali yazo ya wuce ya shiga gidan ya barta gurin

Jiki babu k'wari ta fara kwashe kayan ta shigo gida ta ajiye ta koma ta kwaso sauran ta gama shigo da kayan ta kulle gidan ganin baya d'an falon ta nufi d'akin

Fuskarsa babu walwala yace "kayan waye wannan"?

cikin tsoro ta kasa bashi ansa ya daka mata tsawa ....

Tace na mu...!

Yace na baki kud'i ki siyo?

Shiru tayi...

Yace da ke nake magana...?

Tuni idanunta har sunyi k'wallah tace "kud'in aiki ne aka bani a café shin... Ya katse yace na ce ki rik'a yin wani abu a gidan nan?

Kuka ta fara....

Baya son jin kukanta a hankali ya k'arasa har inda take tsaye ya rik'o hannunta suka zauna bakin gado ya d'ago fuskarta yana kallonta yace "mai yasa kika yi haka bayan ni ke da nauyin yi...?

cikin kukan tace nayi ne sabida na faranta maka rai kuma ay aikinka ne ka bani....

Bata tab'a yi masa magana mai dad'i ba kamar yau,
d'an murmushi yayi yace "Nagode"...!  amma nafi so ki rik'a anfani da kud'inki wajen k'ananun buk'atunki na kanki da ni bazan iya yi miki ba kinji...?

Shiru ba tace komai ba...

Yace magrib ta kusa ba muje muyi alwala ya mik'e tana zaune ya shiga wanka ma yayi yayi alwala ya fito da tawul a k'ugunsa yace kije kiyi alwala kizo muyi sallah

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now