KASAR WAJE. 23

1.3K 51 3
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  45/46

Itama tunani ta d'anyi ta kalleshi cikin shagwab'a da nuna bata san akwai wani a gurin ba bayan su tace "pls ka ci wani abu ko kad'an ne"

k'in d'agowa yayi ya kalleta Yasir kuwa ganin kallon da hayfa ke yiwa Yusuf yasa da sauri ya fara cin nasa ita kuma taqi tashi tana kallon Yusuf

Yasir ya gama ya d'auka take away da ta musu yace "madam mun gode" ya kalli Yusuf yace ni zan wuce sai ka k'araso...

Yusuf ma mik'ewa yayi duk da hayfa ta kusa rinjayarsa amma ya dake dole ya hukuntata kafin ya sakko....

Yana mik'ewa tuni Yasir yayi waje abinsa shima Yusuf yana k'ok'arin binsa itama ta mik'e ta rungumoshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayansa

Sosai yake jinta amma ya dake yace "aikin nan da shi na dogara ko so kike a koreni"?

d'agashi tayi jiki babu k'wari bai ko juyo ba ya wuce abinsa...

Bayan fitarsa ta fara gyaran wurin tare da tunanin mai zata shirya masa kafin ya dawo su shirya tana cikin tunanin tana aikin cikin gida wayarta ta fara ringing ta shiga d'aki ta d'auka ganin Armando ne ta ansa

Queen yaya kike? Yaya gajiya? Yaya jikinki?

d'an murmushi tayi tace "lafiya"...

dariya yayi yace "yaya mijinki"..?

d'an shiru tayi kafin tace "yana lafiya"..!

Yace yawwa albashinki duka biyu sai aikin da za kiyi na tallan wannan balaraben na Bahrain munyi dashi kudinki $100000 sannan na aikin da kika yi jiya $150000 na tura duka $250000 a accnt d'inku na Nageria sannan kiyi k'ok'ari ki d'an d'auki hutu a café dama nayi masa magana yace babu damuwa sabida aikin larabawa akwai wahala kinga hijabai ne zaki masa tallah amma kuma yace zaayi shotting ne na video kina yawo kad'an a gari da hijaban to munyi zamu je har Ontario da Cubec can arewacin Canada da d'an nisa da nan Toronto don haka kiyi k'ok'ari ki bar café ki huta iyakarki kamfani exercise kinji?

d'an ajiyar zuciya tayi tace "toh"

Yace sannan shima hubby d'inki kada kuyi wasa dayawa a kwanakin nan hakan zai janyo miki yawan kasala da nauyin jiki kin gane wannan qa'idar aikin nan kenan in kanada aiki a k'asa baka wasa dayawa kin gane ay

Ajiyar zuciya ta k'ara yi tace "toh" yace ki kula da kanki sanann akwai gift da bunil ya Baku ku duka agogone kamfanin swatch suka mana discounts saidai duk da haka yanada tsada dayawa bansan ko zaki iya anfani dashi ba yanzu ko kuma zaki ajiye kuma mixed ne ma'ana maza da mata

OK tace Nagode yace "kizo kamfani anjuma kiyi signing d'in contract d'in Bahrain sai ki dawo da sauri sabida ni gobe zanyi tafiya Milan kinsan muma har mun fara shirin Gala

ajiyar zuciya tayi tace "pls kasa driver ya kawomin nayi signing bana son fita yau"..!

Dariya yayi yace da kyaw hubby na gida kenan babu fita ko...?

d'an dariya tayi tace ah ah baya nan bana jin fita ne yau

Ajiyar zuciya Armando yayi yana tunani sosai hayfa ke burgeshi yadda sam aikin models bai sanya ta canza ba dukda yawan kud'ad'e da shahararrun mutane da ta fara had'uwa da su amma har yanzu wannan jan ajin da ya ganta da shi tun ranar da ya fara had'uwa da ita yana nan amma yanzu ya qara gane hakan na da nasaba da yadda take girmama aurenta, ajiyar zuciya yayi yana qara mamaki y'ar k'aramar yarinya amma tasan mutuncin kanta da na mijinta... Hayfa ce ta dawo dashi tunaninsa

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now