KASAR WAJE. 50

1.6K 56 3
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  99/100

Jirginsu na sauka Abuja ko b'ata lkc ba tayi ba wajen d'aukar shatar mota zuwa kaduna..

A kano Innarsu Yusuf ke yiwa goggo Yalwa bayanin rasuwar ta gidansu Hayfa inda goggon tace amma yaran zamani basuda hankali yanzu surikinsa ya rasu sai yau zai sanar da mu maimakon tun narar ma a ce da mu akayi janaza

Itadai Inna bata ce komai ba haka goggon tayita fad'a tace shi Isuhu na lura muguwar kai gareshi kamar ta Inzo Haru su baka sanin cikinsu toh yanzu yaushe zamu tafi..?

Inna tayi ajiyar zuciya tace Na kira Aliyu shi zaizo ya samo mana mota sai mu tafi in muka shiga kadunar mu tsaya mu d'auka su Qassim  mu je gaba d'aya

Goggo tace eh hakan ma tunani mai kyaw ne sai mu tashi gobe In Allah ya kai mana rai.. Inna tace IA suka ci gaba da hirarrakinsu na wasu al'amuran rayuwa inda goggon ke cewa Layla ta fiya yanga samari suyita zuwa gurinta tana qin fita ita dai inna bata ce qala ba sanin cewa Layla ta fad'a mata sai ta samu admission zata fara hira da ko waye lokacin hankalinta yana kwance tasan karatu zata fara kawai ..

Koda suka iso Kuse road sosai hayfa ke mamaki ganin tun daga nesa mutane ne a qofar gidansu cike

Toh rayuwar kenan ta zamani indai abu ya faru gidan masu kud'i ko an sansu ko ba'a sansu ba  za a je musu bare nan Ammah na gaisawa da mutane sosai game kyawta lokacin azumi haka tayita rabon abinci da kud'i wannan dalilin yasa nan da nan ta shahara a area d'in kamar ta shekara 20 a kabala

Hayfa ganin cikowa tayi yawa tace mai mota ya shiga da ita har cikin gidansu inda ya wuce dama gate d'in an barshi ne a bud'e suka shige mai motar yayi parking d'an nesa da mutane ya fito ya zago ya bud'e mata a hankali ta sako qafarta waje duk jikinta ya qara sanyi na qara tabbatarwa da tayi tabbas daddynsu ya bar duniya wallet ta d'auka ta sallami mai mota ya wuce mai gadi ya fara shiga mata da kaya tana takawa a hankali ana gaisheta tana ansawa tana wucewa mominsu kawai ta ke so taje ta gani..

Falon ma maqil yake da jama'a wasu dangin babansu wasu bata sansu ba ta fara gaishesu ana mata sannu da zuwa ta gama da su ta nufi saman

A hankali ta Ke shiga d'akin da ke cike Luba na zaune kusa da Suwaiba Luba ta qurawa Hayfa idanu ganin yadda hayfa ta koma tsaf baqa amma kamar haihuwar turai a hankali take ratsa mutane har ta isa gaban ammah da ke zaune kamar zautacciya ta fad'a jikinta tana sakin kuka

Ammah da tun ranar rasuwar bata qara hawaye ba  sai yanzu akaga tayi ajiyar zuciya ta fara hawaye

Mamaki duk d'akin keyi banda suwaiba domin suwaiba tasan yadda ammah ke tsananin son hayfa don haka ganin hayfan ne ya sanyaya mata zuciya taji dama

Sosai ta qara sakin kuka suka fara tare tanayi ammah nayi babu mai bawa wani haquri sun dad'e kafin aka fara lallashinsu da nasiha inda da kyar suka yi shiru suka koma hawaye babu gunjin kukan..

Luba ce ta miqe a hankali ta ratsa mutane ta fito ta shiga wani d'aki a gefen na ammah kamar d'akin hayfa ne ta kulle ta jefa Kira..

Yana Office aiki ya masa yawa domin ya koma CBN saidai yanata bibiyar aikin project d'insu hayfa da Abdulmalik

Kallon wayarsa da ke ringing yayi kamat bazai d'aga ba ganin Auntynsa ya maza ya d'aga baiyi magana ta furta "ta iso yanzu"..!

Ajiyar zuciya yayi yace yanzu zakiga alert na 100k ma namiki qarin 50k akan alqawarinmu, baki ta washe tafara masa godiya su kayi sallama ya fara tunanin zuwa da yamma sannan dole ya bita ya san movement d'inta a Canada domin a yanzu bayaso su b'ata lokaci wajen yin aure..

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now