KASAR WAJE. 6

1.2K 58 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  11/12

Mugun harara ta masa ta rasa mai zata k'ara ce masa lura da tayi shima mugun jiji da kai ne dashi

Mik'ewa yayi ya k'arasa har gabanta yana kallonta yace "sannan ya kamata ki gane ni ba saurayinki ba ne mijinki ne so ki gyara takunki don bazan d'auki iskanci ba ko kad'an ya wuce d'akin yaje yayi wanka ya saka kaya ya wuce tana tsaye inda ya barta

Sai bayan fitarsa ta zauna gurin ta fara hawaye sosai mai yake faruwa da ita? Sam babu wanda ya tab'a k'ask'antata kamar haka iya tsawon rayuwarta kuku ta fashe da shi sosai

Nigeria

Kamal na office yaji kansa ya sara masa nan ya fara tunano hayfa sosai ina take kuma mai ya faru da ita?

d'an ajiyar zuciya yayi sosai yake matuk'ar son hayfa zaiyi komai domin ita tunani ya koma na ranar da ya fara ganinta sunje gaida mamarsa lokacin haihuwar k'aninsa ita da aunty ammah da k'anwar mamansa Aunty Luba lokacin hayfa na jst 14yrs tana js2
Tunawa yayi da yadda yayi ta korar masoyanta ba tare ma da saninta ba ya tuna yadda suka b'ata kwatakwata shi da abokinsa Faisal babansa ambassador ne a dalilin Faisal din ya kamu da son hayfa

Shiru yayi yana kiyasta irin son da yake mata mara iyaka yana tashi office zai wuce gidansu ya dubata da haka ya ci gaba da aiki cike da begen hayfa.

ammah na kwance tana tunanin inda zata tura laraba ta samo mata caji ta nema hayfa ganin sun kwana babu nepa ita kuma ta sayar da generator d'inta wajen hidimar biki ga daddyn yara tun kan ta tashi ya fita a dole ta koma ta kwanta tana jiran zuwan laraba domin tasan hayfa anacan ana amarci kila ma sun bar kasar da sunje yawon kasashen duniya honeymoon, d'an murmushi tayi tana k'ara godewa Allah da ya cika musu burinsu cikin sauk'i da rufin asiri da haka ta koma ta kwanta yara duk sunje makaranta.

Hayfa tasha kuka sosai kusan 2hrs babu d'an adam da ya tab'a sata kuka kamar haka sai Yusuf tabbas zata rama kuma dole kasuwar ta watse tunda k'arya ya musu shi ba mai kud'i bane to ita da bata da waya ya za tayi tayi magana da mominsu?

Mik'ewa tayi a hankali zata shiga d'aki saidai cikin mamaki ta hangi wayar Yusuf a gefen kujera da alama mantawa yayi

da sauri ta k'arasa ta d'auka ta kunna haske taga babu wani security code ko Patten a wayar don haka jikinta na d'an rawa ta fara shigar da number aunty ammah

Saidai cikin rashin sa'a wayar na kashe tayi Ya kai sau biyar a kashe da saura ta fara shigar da na sa'idu mijin ammah wanda suke kira da daddy ita da yaransa da ke ta haddace number ammah da nasa da na kamal da na k'awarta salma baita

Jefa kiran tayi ya fara ringing tayi ajiyar zuciya

Daddy na zaune shagon surukinsa yazo gaisheshi da ciwon k'afa wayarsa ta fara ringing ya d'aga

hayfa ta masa sallama ya ansa ta masa tanbaye-tanbaye da kowa ya mata ban gajiya tace

Daddy mominmu fa? Na kira layinta baya shiga

Yace eh mun kwana babu wuta har yanzu kuma generator yana gun gyara domin haka ammah ta fad'a masa

Ajiyar zuciya tayi za tayi magana yace ina gurin baba ne gashi ki gaisheshi ya mik'awa babanta waya,  Sallama tayi a hankali ya ansa

Tace baba kuna lafiya? Yace lafiya lau auta!

Yace kin isa lafiya ko? Eh tace tayi shiru...

daddy ya mik'e yad'an yi nesa da tunanin k'ila hayfa suyi magana ta d'a da mahaifi da babanta

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now