KASAR WAJE. 5

1.2K 64 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 9/10

Bayan ya gama shiga mata da akwatinan ya fito falo tana inda ya barta tana k'arewa falon kallo fuskar nn sam babu annuri

babu komai sai wata siririyar 3sitters da k'aramin carpet sai hanger na katako a manne a bango na rataye jacket da jaka in mutum ya dawo gida ta juya taga y'ar k'aramar kanta da aka zagaye da k'aramin fridge manne da gas mai burnner biyu sai kanta layi d'aya a sama d'auke da y'an k'ananan tarkacen kiching

Wani irin takaicine ya cika zuciyar hayfa wai nan akurkin waye ya kawo ta

Muryarsa ta jiyo "muje kiyi wanka kiyi sallah kici abinci sai ki huta"

A dole ta bishi suka shiga d'an bedroom d'in mai kama da d'akin kiwon kaji babu ma hanyar da zasu wuce ta shiga ciki a dole ya kwashe akwatunan ya dorasu kan gado wani kan wani cikin tsananin b'acin rai hayfa ta wuce ta shiga bayin

Ganin haka Yusuf ya saka akwatunan cikin d'an wardrobe d'in wani kan wani guda shida tunda dama shi akwatinsa d'aya ne k'arami wasu a dole ya dawo dasu falo sabida babu guri a bdrm falon ma babu guri

Kiching d'in ya tsaya ya d'ora shinkafa sannan ya fitar da fresh nik'ak'en kayan miya yayi mata stew da sardin kafin kace me har falon ya gauraye da k'anshi ya zauna ya fara tunanin yanayin da take masa tunda ta iso kamar ba ita ta nace masa ba saidai a k'arshe yace k'ila gajiya ce zata warware

Bayan hayfa ta fito wanka ta zauna gefen gado duk ranta a b'ace a dole ta bud'e d'ayan akwatin dake gefen wardrobe ta fito da wata rigar shadda ta saka bata shafa komai ba ta saka hijabi ta fara sallah d'an surk'ukin guri a gefen gadon ganin yadda ya bar dardumar ta gane nan ne gabas

Bayan ya gama girkin ya zuba a plate ya jera ya yanka mata fruits a wani plate da d'an k'aramin drink na roba ya kai mata har d'akin

Mugun kallo tabishi dashi ta cire idanunta..

A hankali ta tsinci muryarsa "ki daure kici sai kiyi baccin gaba d'aya ki huta"!

Banza tayi dashi saidai gaskiya tanajin yunwa don haka ya bar mata ya dawo falo!

A dole ta daure ta d'anci abincin ta sha fruits sosai domin dama ita mai son fruits ce

Bayan ta gama ko kwashe kwanukan bata yi ba domin haka ta saba a gidansu ta karkad'e gadon tayi kwanciyarta ta runguma da fillow

Yusuf jin shirunta yayi yawa ya lek'a ga mamakinsa ya ganta gado tanata bacci hankali kwance

Tsayuwa yayi yana kallonta kusan 5mnts ya kwashe kayan ya fito yayi shiri shima ya kwanta falo dukda kujerar a takure yake babu fad'i sannan tsawonsa yafi kujerar.

da asuba bayan tayi sallah ta sake komawa saidai sanyi ya addabeta ta fito da wata abayarta ta lullub'a ganin ko arzikin bargo Yusuf baida

Sosai take tunani sannan ranta a matuk'ar b'ace wai mafarki ta keyi ne mai yake faruwa da wannan guy d'in?

Shima Yusuf dama da yayi sallah yake fita aiki sabida train yafi sauk'in kud'i akan taxi in kuma baka fita da asuba ba sai kayi missing train

Akwai bread da d'an abubuwa na abinci don haka ya rubuta mata d'an note "ina fata kin tashi lafiya?" Na wuce aiki.

Yana aiki yana tunani dole ya nema wani aiki sam in ba haka ba bazai kai labari ba

Yasir yazo yana kallonsa yace wai mutumina kwana biyu duk ka zama wani iri har yanzu akan yarinayr ne?

KASAR WAJEKde žijí příběhy. Začni objevovat