KASAR WAJE. 36

964 55 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 71/72

A hankali ya fara bud'e fayell d'in yana dubawa mugun fad'uwa k'irjinsa yayi ganin sunayen masu project d'in "Armando Martinez da Khadija Yusuf Suleiman"..  Shiru yayi na mintuna yana tunani saidai ya kasa fahimtar abu d'aya "Hayfarsa sunanta khadija Khalid, wannan kuma khadija Yusuf Suleiman".. d'an d'aukar wayarsa yayi ya lalubo wani number ya jefa kira.. Daga d'ayan b'angaren aka ansa

..Yarona na kaina ya kake..? Kamal ya ansa lafiya Aunty, pls Aunty wani abu na keson tanbayarki..

d'an dariya tayi tace Allah yasa na k'aruwa ne kud'i nake nema inason canza mota.. Dariya yayi yace Aunty wai dama maganar canza motar nan tana nan har yanzu..? Langwab'e murya tayi tace to ba kace sai nx year zaka canzamin ba ni kuwa yanzu nake so sabida Ammah tace na kawo jst 1.800 ta bani BMW d'inta wai tayi order sabo kasan yanzu tanada Range Rover ne.. Ajiyar zuciya yayi yayi tsaki idan Aunty Luba na bashi labarin arzikin mijin hayfa ji yake kamar ya had'iye zuciya ya mutu ko da yake shima ay yana dab da komawa aiki a CBN kuma yayi alkawarin yana komawa ko ta wani hanya sai ya dawo da hayfa gareshi.. Muryar Luba ya dawo dashi tunaninsa.. Ina jinka mana kuma kayi shiru.. Ajiyar zuciya yayi yace yanzu nawa kika had'a na sanja motar..? Cikin zumud'i tace na saida tawa 700k sai 200k da baban yara ya bani sai loan da na ansa a office 300k.. Yace OK za muyi agreement yanzu zan cika miki sauran 600k d'in bisa sharud'a in kin amince.. Da sauri tace ko meye sharad'in na amince..

Murmushi yayi yace "OK" da farko menene sunan mijin hayfa..? Ko b'ata lokaci ba tayi ba tace "Yusuf Suleiman".. Sosai hankalinsa ya tashi.. Ya sake daurewa yace ko hayfa ta zo Nageria kwanan nan..? Da sauri tace eh ay jiya ma ta koma nima ko had'uwa ba muyi ba yayarta tace wai aiki tazo na btaimakawa mabukata ann kauyukan kasuna to tayi tafiya kuma kasan halin hayfa dama ya lafiyar kura bare tayi hauka domin girman kanta k'aruwa yayi sabida tsabar wulak'ancinta babu inda taje gaida kowa har ta bar garin nan wai duk yadda mu ke ni da yayarta amma ko gidana bata zo ba.. Ajiyar zuciya yayi yace.. Shikenan Aunty bari na barki za kiga alert yanzu sannan sharad'i na k'arshe kada ki bari Mommy tasan munyi wannan maganar fa pls.. Cikin zumud'i tace ko da wasa da ke ita da Kamal ba wani tazarar bane tsakaninsu dayawa shiasa suke yi kamar sa'oi nan suka yi sallama tana ta shi masa albarka.. Ko minti hud'u basu yi da sallama ma ba  taji alert ta daka tsalle tana neman layin Ammah domin motar ta kai 3m kawai kusan kyauta ammah ta bata shiasa ba tason tayi wasa da damarta bugu biyu ammah ta d'aga wayar

Kina gida..? Ammah tace eh saidai ina shirin fita.. Luba tace bari nayi miki alert yanzu.. Ammah tace OK ay motarki na ajiye kinsan tuni na daina using zan barwa laraba key in kika zo sai ki ansa.. Godiya luba ta fara sosai kafin su kayi sallama ammah na murmushi sabida ita wannan shine dream d'inta tuni ta rik'a kyawta irin ta manya.. Lol Ammah duniya

Tunda su kayi sallama da Luba ya fad'a tunani shin waye Yusuf Suleiman..? da ya rabashi da farin cikinsa Idan kud'i yake tak'ama dashi to zasu zuba daga yanzu shima ya sha alwashin ko zai rasa k'arshen kobonsa zai dawo da hayfa gareshi tunani ma yayi tunda Daddynsa ya gama masa komai na komawa CBN to zai koma nx mouth dama shi yak'I cewa sai nan da six mouth da haka ya gama duba fayell yana mamakin gurin da suka saya har 130M lallai sai yayi da gaske ya tabbata dai hayfa na sonsa kud'ine ya rud'i y'an uwanta suka mata dole kuma a wannan karon babu mai taka masa burki har sai ya dawo da hayfa gareshi..

Sai wajajen 4:30am ta d'an bud'e idanunta a hankali Clara na kujerar d'akin tana bacci a hankali taci gaba da bud'e idanunta har ta bud'e gaba d'aya saidai kanta ya mata nauyi sosai ta fara d'an kalle-kalle inda ta hango Clara na bacci tayi ajiyar zuciya.. Ko kad'an bai k'ara runtsawa ba tun bayan da Clara ta tasheshi joyo motsin su mahfuz yayi suna sahur inda yaji ana k'wank'wasa masa k'ofa a hankali ya mik'e ya bud'e mahfuz yace "kazo muyi sahur.. d'an jimm yayi tabbas yana jin yunwa saidai baya jin zai iya had'iyar wani abu amma ya daure ya cewa mahfuz bari yayi brush yana fitowa..

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now