KASAR WAJE. 34

942 57 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 67/68

Yace ban tab'a baki labarin asalinki ba sabida ganin yadda y'an uwanki suke k'ok'ari a kanki tun tasowarki amma a y'an baya-bayan nan sosai na ke mafarki da kakanki wanda tabbas nayi masa alkawari bayan aurena da mahaifiyarki cewa idan har muka samu zuri'a zan sanar da su komai na daga asalinsu wanda ya rok'eni sosai akan kada na bari zuri'arsa ta k'are ba tare da mun nemo koda tsatson y'an uwansa ba ..

Kakanki Sunansa Haruna amma yace ainihin sunansa "Inzo Haruna"  yace su shida ne wajen iyayensu maza biyar mace d'aya buzaye ne na Niger inda suna zaune wani k'auye na marad'i y'an ta'adda ne suka dami k'auyen sosai suna musu satar rak'uma da k'ananan dabbobi daga k'arshe suka fara kashe mazaje suna aure musu mata sannan suna yiwa yaransu mata fyade suna d'aukar yaransu maza suna koyar da su ta'addanci wannan dalilin yasa mahaifinsu kakanki ya yanke shawarar gudu tare da iyalinsa inda ya yanke hukuncin shigowa Nigeria.

Koda suka shigo Nigeria sai motarsu ta samu matsala a wani k'auye mai suna "dogon daji" can a sokoto saidai bayan motarsu ta tsaya tasha ana gyaranta duk yunwa da gajiya ya damu kakanki da iyayensa da y'an uwansa saidai su ganin guzirinsu da kud'insu ya k'are duk suka daure a yayinda kakanki ya tsananta rigimar yanason cin abinci wanda hakan yasa y'an uwansa suka far masa sunata fad'a na sangartarsa da ya saba ya manta halin da suke ciki na halin tafiya.. ana haka duk y'an uwansa aka gama gyaran mota suka shiga inda kakanki ya hango wasu masu saida abinci ya bisu.. Kamar da wasa y'an uwansa suka fara nemansa mota zata tashi domin dama babansu burinsa su yi masauki Malumfashi sabida akwai mutumin da ya sani a can

Saidai babu shi babu alamunsa haka suka sauka mota suka bazama nemansa hankali a tashe mahaifiyarsa na ta kuka da yayarsa a k'arshe haka dare yayi musu.. A yayinda shi kuma bayan ya k'oshi ya dawo saidai wayan babu danginsa babu motarsu haka yayi ta kuka wani mutum ya ganshi a tasha ya tanbayeshi dama ina zasu je da dangin nasa yace masa malumfashi mutumin ya saka shi a motar malumfashi ya wuce da nufin ya Gano danginsa.. Koda ya isa malumfashi haka yayi ta garari a tasha har kusan magrib Allah ya had'ashi da wani bawan Allah da ya d'aukeshi zuwa gidansa shima mutumin ainihinsa d'an Niger ne a Niamey saidai haka suka yita neman dangin kakanki shiru kamar da wasa lokaci yayi ta tafiya babu wani labari inda shi kuma ya nace cewa tabbas babansa malumfashi yace zasu zo gurin wani mutum da haka shekaru suka tafi sosai kakanki ya fara makaranta ya gama tare da yaran mutumin su biyu musa da tanimu haka suka tashi tare inda suke zuwa kasuwa aiki shagon wani attajiri da haka Allah ya k'ara bawa alhaji haihiwa inda aka haifi Takwararki "Hadiza" bayan hadiza na da shekaru 15 babanta ya yanke hukuncin had'ata aure da kakanki sabida kwantar masa da hankali akan damuwar rashin gano danginsa har wannan lokacin da haka suke zaune suna rayuwarsu a nan kusa da gidan iyayenta inda suma yayyunta ko wannensu yayi aure saida suka shafe 8yrs kafin Allah ya basu haihuwa aka haifi mahaifiyarki tun bayan haihuwarta kuma shiru inda hakan ke damun kakanki sosai sabida bashida burin da ya wuce ya tara iyalai a ganinsa hakan ne kawai zai sanya masa jin sauqin ciwon da yake dashi a zuciyarsa na rashin danginsa... d'an shiru yayi yana kallon hayfa da tunda ya fara labarin kuka take a hankali yaci gaba babu wani buri da naga kakanki dashi har ya koma ga Allah yana dashi irin gano danginsa da kuma tara zuri'a mai yaw a sosai yanason yara.. Ana haka baban kakarki ya kwanta rashin lafiya Na ajali inda ya rok'i kakanki da koda zai koma Niger neman danginsa kada ya rabu da kakarki kakanki yace ya masa alkawari.. Bayan kwanaki Allah yayi masa rasuwa wata 17 bayan rasuwarsa kakanki ya tara y'an uwan matarsa yace shi zai bazama neman danginsa ko ina cikin fad'in Nigeria suma da sunki amma daga k'arshe suka k'yaleshi da ganin ma bai nemi a bawa kakarki gadonta ba  da haka suka bar malumfashi zuwa funtua shekararsu 2 a funtuwa nan ma babu labari ya shiga Kano nan ma shiru yayi baushi nan ma haka ya shiga kebbi ke ya zaga dayawan garuruw babu labari, Sai a Yobe ne wani ya bashi shawarar shigowa Kaduna cewa a Kaduna buzaye na nan sosai suna aikin gadi mai yiwuwa suna can cike da farin ciki da fatan nasara ya shigo Kaduna inda ya fara aiki wani gida a "Ja Abdulqadir u/Rimi" daga nan yayi aiki katuru rd shekarsa daga nan ya dawo gidan wani tsohon soja a badarawa inda har Allah ya taimakeshi sojan ya bashi gidan kusa damu na badarawa wanda na wasu ne gado sojan ya sayawa kakanki sabida yadda yake jin dad'in aiki dashi a loakcin ne muka fara sabawa dashi dukda ya d'an girme min sosai saidai mutum ne mai barkwanci da girmama kowa da haka har matarsa ta kwanta rashin lafiya goggonku ce ma tayi jinyarta har Allah ya mata rasuwa bayan rasuwarta ma goggo ke kula da mamarki kasancewar da kad'an Suwaiba ta girmeta da haka ne kakanki ya nemi da in aureta ganin shima a lokacin yau fari gobe bak'i.. D'an d'agowa yayi hayfa na kuka sosai.. Yaci gaba tun bayan aurenki na fara neman maki danginki amma zuwa yanzu babu abinda na samu saidai nayi alkawarin zanje sokoto IA bayan anyi hutun makaranta na yara amma banaso y'an uwanki susan komai har sai bayan burinmu ya cika, ya barmin sunayen duk y'an uwansa da iyayensu na rubuta zan kuma baki ki tafi dashi ki adana da kywa, Sannan ki adana da kyaw ni kamar yadda na fad'a miki da anyi hutu zamu shiga sokoto sannan duk halin da ake ciki zan rik'a sanar da ke, ki kwantar da hamkalinki ki rik'e mijinki tsakani da Allah shi arziki daga Allah ne yana bawa wanda yaga dama a lokacin da yaga dama sannan kiyi duk k'ok'arin da za kiyi wajen kiyaye sirrin aikin ki daga gurin mijinki har y'an uwanki zanci gaba da yi miki addu'a Allah ya bud'a masa wata k'ila kafin ku dawo Nigeria Allah ya sa sun canza tunaninsu akan dole sai kina auren mai kud'i kuke da mutunci.... Har yanzu hayfa kuka ta keyi da kyar ya lallasheta ta mik'e ta koma zuwa sashinsu inda shima ya sake fad'awa tunani na rayuwar yarinyar tasa..

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now