KASAR WAJE. 43

825 54 4
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  85/86

Haka rayuwar taci gaba yau ake vote a anayi ne a kowani k'asa da kamfani da ke da yaranta sai a tura da sunayen Milan inda can ne ake taron

Ta internet ake loda pic d'in candidate da information inda ake vote online su hayfa ansha gayu kamar baturiya su duka sunsha kyaw saidai bunill ya kira Armando suka shiga wani office bunill ya kalli Armando yace "anya queen d'inka batada lafiya..? K'irjin Armando ne ya buga inda ya kame ya kalli bunill yace why kace haka..? Bunill yace idanunta duk suna gajiye gashi jikinta a cike kamar mai ciki da alama taje tanata iskanci irin na kowa ce model da zarar sun shigo duniyar d'inkuna

Yawu Armando ya had'iya yace wani yaro ne take soyayya dashi inajin shi ya d'an d'auke mata hankali amma karka damu kafin gala zan maidata daidai

Tsaki bunill yayi yace wlh in ta b'ata mana suna kai ka sanni gaskiya domin sam a result d'inta na gym ma bata kamaci shiga vote ba amma na barka sabida farkonta ne mu bata damar

Ajiyar zuciya Armando yayi yana k'ara ci gaba da lallashin bunill har suka daidaita suka fito inda hayfa na gun Vivian tanata shan drink d'inta

K'arasawa Armando yayi yana kallonta ya kalli Vivian da alamar zargi amma ya share ya kalli hayfa yace "queen" biyoni office ya juya ..tsaki tayi kafin ta mik'e ta fara binsa duk jikinta ya fara ansa abinda take sha

Bayan tafiyarsu cikin Vivian ya k'ulle kada Armando ya ganota domin itama bata tab'a tuna hayfan zata kamu haka da sauri ba Sam yanzu bata jure sai taje gida tasha drink d'inta

Suna shiga office ya maida k'ofar yana kallonta ya kasa magana kusan 5mnts cikin tsawa ya furta "wai ba kyajin magana"? Kina nufin duk k'ok'arin da nake miki bakya gani? Kinaso career d'ina ya lalace a karo na biyu ace na kawo yara da suka kangare haka raudha ta fara a k'arshe abu ya lalace... Kallonsa hayfa ke yi tana yamutsa fuska ita yanzu ma sex take ji sosai da zai k'yaleta da gida ta wuce ta jira Yusuf.. Shi ya dawo da ita tunaninta cikin yanayin lallashi ya fara pls queen ki cire damuwa a ranki ki nutsu kamat yadda na sanki wlh domin future d'inki na keso ki samu gala d'in nan kinji..? Kallonsa tayi a hankali kafin ta girgiza kai.. Kusan 40mnts yana lallashinta da nasiha kafin suka fito a kayi audition na video vote ta rok'eshi wai bacci ta keji za ta wuce gida yace shikenan gobe dai da wuri zata fito tace toh

Sai bayan tafiyar hayfa ya fad'a tunani sosai zuviyarsa ta fad'a masa zargin Vivian akan abinda bai gane ko meye ba inda ya yanke hukuncin saka Camera a kiching d'in..

Tana isowa gida 4:11pm tana cikin cire takalmi Yusuf ya shigo sabida ya bar super market da wuri zasu je duba course d'in da aka basu shi da yasir d'agowa tayi tana kallonsa duk idanunta a birkice a hankali Yusuf ya k'arasa ya d'agota da taammanin gajiyar aiki ne saidai wannan warin yaji.. Runtse idanunsa yayi to ko wani turare ne take anfani dashi ko lotion mai wannan k'anshin

A hankali yake kallonta yana son gane abinda ke yawan sawa yanzu kullum idanunta a tsume.. Labb'ansa yaji ta kama ta fara sha shima ya biye mata domin sam shima hakan bai tab'a damunsa na yawan son sex da take.. Haka suka fara nisa suka ture kujerar falon suka zube gurin suna fitina inda kamar ko yaushe su kayi sex kamar ba gobe ko anjuma..

Bayan komai ya lafa ta wuce baccinta Yusuf ne ya mik'e a hankali yana kallonta saidai ya sunkuya da nufin ya tashi 5:30 ya jiyo warin sosai daga jikinta kuma ya kanji har bakinta runtse idanu yayi ya mik'e ya shiga wanka ya fito ya shirya yana saka takalmi yasir ya k'wank'wasa masa k'ofa da sauri ya nufi k'ofar ya bud'e suka fita kawai kada ya hango hayfa a falon..

Koda suka je inda aka manna course d'in da aka basu yasir an bashi marketing inda Yusuf aka bashi Industrial chemistry sosai Yusuf yayi farin ciki nan suka nufi café inda za suyi printing komai cike da murna suka shiga gari yawo inda k'arshe suka wuce gidan tiffun sabida yasir can zai tsaya su wuce aiki club da tiffun d'in

tiffun yayi murna ganin Yusuf bai tab'a zuwa gidansa ba anata hira k'anin tiffin yazo dubashi inda ya bud'e fridge ya d'auko vodka yana sha.. Tiffun yace zaka kararmin ko..? Bayan na fad'a maka shikenan ya saura banida kud'i ina lallab'ashi .. Kallonsa yasir yayi yace aikinka kenan lissafi ka bar masa mana ina wannan tun 2mths ka saya..? Tiffun ya harari yasir yace pls ka saya masa nasa ya batmin sauran nawa da shi na ke gud nyt in baby's sun kawo ziyarar dare kasan harka yafi dad'i in na san musu a drink.. Dariya yasir yayi ya kai masa naushi ya kauce tunda suka fara hirar hankalin Yusuf na kan jack da ke wani wari-wari wanda ke Kama da warin da ya ke ji a jikin hay.. Da sauri ya furta innalillahi a zuciyarsa yana kallon tiffin yace Man zan wuce inada aiki zan tsaya gida kuma b4.. Tiffun yace tnx man yau ka kyawtamin over gadiya na ke ka gaida "African beauty" murmushi Yusuf yayi yace "tnx" ya musu sallama suka rakoshi da yasir ya wuce

Tun da ya shiga taxi yake kiran sunan Allah anya wannan abin ne ya kejin warinsa a gida da jikin hayfa..? Runtse idanunsa yayi yana fatan mistake ne ba  shi bane haba ta yaya ma.? Da haka har ya iso gida kusan 9:12pm tana kan dadduma tanata ramakon sallah tayi turaren wuta tunda ya shigo ya ke ta jan numfashi ko zaiji wannan warin bai jiba ya k'arasa d'akin tana kan daddumar bayi ya shiga yayi alwala ya fito ta mik'e ta zauna gefen gadon ya tayar da sallah zuciyarsa cike da wasiwasi kala-kala.

Bayan ya idar yana kan daddumar yake kallonta sosai itama ta d'an kalleshi kafin ta sunkwi da kai tana jin wani iri kamar yana tuhumarta.. d'an d'agowa tayi taga still idanunsa na kanta

A hankali ya mik'e ya ninke daddumar ya k'arasa ya zauna gefenta ya rik'o hannunta yayi kissing ya d'ago hab'arta yana kallon cikin idanunta ya furta "pls baby ki rik'a kulamin da kanki kinji"..? Gitgiza kai tayi a hankali.. Yaci gaba yau mun ga course d'inmu ina jin d nx 7wks zamu fara lecture IA.. Kallonsa tayi ta d'anyi murmushi ba ta iya magana ba..

Yayi ajiyar zuciya yace bansan mai zai faru ba amma zan k'ara busy maybe ma sai na ajiye aikin supermarket amma ina fata Allah ya tabbatar min da abinda yafi alkairi sabida sai dole na nemi aiki ko na wk end ne na had'a da masallaci amma I promise u ke ma next year zaki fara karatu kinji IA.. Rungumeshi tayi tana d'an sharar hawaye shima ya k'ara matseta jikinsa.. Kusan 3mnts yace "baby bari naje aiki zanyi lati.. Mik'ewa tayi ya saka takalmi hannunsu na sark'afe ta rakashi har ya samu taxi ya wuce ta dawo gida..

Ammah ta kalli Abba tace "Abba wai shi abokin na ka bai baka a dress ba "? Abba yace eh in mun shiga kebbin zan kirashi kawai haka mu kayi.. Ajiyar zuciya tayi tace shikenan Abba Allah ya tsare ya kiyaye hanya da ka isa pls ka kira.. Toh yace ta ciro 50k tace Abba ka rik'e a hannunka sabida tsaraba a hanya "toh" yace yace Allah yayi albarka tace amin suka fito duka harda yara suka rakashi har mota dreba ya tayar suka fito su ammah da goggo da yara sunata d'aga musu hannu..

Sai da suka yi nisa ya kalli garbati dreba yace kayi parking na kira Hadiza.. Hayfa na zaune shiru tun bayan tafiyar Yusuf taji wayarta na ringing ta d'aga tana kallon screen ganin abbanta ne ta bari ya tsinke kafin ita ta kirashi ya d'aga ta fara gaisheshi..

Yace muna hanyar sokoto IA ki yi mana addu'ar nasara nadawo miki da labari mai dad'i.. Allah yasa tace Abba sun dad'e suna hira kafin suka yi sallama su Abba suka nufi sokoto..

Wajajen Magrib suka shiga sokoto inda Abba ya kama musu hotel shi da garbati ya kira su ammah yace yana masaukin sosai suka yi waya da su da goggo alje kafin su kayi sallama ya jefa layin hayfa siadai bata ansa ba  saida ya tsinke kamar ko yaushe tukuna ta kirashi

Ya bata labarin suna sokoto sun isa lafiya sunyi fira sosai kafin su kayi sallama..

Yusuf yana aiki a masallaci yanata tunanin warin da yaji jikin jack da wanda yake ji a gida jikin hayfa tabbas irinshi ne to ko su Clara ke sha dake suna aiki tare dole abin na shafarta ajiyar zuciya yayi yana fatan Allah yasa kada itama wataran ta kusanci hakan ganin tana tare da masu yi hakan yasa bayason ma aikin don kawai baida yadda zaiyi ne amma IA da bud'insa ya k'aru ya gama biyan alhaji nx mth inajin zata bar aikin cafe d'in ina bata kud'in kashewa ko yaya ne da wannan tunanin hankalinsa ya d'an kwanta

KASAR WAJEحيث تعيش القصص. اكتشف الآن