KASAR WAJE. 51

1.3K 61 1
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 101/102

Tunda gari ya waye Inna suka fara shiri inda inna ta saya gurasa babbar leda duga mai cin gurasa 200 sannan ta saya hadd'ad'en kuli mudu goma da kayan miya ko wanne kwando su layla da Rafiya duk suma sun fito cikin abaya sunyi kyaw kamar twins Aliy ya iso suka gaisa da goggo da itama take zaune tabarma su layla na kusa da ita yana shirin magana Wayarsa ta fara ringing ya duba yaga Yusuf ya d'auka yana furta ranka ya dad'e Yusuf ya saki d'an dariya yace ka cika shirme ya kake.? Aliy yace lafiya Yusuf yace zan saka maka kudi yanzu su inna suyi hidimar tafiya pls ka raka su ku je ku dawo tare OK aliy yace suka d'an tab'a fira suka yi sallama bai Inna ta fito suka gaisa da Aliy yake fad'a mata mota na waje su fito nan ganin yawan kayan da inna tayi aliy ya fita ya kira mai mota dama sienna ya hayo musu suka fara fita da kayan shi da dreban saida suka gama tas kafin su inna suka fita goggo na ta masifa wai ya kamata a ce tun asuba ma suna gidan rasuwar babu wanda ya tankata suka gama shiga aliy da dreba a gaba goggo da Inna da su Rafiya duk suna baya suka kama hanyar Kaduna

Suna hanya Aliy yaji alert ya duba saqon Yusuf ne ya tura 145k a naira murmushi yayi yana ayyana yadda Yusuf ya tara kud'i ba laifi daga rasuwar alhaji da Hayfa ta biya masa bashi zuwa yanzu kud'insa sun ma kai ya sayi qaramin gida ya saka haya..

Tunda ta tashi da safe ma jikin ya sake rikice mata amai ta ke ji bayan bata ci komai ba ga jiri-jiri Ammah ce tace ta dawo d'akinta kusa da ita sabida ta riqa kula da ita Abba kuwa shima almajirai masu zuwa karb'ar sadaka sun zagayesu yanata raba musu abinci harda wanda ya kwana yasa laraba ta kwaso a fridge

a badarawa maqotan Suwaiba suma dake sunsan yadda su suwaiba suka kud'ance tunda qawarsu ta auri billonia suka yanke hukunci yin qungiya suje mata ta'aziya wasu na burin daga haka su qara shigewa suwaibar suna zuwa gidanta maula.
daga cikin maqotan suwaibar akwai Talle wacce ke auren yayan Yasir suna shiri sosai ita da Yasir inda harda Talle za'aje ta'aziyar dukda ita batama san Suwaiba kawai tsabar shishshigine jin masu kud'i ne su suwaiban

a gidan rasuwar kamar gidan biki mutane sai b'ulb'ulowa suke qara yi inda Hayfa ta kalli Ammah tace "momminmu bakya buqatar wasu kud'in".? Ammah tace karki damu hayfa tace mommy naga mutane sunata qaruwa.. Ammah tace eh inaso zanwa suwaiba magana anjuma su koma kasuwa da garbati da su yalwati da goggo Mauje da goggo marka sai suqara cefanen hayfa tace akwai kash a hannuna sai ta ansa suyi canji suyi anfani da shi shafa kanta ammah tayi tace babyna akwai kud'i sosai ma a gida kada ki damu shiru hayfa tayi

11:38am su inna suka shigo Kaduna direct kasu suka nufa inda tuni su Qassem na jiransu suka shiga goggo yalwa na ta tsokanarsu wai duk kallesu kamar yahudawa sunsa qananan kaya bayan gidan ta'aziya zasu sudai duk yaran basuda yawan magana suka share ta tanata yi Inna ta kalli goggo tace zamu biya ta gidan aminin babansu mu sanar dashi shima goggo tace hakan yayi saidai ko fita daga mota ba zamu yi ba sabida yakamata tuni muna gun rasuwarnan ai sai surukanmu su rainamu shi Isuhu Allah ya shiryeshi sarkin nauyin baki da zurfin ciki

A gate d'in gidan alhaji sammani Inna da k'yar ta lallab'a ina ta barta ta shiga sanar da su sosai matar alhaji sammani tayi mamakin ganin irin sanjawar da inna tayi haskenta ya fito kyawunta ya qaru ta qara quriciya kamar matashiyar mace bayan sun gaisa inna take sanar da ita rasuwar inda Inna tace yanzu ma can zamu wuce miqewa itama tayi tace ai dole mutafi tare ga Mardiya ma duk muje inda ta haura sama ta d'auko hijabi dama da kyawunta less ne jikinta itama mardiya abaya ne jikinta suka fito ta fito da motarta ta tsaya ta window mota suka gaisa da goggo mardiya su layla ma suka fito duk suka koma motar hajiya suka d'unguma gidan rasuwar

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now