KASAR WAJE. 20

1.1K 46 1
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 39/40

Hawaye kawai ke bin idanun hayfa sai jinta tayi a jik'e inda nurse ta fara bata agaji su raudha suka wuce suna dariya

sai kusan 1:23pm hayfa ta d'an samu kanta tuni an nurse ta mata wanka da ruwan d'umi sosai ta gyarata tasa maida mata kayanta domin babu maganar exercise aka bata magunguna Armando yace ta huta 3dys a gida zai kira café ma ya fad'a sannan zaiyi arrangements a d'aga aikinsu zuwa nx wk da haka driver ya dawo da hayfa gida....

Bayan ta kulle gidan ta wuce d'aki ta kwanta ta tura ledar magani karkashin gado. Ta kwanta saidai hawaye ta fara sosai tana tunanin wai yaushe ta shigar da kanta wannan duniyar aikin? Mai yasa ta fara?
Saidai tsit tayi tuna aikin ke rufawa y'an uwanta da iyayenta asiri a yanzu saidai sosai hankalinta ke tashi in ta tuna Yusuf da aurensa a kanta take wannan aikin

Sosai tayi kuka kafin bacci ya kwasheta sabida allurai da magunguna da tasha tun a asibitin.

Yusuf da sam ko daya jarraba yin d'an bacci ya kasa zuciyarsa ke masa wani iri ga kansa yanzu yayi sauk'i saidai haka kawai yana jin babu dad'i a zuciyarsa

Yana kwancen yasir ya dawo ya bashi drug da sandwich ya d'anci yasha panadol inda yasir yace ka koma gida kawai ka kwanta a can ni zanma aikin yamman in ma ba zaka iya zuwa club ba kayi zamanka zanma aikin ko nasa tiffon ya karb'a maka dama ina binsa bashin lst wk tym da budurwarsa tazo ya kwana gida

Yusuf ya mik'e da k'yar ya kalli yasir yace "kai d'an uwa ne na gaskiya Nagode"...!

Yasir yace babu komai ya rako Yusuf har ya shiga taxi suka yi sallama...

Tun bayan tafiyar hayfa raudha da liliana ke dariya liliana tace "gaskiya da alama kadhija bata dad'e da sanin namiji ba shegiya k'ila shiasa duk take jin tafi kowa" suka fashe da dariya

Raudha tace ke k'ila kuma saurayin ma ya mata alk'awarin aure ne shiasa take sonsa take k'in kula wasu, kuma kinsan mu musulmai iyayenmu da kinyi 12yrs kullum maganarsu da ke aure

Liliana tace da kenan ko?

Raudha tace ke har yanzu wasu haka suke ko mu a India matsalar da ake fama da ita kenan wasu iyayen su hana yaransu cika burinsu ko zama wani abu a rayuwa su turasu aure

Liliana tace haka...

Raudha tace amma kinsan wani abu da nima na gane da khadija?

Liliana tace ah ah

Raudha tace da alama ta fito inda akwai tarbiya domin ina zargin wannan aikin da wuya in iyayenta sun sani kuma indai nayi bincike na gano basu sani ba ni zan fallasa ta

Liliana tace nima tuni na fara zargin haka in ba haka ba ko kud'inta ba taci sannan kullum muka yi aiki bata zama dinner take guduwa in anyi magana tace ta gaji ne ko aikinta daban ne da wanda muke oho

Raudha tayi mutmushi ki barni da ita zan gano wacece ita sannan in fitar da ita daga duniyarmu

Liliana ta daki kafad'ar raudha tace na yadda da ke, yauwa yau ba zamu club ba?

Raudha tace zamu amma da shiga mai kyaw sabida zanje gina gimnati na ne

Liliana tace shiga mai kyaw kamar yaya?

Raudha tace ni zan saka abaya ta Dubai da d'an kwali ke kuma gown har gwiwa koda baki musulma ya kamata su fara tsammanin munada tarbiya kawai rannan akasi aka samu muka je club a yanayin tsiraici

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now