Part 36

34 3 0
                                    

🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
'''NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.'''

_wannan shafin naki ne ZEENAT, ina godiya da yanda kike ƙaunar Littafina, Allah yabar ƙauna_❤️

.

    *CHAPTER 36*

Dad na zaune a parlour'n sa Khalil yashigo yazauna kan kujeran da ke Facing Dad ɗin, Dad ce masa yayi

"Ina fata kaji abinda ke faruwa ko?"

Gyaɗa kansa Khalil yayi

Dad yace "yanzu kana da wata ko kuwa?"

"Dad ni Banda wata, ni abar ma maganar sai zuwa nan gaba don ban shirya aure yanzu ba dama".

Kallon sa Dad ɗin yake yi  be ce komi ba, sai kuma can yabuɗi baki yace "Ibrahim ba maganar wasa muke yi da kai ba, aure nake so kayi kuma a wannan lokacin na gaji da ganin ka haka, idan har maganar neman mata kake yi to Ni na samo maka, akwai yarinyan Abokina da zaka je kanema domin yanzu mun riga da mun gama maganar da Alh. Mustapha".

Ɓata fuska Khalil yayi yace "Dad meyasaka kake son kabani wacce bana so?"

Murmushi Dad ɗin yayi yace "har yanzu kai yaro ne Ibrahim, ba wai zan maka dole bane amma tunda naga matar ce kakasa nemowa shine Ni nayi maka gwanin ta nanemo maka, kaje wajen ta idan har kun dai-daita kanku shikenan".

Khalil yace "Dad don Allah meyasaka baza'a janye maganar ba? infact ma Ni yanzu bani da lokacin aure sabida zan tafi England yin wani course, kuma One year zanyi acan".

Dad yace "ok kana nufin Adena maganar auren ka har sai kaje kadawo?"

Gyaɗa kansa yayi yana kallon Dad ɗin tare da turo baki, daƙuwa Dad ɗin yayi masa yace

"Kaga naka Ibrahim babu inda zakaje sai kayi aure koda kuwa gobe ne zaka tafi".

Cikin shagwaɓa Khalil ɗin yace " Haba Dad please Mana kabari sai nadawo inyaso sai in auri ita yarinyan da kakeso".

Shiru Dad ɗin yayi yana kallon sa kana yace "ok shikenan, dama itama yarinyan tana karatu kuma dama Mahaifin ta yace min zuwa nan da shekara ɗaya da rabi zata kammala, kaga idan kadawo sai asaka ranan auren hakan yayi?"

Jinjina kansa yayi yace "eh Dad".

"Ok tashi kaje Allah yataimaka, yaushe ne zaka tafi?"

Khalil da yamiƙe tsaye yabashi amsa da cewa "nan da Three weeks".

Dad yace "kana da lokaci ai Yakamata kaje wajen yarinyan kaganta, kuma bana son inji cewa bakaje ba".

Gyaɗa masa kai yayi kafin yayi masa sallama yafice. Koda yafito babu kowa a palrour, kawai ficewa yayi batare da yashiga wajen Mom ba, motan sa yashiga yabar gidan, wayan sa yaɗauka yakira Brr. Tahir ringing biyu yaɗauka yace

BARRISTER IBRAHIM KHALILWhere stories live. Discover now