chapter Twenty Four

68 3 2
                                    

🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

'''Wannan shafin naku ne masoyana Fhadeela, Fateeymuhammad, Auta Safna, Nana Faruk, Nafisa Ibrahim, Mum Afnan $ Yumna.. kuji daɗin ku da wannan page ɗin domin naku ne kyauta, na gode da ƙaunar ku gare ni.'''

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Twenty Four*

________🎓 Jiki na rawa Khalil yamiƙe yanufi Fridge ya ɗauko ruwa yazo ya yayyafa mata a fuska, bata motsa ba sai da yasake zuba mata sosai kafin takawo numfashi alamun ta dawo hayyacin ta, bata buɗe idanun ta ba sai dai hawaye dake fitowa ta cikin idanun suna gangarowa gefen kunnen ta

Kiran sunan ta yasoma yi but taƙi ta amsa masa duk da kuwa tana jin sa, hankalin sa ne yasake tashi yana shirin ɗaukar ta sai wayan ta tasoma ringing, ɗauka yayi ganin Ummi ne me kiran sai yayi peacking

Daga can Ummi ce tasoma magana da faɗin "Hello My dear".

"Aslm alaikum Ummi ba ita ce ba".

"Ok Khalil Kai ne ashe, to lafiya dai ko?" Ummi tafaɗa gaban ta na faɗuwa

"Ummi babu lafiya, Halwa ce tabar gida ita kuma Saleema gata nan akwance har suma tayi sabida tafiyan nata". Yayi maganar ahankali cikin dauriyan murya da dannewar tashin hankalin sa

Cike da tsananin tashin hankali Ummi tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ta tafi kuma me yafaru ne?"

Bata jira kuma amsar sa ba sai tace "gani nan zuwa gidan yanzu insha Allahu".

Wayan takatse tana ɗaukan gyalen ta tayafa tare da jakar ta tafito Parlour

Daidai lokacin da shima Abba ya fito daga nashi ɗakin yana saɓa malin-malin, hannun sa riƙe da takardu, su yamanta shine yadawo ɗauka

Kallon sa tayi yayinda shima yake kallon nata

"Lafiya na ganki ahaka meke faruwa?"

Ummi kamar zata yi kuka saboda tashin hankalin da take ciki tace "Abban Saleema wlh babu lafiya, wai Halwa ce tabar gidan ga kuma Saleema can hankalin ta atashe har suma sai da tayi".

"Subhanallah.. mu je muje gidan". Abba yafaɗa yana yin gaba dasauri Ummi na take masa baya

          *****

Shashsheƙan kukan Saleema ne kaɗai ke tashi cikin parlour'n, tana jingine jikin Ummi, Abba kuma na zaune gefen Saleeman sun saka ta tsakiya, yayinda Khalil ke zaune  a kujeran dake Facing nasu

BARRISTER IBRAHIM KHALILTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon