Part 15

50 3 0
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
'''{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈

         *⚜{{F.W.A📚}}*

'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
'''NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.'''

.

     *CHAPTER 15*

"Ke da wanene haka kike ta ja mishi Allah ya isa?" Cewar Mama tana bankaɗo labulen

Dasauri taɗaura hannu a saman fuskarta, cikin ruɗewa tace

"Ahm Ma.. Babu kowa".

"Ya zakice min babu kowa bayan naji da kunnina kina mishi Allah ya'isa, tukunna ma me yayi miki da za'ayi ma yaran shi?"

"Mama wani ne fa yakusa yabige ni, shine sai ƙunduma min zagi yake yi, shine fa abun yanzu yake damuna".

Guntun tsaki Mama taja tana sakin labulen tace

"Shine ke kuma tunda baki da haƙuri zakizo kina taja mishi Allah ya isa? Allah yashirya ki Halwa, nima da naji ku shiru ne nafice abuna".

Ɗaki Maman tashige tana ci gaba da surutun ta, yayinda Halwa kuma gyara kwanciyan ta tayi tana sauke ajiyan zuciya cike da fargaba, rufe idanuwanta tayi tana jin wani kukan na sake zuwan mata tuna abun da yafaru da ita yau, wani irin ƙunci da baƙin ciki ne suka tokare mata wuya, take tafashe da kuka tana toshe bakin ta

"Shikenan yau an raba ta da abu mafi daraja ajikinta, wai yau ita ce wannan ƙaddara yasame ta, abinda ko a mafarki bata taɓa tunanin wannan ɓakin ranan zai zo mata ba, ya zatayi da rayuwan ta? Ji take yi kamar takashe kanta duk sanda tatuna yau wani namiji yasanta a ɗiya mace batare da aure ba

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Abinda take ta maimaita wa kenan har tasoma jin zuciyarta na mata sanyi.

.

**** **** **** ****

     *WASHE GARI*
          *EGYPT*

Zaune yake saman Three sitter ya harɗe ƙafafunsa yana danna Lapton ɗin sa, takardu ne birjik agaban sa sai faman aiki yake yi, yana sanye cikin fararen kaya masu taushi sosai, wandon Three qweater ne sai Rigan me kamar singlate

Tun jiya da yasauka a ƙasan yake faman aiki babu ƙauƙautawa, bincike sosai yake akan mutumin da yazo don shi amma har yanzu yagaza samun koda bayani ɗaya akan sa, sosai yake cikin damuwa ko lokacin kansa baya dashi, yanzun ma aikin yake yi but tunanin sa na wani wajen daban, wayan sa da tasoma ringing yayi saurin ɗauka domin dama abinda yake jira kenan

"Hellow Poker.."

"Ok.. ok turo min da address ɗin wajen".

Cire wayan yayi a kunne yariƙe a hannu yana kallon screan ɗin wayan, 1mint sai yaji Message ya shigo, dasauri yabuɗe yaduba sannan yatashi, cikin sauri yasauya kayan sa cikin farar riga me gajeren hannu da blue jeans, sai yaɗaura jaket saman rigan baƙi ne me belt a wajen cikin sa, jaket ɗin me hula ne sai dai be sanya hulan ba iyakan yasaka Combat a ƙafan sa Black, yaɗau wayoyin sa yazuba a aljihu yafito yarufe ɗakin, kasancewar a Hotel ne ɗakin sa yana hawa na uku ne, cikin sauri_sauri yake taka step ɗin har yasauko ƙasa, yana fita yatari taksi yashige suka tafi, a wani haɗaɗɗen club aka sauke sa yafito yabiya me taksi ɗin kuɗin sa kana yamatsa gefe kaɗan yana ƙare ma wajen kallo, tsawon mintuna 5 yaɗauka awajen kafin yajanyo hulan Jaket ɗin ya'aza akan shi yasoma takawa yashige wurin, sosai ciki yake da duhu, mutane ne birjik ciki kowa na sha'anin gaban sa, ba abinda ke tashi aciki sai daddaɗan cool music da aka sanya wasu sai cashewa suke yi, yana shigowa kallon wajen kawai yake yi har ya'isa wani hill chair yazauna yana kallon mutane, tsawon mintoci yana zaune a wajen yana nazarin inda zai ga mutumin da yazo nema, sai kawai yayanke shawaran nufan wasu matasa maza da mata dake zaune gefe can saman wasu haɗaɗɗun kujeru sai kurɓa alcohol suke yi, wata matashiyar budurwa ce taƙariso kusa dashi hannun ta riƙe da cup, kallo ɗaya zaka yi mata kagane irin waɗannan gogaggun karuwan nan ne, skin ɗin ta baƙi ne but ko kaɗan batayi yanayi da ƴan Nigeria ba coz yanayin shiganta da wayewan ta

"Hi". Tace dashi lokacin da ta'isa gaban shi

Kallon ta yayi sai yaɗauke kan sa dasauri batare da ya amsa mata ba, murmushi tayi tace

"Kana son wani abu ne? Naga tun ɗazu kazo kazauna anan kamar kana neman wani ko?"

Gyaɗa mata kai kawai yayi batare da yasake kallon ta ba

"Ok ko zan iya taimaka maka?" Tafaɗi maganar tana kurɓan Juice ɗin dake hannun ta

Shiru yayi kamar bazai ce komi ba sai kuma yace

"Ina son ganin Mr. Jay pitter ne, me wajen nan, ance min in nazo nan zan same shi".

Murmushi tayi tana gyara gashinta takalle shi dakyau, sai kuma tagirgiza kan ta tana jawo kujera tazauna taci gaba da shan Juice ɗin ta, shiru ne yagibta a tsakanin su har Khalil yana shirin tashi sai yaji muryan ta ya doki kunnin sa

"Meyasaka kake neman sa?"

Ɗan kallon ta yayi sai yakau da kai be ce komi ba, ƙure shi da ido tayi tana wani irin murmushi tace

"Daga Nigeria kake ko? Nima acan nake ai".

Taƙarike maganar tana kau da kan ta taci gaba da sipping juice ɗin ta kamar ba itace tayi maganar ba, shi kam kallon ta yake kamar me neman wani abu jikinta, mamaki ne kwance acikin ran sa domin ko kaɗan batayi kama da zubin ƴan Nigeria ba, musamman ma da yaga tana mishi turancin kamar tana wani yare, sam ba wani fahimta yake ba, murmushi tasake yi wannan karon da Hausa tayi maganar tace

"Kana mamaki ko? Uhmmm kadena mamaki sabida ni da kake ganina cikakkiyar Bahaushiya ce ƴar Nigeria, Nigrian ma a Kano, sunana Fadila kuma musulma ce ni, but anan ana kira na da baby Dil".

Ɗago kai yayi sosai yana kallon ta da tsantsan mamaki a face ɗin sa wannan karon, but yaƙi furta komi

"Kafaɗa min meyasaka kakeson ganin Mr. Jay pitter?"

"Meyasa kikeson nafaɗamiki?" Yayi maganar yana kau da kai kanta

"Sabida zan taimaka maka, bazaka taɓa samun shi anan ba, koda zaka kwana kana sintiri ne, wahala kawai zakayi, but Ni kuma zan iya taimaka maka in kaika inda yake".

Khalil yace "Please kitaimaka min ina son ganin shine sabida wani bincike da nakeson yi".

Dariya tasaki tana kallon shi cike da sha'awa tace

"Sau da yawa ina ganin irinka suna zuwa nan don neman sa, kuma tun sanda naganka nagane kai ɗan Nigeria ne kuma nasan abinda yakawo ka har kake neman sa".

Da mamaki Khalil yakalle ta yace

"Taya kika sani".

Sai da tashanye sauran Juice ɗin ta'ajiye cup ɗin sannan takalle shi tace

"Idan har kana son taimakona to mubar nan wajen, Ni kuma zan faɗamaka duk abinda kakeso kasani, har da wanda ma bakaso".

Shiru yayi yana nazari kafin yace

"Ok muje to".

Tashi tayi takalle sa tana kashe mishi idanu, tamatso kusa dashi kaɗan ahankali tace

"Kabari in nafita sai kabiyo bayana".

Hakan ko akayi, sai da tafice kafin yabiyo bayan ta, daga can nesa yahango ta tsaye tana ware hannayen ta tana yarfe su, wajen ta yanufa yana kallon ta, bata bari yayi magana ba tace

"Kasamar mana taksi mubar nan".

Sai kuma tasakar masa murmushi tace

"Ko muje musaukin ka".

Wani irin kallo yayi mata, sai tawaro idanu still tana murmusawa tace

"nan zai fi sirri, coz za'a iya samun matsala ne".

Jimm yayi kana yace

"Ok"

Daga nan yatare musu taksi suka shiga suka tafi.

BARRISTER IBRAHIM KHALILTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang