Part 6

89 6 0
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
'''{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

         *⚜{{F.W.A📚}}*

'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
'''NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.'''

.

     *CHAPTER 6*

Shiga tayi cikin gidan nasu da sallama a bakin ta, Mama da fitowar ta kenan daga ɗaki riƙe da kwano ahannu ta'amsa mata tana kallon ta, ƙarisowa Halwa tayi tana kallon Maman nata da tasami waje saman tabarma tazauna tace

"Mamana sannu da gida".

"Yauwa ƴata takaina, kin dawo?".

"Washh.. nagaji wlh Mama".

Halwa tafaɗa tana zama gefen Maman

"Ai daga ganin yanayin ki nasan da haka, da fatan dai ba wahalan mota ce tatsai dake ba?"

"Shine wlh Mama, kuma sai nabiya gidan su Zainab na je duba jikinta".

Mama kallonta tayi tace

"To ya ya jikin nata? Ta samu sauƙi dai ko?"

"Alhamdulillah Mama jikin nata ya warware ai sosai, Umma ma na gaishe ki".

"Tom Ina amsawa, naso ma in shiga in gaishe ta Allah be yiba, sai ki tashi kije kiɗau abincin ki yana ɗakin ki, don nasan tunda kika langaɓe anan sai kizauna kiyi ta zuba bazaki ci ba, kuma nasan da yunwa atattare dake".

Dariya Halwa tayi tace

"Wlh Mamana shiyasa nake ƙara son ki sabida ƙaunar da kike nuna min, uhm ai yau bazan iya wasa da abinci ba sabida yanda naji hanjin cikina suna kaɗawa, bari dai inje in ɗauko".

Tamiƙe tsaye tana kwaɓe hijabinta, Mama kuma taɓe baki tayi tace

"Da dai bansan halinki bane, yanzu sai ki jagula kibar shi nan".

Halwa shigewa ɗaki tayi tana ɗaga murya tace

"Mama banda yanzu dai, kibari kigani har ƙari ma sai kinyi min".

"To bansan surutu kimaza kiɗauko kizo nan kizauna kici".

Fitowa tayi riƙe da coolar ahannun ta da wayanta, zama tayi tana tanƙwashe ƙafafunta tasoma danna wayan tana faɗin

"Mama har yanzu Yaya be dawo ba?"

"Ni ban ganshi ba, sai ki neme sa ta waya kiji inda yatsaya". Cewar Mama tana ci gaba da ɓare maggi

Wayan takara akunni tasoma buɗe coolar'n, hannu tasaka tasoma kai loman abincin dai-dai lokacin da aka ɗaga wayan nata tace

"Wai yaya ina kaje ne har yanzu shiru baka dawo ba?"

BARRISTER IBRAHIM KHALILWhere stories live. Discover now