24

1.7K 89 22
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 24*

Kallanta yayi tun daga sama har kasa, wando ne a jikinta sai hijab data saka akai, sai kuma kudin da yaga ta rike a hannunta, wani irin bugawa kirjinshi yayi da karfi, tunda yake a rayuwa yau ya taba jin irin wannan mummunan yanayin idonshi har wani dishi dishi yakeji Yana Masa, kokari yake yayi salati Amma ya kasa saboda bawai iyawa yayi ba, dakyar ya iya furta kalman Oh my God...... Kokari yayi ya matsa kusa da ita wacce itama take a tsorace da ganin irin yanayin da yake ciki kuma tasan tabbas Bata da bakin mishi bayani domin ba lallai bane ya yarda da bayanin da zata mishi ba

Gab da ita yazo dai dai saitin kunnenta ya matsa sannan ya kira sunanta tare da fadin Afrah...... Shuru yayi kaman Yana tunanin abunda zai fada, wani irin ajiyan zuciya ya sauke sannan yace mai yasa kika fita ba tare da sanina ba???

Sannan wajan wa kika je?? Plz Afrah kar kiyi abunda zaisa in fara zarginki dan Allah bana son zargi ya shiga tsakaninmu ni dake plz......

Matsawa yayi daga kusa da ita, tare da fadin In kin shirya sai muje, Yana fadin haka yayi gaba har yayi taku uku zuwa hudu, ya juyo ya kalleta yace ina jiranki a Mota tare da fita

Jikinta a sanyaye tayi dakinsu tafiya take kaman wacce kwai ya fashewa a ciki, harta karasa cikin dakinsu dake Hotel din

Aysha ta kalleta tare da fadin Afrah Kinga David kuwa??

Afrah kaita daga mata alaman eh ta ganshi tare da kallon Aysha tace Aysha David ya ganni na fito a dakin wannan mutumin kuma wlh ranshi ya baci duk da yaso ya boye fushinshi Amma naga tsabar fushi da kishi a idonshi, wlh ina son David ina mai son so, bana tunanin zan iya cin amanarshi tunda na tabbata ina sonshi na daina hulda da kowa, kema da kanki zaki iya shaidana, inda nasan zai ganni bazanje Kiran wannan mutumin ba wlh, domin ko kadan bana son fushin David

Aysha tace karki damu nasan David Yana sonki bazai kuma zargeki akan aikata alfasha ba, na tabbata sonda yake miki bazai yi zarginki ba, yanzu Yana ina

Afrah tace Yana mota Yana jirana

Aysha tace yauwa kin gani, inda Yana zarginki na tabbata bazai ce zai jiraki ba, sai dai ina son ki sani ki kara taka tsan tsan domin duk wata mace da tayi irin wannan rayuwar toh babu shakka saita fuskanci Challenge ma'ana kalubale, wlh Afrah David Yana matukar sonki, ki duba ki gani yau kwananki nawa a hotel duk saboda tsaron lafiyanki, kuma duk kuna daya kudi yake biya masu yawa, ga abincin da muke ci duk shi yake biya dan haka inaso ki cire kowa da komai ki tsaya waje daya wannan itace shawarar da zan baki a matsayina na kawarki yar uwarki mace kuma

Afrah ta numfasa tare da fadin na gode sosai da shawarar da kika bani, sannan insha Allah zanyi taka tsan tsan tabbas nasan ina son David kuma bazan so ace wani abu da zai kawo Mana zargi ya shiga tsakaninmu ba, nasan Aysha keda kanki kin san ina taka tsan tsan yaushe rabonki da kiji ina waya da wani namiji???

Aysha tace hakane nasan ai duk kin daina, ina so ki kara kiyayewa sosai ne rayuwa saida taku

Afrah tace hakane, Allah dai yasa mu dace tare da fadawa toilet batafi minti biyar ba ta fito ta canza kaya tasa wata jallabiya baka tare da yane kanta da gyalen jallabiyan ta fashe ko ina na jikinta da turare masu dadin kamshi, sannan ta janyo wani karamin akwatinta tare da kallon Aysha tace zamu kama hanya, sai kiyi Mana addu'an samun nasara

GIDAN KASHE AHUحيث تعيش القصص. اكتشف الآن