48

249 10 0
                                    

David kasa yayi, yayin da mum dinshi ta saki Kara mai ban tsoro tana ihu tana fadin he kill my sonI will never ever forgive you for that, how dare you inda ta nufi mahaifin David din tare da kama mishi wuyan Riga tana ihu...........

David Kam Yana kwance cikin jini, yayin da mum dinshi lokaci daya ta nufi David din, tana kiran sunanshi da David wakeup ai ganin jini yasa ta Kuma rudewa tare da Kara jijjiga Dan nata tana fadin ya tashi karya mutu ya barta, lokaci daya ta fara kici kicin daukarsa Amma mahaifinsa yazo ya riketa tare da fadin Ina zaki kaishi he have to die, ganin Yana riketa yasa ta waiga tana tureshi tare da fadin duk fadan da kakeyi zaka kasheshi inya musulunta ban taba dauka dagaske kake ba, yau itace rana ta farko da nayi dana sanin mara maka baya a duk abunda kake aikatawa, sannan yau itace rana ta farko da kasa zan fara bincike akan addinin musulunci..... Tas ya wanketa da mari tare da fadin you are mad baki da hankali...... Cikin ihu tace da hankali na inada hankali kaine baka da hankali ka barshi yayi addinin da yake so mai yasa zaka kashe mun gudan jini na, he is only my son shi kadai gareni, miye abun tsoro danya canza addini indai har addinin mu gaskiya shida kanshi zai dawo.......

Dakinta tayi da gudu inda taje ta rufe dan karya shigo number din police ta kira ta fada musu abunda mijinta ya aikata, aiko minta shabiyar ba'ayi ba Police suka zo, kai tsaye gidan suka shigo ita ta musu iso bayan tace kar su saka jiniya, aiko suna shigowa suka ga David a kwance cikin jini, tuni suka saka ma mahaifinsa ankwa, sukai gaba dashi yana fadin Kun San wanene ni kuwa?? Kunyi kuskure na kamani...... Shi Kam David daukansa sukayi amma abun mamaki Bai mutu ba nan akace a kira ambulance cikin minti goma motar asibiti tazo aka sakashi akai asibiti dashi domin ceton rayuwarsa, harsashin ya sameshi a kirji.......

Anyi nasara an cire bullet din, sai dai ya zubar da jini sosai, inda aka kara mai jini, David yana samun kulawa sosai wajan likitoci sai dai har yanzu bai farka ba, mahaifiyarsa Kam tana cikin damuwa tunani ne kala kala ya taru ya cunkushe mata a kai, na farko na ko danta zai tashi, ga mijinta daya aikata laifin na hannun hukuma, sannan shi wannan addinin na musulunci miye shi? Tana bukatar sani ya addinin yake da ake kyamarsa, kawar da tunanin tayi domin ita burinta danta ya tashi shine abunda tafi bukata yanzu sauran duk masu sauki ne a wajanta

David saida yayu kwana uku kafin ya farfado bakinsa dauke da salati, inda mahaifiyarsa ta nufeshi da sauri tana kiran sunansa tare da godema Jesus daya tasar mata da Yaron nata, tabbas tana cikin farin ciki sosai na ganin yaronta ya tashi inda ta tafi ta kira dr aka zo aka dubashi aka ga komai normal, magananshi daya fara Yima mum dinshi ina Dad dinshi??.

Tamke fuska tayi tare da fadin yana prison an kamashi akan abunda ya aikata mishi, tare da fadin da farko anso a sakoshi duba da yanda yake babban mutum, shine nace zan shiga media in fada sannan in fadi dalilin da yasa ya harbeka shine fah maganan tayi shuru ana shirin kai maganan koto yanzu

GIDAN KASHE AHUOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz