5

5.1K 129 7
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*



*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*




*DEDICATED TO.....*
*AYSHA A BAGUDU*


*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*


*PAGE 5*





David ne ya shigo dakin domin yaji ta dade a ciki, ganin tana zaune a kasa tana rusgan kuka kaman ranta zai fita, yasa ya karasa inda take tare da fadin Afrah maiya faru cikin tashin hankali yake tambayanta ganin bata kulashi ba yasa yace ko hannun ne???

Wani irin kallo tamai cikin tsana tare da tashi ta fara daukan jakarta ta nufi kofar falon

Da sauri ya shiga gabanta yana fadin Afrah maiya faru?? Plz tell me, kin sani cikin damuwa..... ya karasa maganan cikin damuwa da tashin hankali

Ganin yasha gabanta bashi da niyan matsa mata yasa tace David ka matsa min ina bukatar in wuce

Galalo yayi yana kallonta cikin mamaki, tare da tambayan kanshi maiya sameta haka??

Wucewa tayi inda tayi dakin da Aysha take tace ta fito su wuce

Aysha tashi tayi tana tsaki tare da fadin kai naji dadin bacci wlh, bari in watsa ruwa

Afrah tace ban tunanin zan iya jiranki, sai mun hade kawai a Skul, tana fadin haka tabar mata dakin

Aysha tace ke kika sani, nidai ban fita sai nayi wanka wlh, har abinci sai naci tun dazu nake ta jiyo kamshi

Koda Afrah tayi waje ta nufi kofar fita amma sai taji a kulle, kallon David tayi dake zaune yana kallonta, tace ka bude min kofa in wuce

Yace Afrah zan bude miki amma you have to eat, sannan ki fadamin maike  damunki kafin in barki ki tafi

Wani irin kallo tayi mishi tare da nufanshi tana fadin mai yasa sai kaji abunda yake damuna, and k...... had'a idon da sukayi yasa ta kasa magana domin yayi mata kwarjini sosai, da sauri ta lumshe ido

David ganin haka ya matsa kusa da ita tare da saka hannunshi akan kafadanta ya janyota jikinsa inda ta fada kan jikinsa ya manneta sosai

A hankali ya fara magana kaman haka..... Afrah plz kiyi hakuri kici abinci before you leave am begging you

Gaba daya kasa magana tayi, inda take manne a jikin nasa, lokaci daya ta saka hannunta wanda ta manta taji ciwo ta tureshi..... aida sauri ta saki kara tare da fadin ahhhh sai kuma ta saki kuka mai sauti

Jin haka David ya kara rudewa inda yaita bata hakuri, babu yanda ta iya dole ta hakura inda suka nufi inda aka jera abincin ya zaunar da ita tare da zuba mata chips nd egg sai farfesun kazan da akayi, tare da hada mata tea, ya tura mata gabanta, gaba daya tsura mata ido yayi yana kallonta

Fara ci tayi a hankali, inda ta dago taga ita yake kallo, da sauri ta juyar da kanta gefe, cikin ranta tace kai wannan ko jarababbe, ji yanda yake ta kallona kaman me, sai wani manne min yake shi'a dole baya son in tafi, uhm ai idan na tafi kaida ka ganni hmmm tayu har abada......

Maganan Aysha ne ya katse mata tunani inda take fadin baki tafi ba???

Afrah bata ko kalleta ba, balle ta bata amsa, sai abincinta da taci gaba daci

Zama itama Aysha tayi inda ta fara zuba abinci, bayan ta gaida David ya amsa cikin sakin Fuska

Afrah lokaci daya ta tashi alaman ta koshi, idon David na kanta, yace Afrah badai kin koshi ba??

Eh kawai tace a takaice

Tashi yayi ya nufeta tare da fadin plz i need to talk to you in private

Kaman bazata bishi ba, komai ta tuna kuma tabi bayanshi, sukai bedroom dinshi, koda suka shiga idonshi na cikin nata ya fara magana da fadin Afrah plz maiya sameki lokaci daya kika canza???

Baki ta dan tabe tare da fadin babu komai, kawai ina son tafiya Skul ne

Shuru yayi yana kallonta kaman yana nazarinta, can yace are you sure???

Tace eh

Cewa yayi ta bashi number dinta, fada mai tayi inda ya fara rubutawa tare dayin saving

Fitowa sukayi inda Aysha itama ta gama, nan suka fita inda yace shine zai kaisu skul din, domin bazai bar Afrah ta shiga motar haya ba a irin wannan yanayin

Fita sukayi saida ya biya bank, sannan suka wuce, inda yake ta sharara gudu, yayinda waka take ta tashi a cikin motar, har cikin skul din ya saukesu, tare daba Aysha kudi yace tasa kati, Afrah tana  kokarin fita itama ya kira sunanta, wanda yasa dole ta tsaya cak

Yace Afrah plz inna miki wani abu am so sorry

Ido ta lumshe domin lokaci daya taji ya bata tausayi, yanda duk ya shiga damuwa ganin ta canza

A hankali ta furta bakamin komai ba

Hannunta ya riko tare da fadin, i love you baby, you are so swt

Murmushi tayi tare da fadin thanks, kudi ya bata wanda yake a cikin leda, tare da bata maganinta, yace sai munyi waya koh??

Kaita daga mai sannan ta fita inda tayi ciki

David da ido ya bita harta bace mai, a hankali ya furta what wrong with me?? Mai yasa na damu da ita haka?? A hankali yace just saboda ta karye a gidana nake jin tausayinta, murmushi yayi tare da fadin yeah hakane, kai tsaye ya tada motar inda ya nufi hanyar komawa kaduna


AS ne zaune a office dinshi, yana duba wasu file daga ganin alama suna da matukar muhimmanci takardun da yake dubawa

Nocking akayi mishi yace yes, shigowa akayi, wata yarinya ce hannunta dauke da coffee tana tafiya tare da rangwada, amma AS bai dago ba balle yasan tanayi, gab dashi ta nufa inda ta ajiye mai coffee din tana wani dan goga jikinta a nashi, lokaci daya ta fara fadin ga coffee din Sir

Sai a sannan yayi magana tare da fadin you can leave

Mai yakon ta tafi kaman yanda ya umarta, tsautsayi ya jata dauko coffee din zata bashi wai a baki aiko cup din ya kufce daga hannunta ya zube akan takardun da yake dubawa.......

Wani irin tashi yayi cikin fushi idonshi ya rune yayi ja, domin wannan takardun masu matukar muhimmanci ne a garesa.... tas tas har sau biyu ya sakan mata mari tare da fadin kina da hankali kuwa?? Kin san mai kika aikata?? Hannunshi ya daura akan goshi tare da fadin oh my God...... lokaci daya ya bude idonshi ya sauka a kanta, tare da fadin let me tell you na koreki daga wannan company din karki bari in k'ara ganin wannan ugly face dinnan naki

Yarinyar ta fara fadin please am sorry sir, plz sir dont fire me......

Telephone ya danna tare da sawa a kunnenshi yace come to my office right now, yana fadin hakan ya ajiye wayar

Aiko ko minti daya baiyi ba saiga security sun shigo su biyu suna fadin Sir

AS yace take this girl out of hare, and karku kara bari ta shigo cikin wannan company din

Yarinyar tana kuka take fadin sir i apologize plz forgive me, your love push me to...... janta security din sukayi suka fitar da ita waje

AS gaba daya ranshi a jagule yake, wannan takardan ya kunshi abubuwa masu girma cikin rayuwarshi, domin yana  daya daga cikin abunda ya zaunar dashi a garin kaduna..... tsaki ya saki mai cin rai lokaci daya kuma ya buga table dinshi tare da watsar da kayan kai yana fadin why will i leave her to go free??  She has to be punished..... zuciyarshi tace you punished her tunda ka koreta.... da sauri yace no wannan ba punishment bane, i will destroy her completely......

Waye AS???? Mu hade a next page domin ji




*MARYAM OBAM*

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now