16

2.8K 100 12
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*KHADIJA SULAIMAN JAGINDI*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*



*PAGE 16*






Afrah gaba D'aya hankalinta yayi Kan hjy Fatima domin son sanin abunda yake boye

Hjy Fatima ta fara magana kaman haka shekaru ishrin da suka wuce baya......... Mama ce ta katse hjy Fatima da fadin Dan Allah hjy Karki saka zargi a cikin zuciyar y'ay'anmu Karki saka su zargemu akan abunda kuke zarginmu akai, wlh wlh ban aikata wani......  Hjy Fatima tace dakata Hafsat dakata Karki Kuma magana, Koda yake ai bazaki so in Fadi abunda kuke boyema yaranku ba, shikenan nayi shuru Amma bari kiji komin Daren dad'ewa gaskiya zata fito, Kuma wlh duk abunda kake boyewa wata Rana zai bayyana, kallon Abba tayi tace Kai Kuma mijin tace gaka gata saika zauna da ita...... Ajiyan zuciya ta sauke bayan ta sauke ma Abba wani uban harara sannan ta daura da fadin nazo ne akan walimar wannan yarinyar domin akwai baki da zanyi za su Kuma halarta, bana bukatar abun kunya banso kuyi komai na abinci zan dauki nauyi, karku dauka wani abu yasa nayi, a'a saboda bak'ina nayi, tana fadin haka tayi gaba

Har takai bakin kofa ta tsaya cak tare da waigowa tace gobe ku shirya ku dawo gidana a can za'ayi taron bayan walima saiku dawo, tana Gama fadin haka tai gaba

Afrah kam gaba D'aya komai nata ya tsaya cak, babu komai cikin ranta sai tunani da tarin tambayoyi da take bukatar amsar su a halin yanzu, lokaci Daya ta fara girgiza Kai tana fadin no, no ba haka bane no hakan bazai taba faruwa ba inada asali inada tushe......

Gaba D'aya idon kowa na kanta iya tashin hankali iyayenta sun shiga sosai, Mama ce ta matsa kusa da ita tare da riketa tana fadin Afrah Afrah.... 

Wani irin kuka mai karfi Afrah ta saki Mai ban tausayi tare da fadin Mama Dan Allah Dan sonki da Annabin rahma (S A W) ki fiddani cikin rudani da wasi wasi, ki fadamun abunda nake son sani, Mama Ina cikin tashin hankali Ina cikin rud'ani Dan Allah Mama ki taimaki rayuwata ki fadamun abunda nake son sani, inaji a jiki na Bata aure aka sameni ba, inaji a jikina abuwawa da dama namin yawo cikin kaina, ko tsintata kukayi Dan Allah ku taimaki rayuwata ku fadamun abunda n.......  Ido ta lumshe lokaci Daya ta fara yunkurin fad'i inda ta tafi luuuuuu  Amma Mama ta riketa tana Kiran sunanta haka Shima Abba da zainab, Amma Ina Bata masan sunayi ba domin Bata San inda kanta yake ba.....

Koda Afrah ta farka ta tashi ta ganta a kwance a asibiti, hannunta na dauke da drip da aka saka mata, ga iyayenta Nan sunyi cirko cirko cikin tashin hankali da damuwa, lokaci Daya ta rufe ido tare da tuno abun Daya faru, hawaye ta farayi sheshekar kukanta yasa suka farga data farka inda Abba ya Riga zuwa wajanta ya fara magana tare da fadin Afrah kibar wannan kukan ya kamata ki cire komai cikin ranki

Cikin kuka tace toh Abba zanyi yanda kace, Amma abun zai tsaya mun a Rai, Abba wlh Koda ban furta ba abun zaiyi ta cina a cikin Rai, Abba indai shurun nawa shine zai saku farin ciki toh nayi bazan Kara magana a kai ba, Koda kuwa zuciyata zata fashe da tunanin abun......

Mama cikin hawaye tace Afrah zan fada Miki komai Amma inaso ki yarda Dani, inaso kiyi mana kyakyawan fahimta inaso ki yarda da kaddara......

Shekaru ishrin baya da suka wuce...........

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now