22

1.9K 108 11
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 22*

Mas'ud sun Isa garin Zaria very late dan haka kai tsaye hotel ya nufa domin ya kama daki, a matukar gajiye yake sosai, burinshi bai wuce ya ganshi a kwance ba Yana hutawa ba, koda ya kama daki, saida yayi wanka kafin ya Kira waya aka kawo mai abinci, bayan ya ci ya samu ya kwanta Amma gaba daya baccin yaki daukanshi, sai faman juye juye yake ba komai yake tunani ba sai ranan daya afka ma yarinyar da bataji ba Bata gani ba duk saboda malaminshi yace mishi sai ya aikata hakan kafin ya haye......... Kalmar Innalillahi wa Inna ilaihira jiun ya furta tare da fadin maina aikata haka? Maina aikata na cuci kaina da kaina

Haka yaita sakawa da warwarewa tabbas bazai taba samun salama ba har Sai yaga wannan yarinyar ya roki gafararta tare dana iyayenta, domin yasan duk inda take tana kullace dashi haka ma iyayenta, bazai taba manta fuskanta ba har abada

Washe gari tunda Afrah ta tashi da asuba Bata koma bacci ba, jin jikinta take wani irin sakayau kaman an cire mata wani abu mai nauyi a jikinta, Aysha ce ta kalleta tare da fadin ya jikin naki

Ta amsa da Fadin da sauki, sai dai gaba daya jikina ji nake kaman an cire mun wani abu, jina nake babu nauyi

Aysha tace sai hakuri dama haka zakiji kafin daga baya ki koma normal ...... Nocking sukaji wanda yasa Aysha tashi ta nufi kofar tare da budewa

David suka gani sanye yake da kananan kaya, yayi matukar kyau hannunshi yasa agogon rolex, Amma wannan karan baisa chain din daya saba sawa ba, kamshin turaren shine ya cika dakin idonshi nakan Afrah

Aysha ta gaidashi ya amsa tare da tambayarta ya jikin Afrah din??

Tace da sauki

Karasawa yayi kusa da Afrah tare da zama dan nesa da ita Yana kallonta, lokaci daya duka suka bude baki wajen gaisuwa

Jin sun hada baki yasa sukayi murmushi, yace ya jikin naki

Tace naji sauki, hope kaina jikinka da sauki

Yace eh da sauki, in ina tare dake bana jin wani damuwa tare dani

Murmushi tayi..... Aysha tace bari inje in dawo inada lecture, Afrah tace ok sai kin dawo

David ya dauko kudi ya Bata tare da fadin tayi kudin mota, bayan ta amsa tayi godiya tare da fita

David kallon Afrah yayi tare da fadin kinyi breakfast kuwa??

Kaita girgiza mishi alaman a'a,

Yace why? Mai yasa bazaki ci abibci kisha magani ba, telephone din yayi dialing tare da fadin abunda za'a kawo

Bayan ya gama wayar ya zauna Yana ta janta da fira har aka kawo abincin taci sannan ya tambayeta ina maganinta? Nuna mishi tayi da hannunta tashi yayi ya dauko maganin tare da ruwa ya kawo mata, tare da Bata maganin tasha, saida ta gama ya amsa sauran ruwan ya ajiye, sannan ya kalleta tare da fadin Afrah ina son muyi magana mai matukar muhimmanci

Kallonshi tayi taga ita yake kallo dan haka ta dan juyar dakai inda lokaci daya taji ya ruko hannunta komai ya tuna kuma ya saki hannun nata oho, magana ya fara cikin wata irin murya kaman mai rada.....

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now