43

302 10 0
                                    

Ai cikin wani irin razanannen ihu ta ruga da gudu wajansa, tana kuka tare da bugun kirjinsa tana fadin muhd ka tashi Dan Allah muhd ka tashi kuka take sosai yayin da mutane suka karasa wajan inda wasu sukai kokarin daukar wayarsa suka kira number din asibiti,

Nadia taita Bata hakuri Akan tayi shuru ta daina kuka, duk da ita Nadia din Bata San koshi mohd din waye ba a wajan Afrah, motar asibiti tazo inda ta dauki David suma su Afrah da Nadia suka bi motar asibiti din

Koda suka karasa emergency akai da David din, duk wani mutum in zashi wata kasa karatu sai an bada rahoton lafiyarsa ga kasar domin Koda ciwonshi ya tashi su San kan matsalan ba tare da an Bata lokaci ba, Dan haka likitoci suka fara duba David a kalla sunyi wajan minti 40 suna dubasa Amma ina David Bai motsa ba.

Hankalin afrah in yayi dubu ya tashi, Nadia itama ganin halin da afrah ta shiga yasa ta fara tausayawa muhd din duk da Bata sanshi ba, duk Zaman da Nadia da Afrah suke Bata taba fada Mata ita matar aure ceba, hasali ma ita Nadia tana daukar Afrah a budurwa tana ganin kaman gidan Yan uwanta take zaune duk da basu taba maganan ba, domin cikinsu babu Wanda ya taba zuwa gidan kowa

David da idonsa ke rufe likitoci na kansa, da sauri ya farka tare da fadin Afrah cikin firgici da ihu, sunan Afrah yaita kira yana fisge fisge nan Dai aka samu aka Mai allura Wanda ko minti biyu Bai Kara ba, bacci yayi gaba dashi

Koda Dr's din suka fito Afrah nufansu tayi tana tambayansu ya mohd dinta, sun gane Wanda take magana Dan haka daya daga cikin Dr's din ya tsaya tare da fadin ya samu yayi bacci Amma wacece Fira something lyk that naji yana fadi

Afrah tace Dr Afrah Dr yace yes waye Mai wannan sunan, Afrah tace nice Dr, Kai Dr din ya daga tare da fadin kizo muje ki zauna dashi yanda daga ya tashi zai ganki, daga duka alamu ya tuna abunda ya manta, kaman yanda na gani yayi losing memory d'inshi a wani hatsari da yayi tun a najeriya Amma yanzu ina tunanin ya tuna komai

Afrah wani shock taji tare da fadin Dr kana nufin mohd yayi losing memory d'inshi, Kenan ya mance komai yanzu ne ya tuna??

Dr yace eh Amma a yanda Naga file d'inshi ba komai ya manta ba a lokacin da yayi hatsari ya manta wani bangare ne na rayuwarsa

Wani hawaye ne yake fita daga idonta tana kuka kuma tana dariya tare da fadin dama na sani, haka kawai muhd bazai manta dani ba, muhd yana sona sosai, sai a sannan Nadia ta fahimci cewa saurayin Afrah dinne

Dr ya kaisu Dakin da David din yake tare da fadin Kar suyi surutu plz, su bari Har alluran ya sakeshi Ya farka da kansa

Nan Afrah ta amsa da OK sannan Dr din ya fita, Nadia ta kalli Afrah tare da fadin Afrah wannan Dai duka alamu sun nuna shine na hannun daman shine baki taba bani labarinsa ba

Afrah cikin da sassan muryanta da Tasha kuka tace Nadia labari ne Mai tsawo, Amma ina son ki sani wannan da kike gani shine rayuwa ta, ina matukar kaunarsa, Nadia kin taba soyayya?

Nadia murmushi tayi tare da fadin Afrah nasan yanda kikeji na kuma fahimceki....... Shuru tayi tana kallon Afrah lokaci daya Kuma ta daura da Kara fadin Afrah so na tsani wannan kalman domin taso tarwatsa mun rayuwa....... Farkawan David yasa Nadia yin shuru tare da kallonsa

David hannunsa ya Bude alaman Afrah Tazo garesa, Aida gudunta ta nufeshi cikin kuka tare da fadawa jikinsa tana fadin muhd yanzu ka tunani muhd nayi kewarka, sonka yaso illatani

Wani irin Kara matseta yayi a jikinsa yana hawaye, lokaci daya ya fara magana ta setin kunnanta da fadin Afrah hatsarin da mukayi shine Har saida aka kawo ni kasar waje

Cikin kuka tace a'a muhd tana kuka tana bashi labarin Abunda ya faru lokaci daya ta fara Jan jikinta Daga nashi tana fadin muhd a ranar bayan abun ya faru ka nuna baka Sanni ba a ranar da mukai wannan mummunan hatsari aka....... Shuru kuma tayi tunawa yana kwance Akan gadon asibiti inta fada mishi komai zai iya faruwa.....

GIDAN KASHE AHUΌπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα