45

301 9 1
                                    

Wani irin razana tayi dajin kalman daya fito daga bakinsa, yayinda takeji kaman ba Hakan ya furta ba, kawai tana hasashen Hakan ya fada ne bata dada tsinkewa ba Saida ta Kuma Jin muryansa ya Kara fadin Afrah Ina sonki...... Aida sauri ta tashi daga jikinsa tare da kokarin dagawa daga jikinsa duka, Kara manneta yayi a jikinsa Tare da fadin Afrah yau zan fada miki abunda na dade Ina boyewa, bazan iya cigaba da boye Miki ba, na fara sonki tun daga ranar Dana fara ganinki a lokacin kin fito kina waya har kika koma gida aka baki sako ki kawo mota wanda a ranar ne ni dake muka samu matsala........ Dakatar dashi tayi da fadin ya Isa haka bana bukatar Jin wannan kalma daga gareka, mai yasa kake kokarin tsara mun labari saboda duk saboda kasa inji dadi saboda Ina dauke da cikinka?

Bari kaji daka sani baka bata bakinka ba wajan fadin wannan tsararran labarin karka manta kaine mutum na farko daya taba furta mun kalman tsana ido da ido, kaine mutum na farko da kace baka taba Sona ba, kaine mutumin da kace ka aureni ne domin biyan bukatan kanka, sannan yanzu kazo kace kana sona rana tsaka, tashi tayi daga jikinsa fuskanta na zubda hawaye tace wannan yaudara ne, karka kuma fadamun haka, ni nasan na rasa wannan kalman daga bakin masu Sona daga ranan Dana aureka, sannan karka manta duk bakin daya furta kalman kiyayya daga baya yace kuma yana kaunar mutum toh karya ne yaudara ne kawai, wanda ya kika tun farko har abada bazai taba sonka ba, dafe cikinta tayi tace nasan saboda shine kake fadin haka ina so ka sani bazan taba cutar da wannan cikin ba, sannan insha Allah zan haiyu lafiya in raini abunda na haifa sai dai zan maka alkawarin abu guda daya shine zan boye ma abunda muka haifa cewa ni dakai zaman kiyayya mukeyi......

Nufanta yayi tare da fadin Afrah ina so ki sani, shi kiyayya tana zama soyayya haka soyayya tana zama kiyayya, duk yanda zuciya takai da tsanar mutum indai yana samun kyautatawa toh wannan tsanar tana zama soyayya, sai yasa Annabi muhd S A W yace idan zaka ki mutum ka kishi sama sama, haka idan zaka so mutum ka soshi sama sama, domin wannan kiyayyar takan zama soyayya haka zalika wannan soyayyar takan zama kiyayya, ni nasan da farko na nuna miki tsana amma baki san miye a zuciya na ba.....

Ban sani ba sannan bana fatan in sani Abubakar kaman yanda nayi alkawari tun farko zan zauna dakai badan ina sonka ba, sai dan hakan shine kaddara ta, masana so sunce so daya ne babu na biyunshi..... Inko haka masana so suka furta to zan iya cewa sunyi kuskure ko kuma ince kece kikai kuskure Afrah so tsuntsune yana tashi daga Wani waje ya dawo wani waje

Dan shuru yayi sannan yaci gaba da fadin, ban taba tunanin zan taba bayyana soyayya ta a gareki ba, Amma gashi na furta kina karyata soyayya ta, Afrah soyayya ta a gareki gaskiya ce babu yaudara

Murmushi tayi tare da fadin wow wow, kayi kokari kaman yanda ka fada kace ka fara sona tun ranar daka ganni inda dagaske ne Bai kamata ka auri wacce kake soba ta wannan hanyar daka aure niba..... Kuka ta saki tana fadin ka rusa mun farin ciki na, kasa na rasa komai nawa, kasa rayuwa na cikin kunci ka bata mun duk wani Jin dadi na duniya ta gashi tana kokarin Bata mun lahira na, Abubakar you are a selfish kana da son kanka, baka taba zama dani once kayi magana dani ba akan kana son aure na ba sai dai kawai naji an daura aure which babu wanda ya fadamun saida nazo. ........ Nasan baka san miye soba inda kasan miye so toh da baka aureni ta haka ba, har gobe bazan daina tuna wannan kalmar ba ka aureni ne badan kana sona ba sai dan daukar fansa akan abunda nayi maka lallai Duniya gidan kashe ahu, ka aureni a lokacin da kake bukata kuma kaso duk saboda ni bani da gata

Yace look Afrah ki daina wadannan maganan marasa amfani, abunda nake fada miki gaskiya ne, bance dole ki yarda ba, Amma what I'm telling you is from the bottom of my heart

Sannan maganan aure na dake da farko na dauka dan in dauki fansa yasa nace zan aureki saida na aurekin na gane na fara sonki ne tun daga ranar farko, Afrah abubuwa da dama nawa sun canza saboda ke, yanzu na koma wani sabon mutum daban duk saboda sonda nake miki, Afrah kina da Daman da zaki fadi abubuwa a kaina sabo....... Ja da baya tayi tare da fadin ka soni ko karka soni zan zauna dakai inyi maka biyayya Amma maganan so ka daina fadi domin ni bazan taba sonka ba tsananka ce a cikin Raina kullum, bana kaunar in ganni cikin wannan gidan Amma babu yanda na iya haka Allah ya tsara mun, karka dauka abubuwan da nake maka akwai wani abu ne a cikin rai na babu ina kokarin sauke hakkin ka dake kaina sannan......

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now