27

2.4K 103 37
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 27*


Ambulance din na tsayawa suka nufeta su duka sai dai police din sun dakatar dasu daga karasawa kusa da wajen, inda AS shi kam yana nan tsaye kaman mutum mutumi a tsaye a wajan ya kasa gaba balle baya domin gaba daya jin jikinshi yake a sake babu wani kwari, Kamal ne ya dafa kafadarshi tare da kiran sunanshi da AS kazo mu karasa, bai kula kamal ba haka bai motsa ba, domin baya tunanin zai iya motsawa, ganin haka yasa kamal jan hannunshi sukai gaba wanda a dai dai lokacin aka fito dasu sai dai ga duka mamaki yanda na gansu akwai rai a jikinsu domin su duka drip ne a hannunsu an makala musu. Kowa ajiyan zuciya yaita saukewa ganin basu mutu ba, nan akai ciki dasu sai dai gaba daya jini ya bata musu jiki.

AS kam ajiyan zuciya yaita saukewa, ga wani abu da yake kokarin tsaya mishi a zuciya tare da tambayar kanshi shin wanene namijin da aka kawo su tare?? Ido ya lumshe tare da fadin may be shine driver din motar ta dauki drop ne hala, wannan tunanin da yayi yasa ya kawar da komai a cikin ransa na tunanin ko waye ke tare da ita.

Bayan an shigar dasu aka fara dubasu, Wanda su duka da farko sunyi doguwar suma ne wanda firgici yasa sukai hakan, Afrah bata wani Dadeba ta farka tana kiran David David move the car...... Wani irin ihu ta saki mai firgitarwa wanda hakan yasa duk wanda ke kofar emergency din suka ji harya janyo hankalin iyayenta dake kusa da wajen suka matsa kusa da window suna kallon yanda take fusge fusge, gaba daya kuka suke saki ciki harda hjy Fatima, AS kam har yanzu jinshi yake wani iri......

Ganin irin ihun da take hadi da kiran David yasa aka mata allura, ai nan take bacci yayi awon gaba da ita.

Iyayen David jirgi suka biyo basuyi 1hr ba sai gasu sun iso, cikin ikon Allah da tambaya aka sadasu da inda Emergency yake, ai kai tsaye nan suka nufa cikin tashin hankali, a lokacin an samu an fara kokarinshawo kan matsalan sai dai ana jiran farkawansu musamman ma David wanda har yanzu bai farka ba, a dai dai lokacin Dr ya fito inda iyayen Afrah suka nufeshi wanda hakan yayi dai dai da zuwan su iyayen David dinma, nan suka fara tambayan ya jikin Afrah??

Muryan mahaifin David shima naji yana tambayan Dr ya yaro na wanda sukai accident shida wata yarinya a hanyar zuwansu kano??

Doctor yace duka da sauki sai dai shi namijin ne bai farka..... Ihun David dinne yasa dr shiga da sauri ai suma mara musu baya sukayi, nan ya fara fusge fusge yana kallon dakin alaman bai san inda yake ba, nan Dr's suka fara kamashi domin kokarin bashi taimakon gaggawa, amma ganin yaki nutsuwa sai faman fusge fusge yake yasa dole suka mai allura wanda yasa hakan duk wani jijiya dake jikinsa fara saki har bacci ya daukeshi na dole, gaba daya duk wannan abunda akeyi a gaban iyayensu ne, yayin da Dad din David ya matsa kusa da dan nashi dake bacci ya fara magana da fadin ya jikin yaro na maike damunshi? tare da nuna Afrah dake baccin wahala jikinta duk jini ya fara fadin duk itace silan fadawan dana wannan matsala duk itace sanadi i hate that girl if anything happens to my son she will pay for it, i promise

Gaba daya kowa kallonshi yake a dakin, AS kam kanshi ne ya kulle inda ya fara jero ma kanshi tambayoyin da bashi da amsar su, miye alakanta da wadannan mutanan daya tabbata ba musulmai bane, har suke ikirarin itace silan fadawan dansu wannan halin?? Toh miye dangartakarsu haka?? Haka yaita jerowa kansa wannan tambayoyin da bashi da amsarsu........ Maganan Dad din David dinne yasa ya dawo daga duniyar tunanin daya fada inda yake fadin shi zai dauke dansa daga nan domin bazai iya barinshi kusa da wannan yarinyar ba, Hjy Fatima ce ta katseshi da fadin wai miye haka yake fada ne akan yarta?? Ba Mama ba harta abba saida yayi mamakin jin hjy Fatima ta kira Afrah da yarta ikon Allah wai yau hjy fatima da kanta take kiran Afrah da yarta iko sai Allah

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now