41

299 11 0
                                    

Wani irin kallo ya wurga mata lokaci daya ya matso gab da ita tare da fadin ke har kina da bakin magana? Karki mance ni namiji ne komai nayi ado ne inni virgin ne ko ba virgin ba babu wanda zai gane, sannan inaso ki sani....

Dakatar dashi tayi da fadin abunda ke cutar da yawa daga cikin al'umma kenan, maza kuna dauka idan kukayi zina kaman ba komai bane idan mace tayi shine laifi, toh bari kaji in fada maka da mace dana mijin duka laifinsu daya, kuma inaso ka sani har gobe bazan fasa kiranka dan bariki ba indai har zaka ce mun I'm not a virgin....

Shut up yimin shuru, lallai na yarda macen bariki bata da kunya, a kawo ki gidan miji amma ya jiki empty babu ko kunya kizo kina surutu dan ki tabbatar ke din cikakkiyar yar duniya ce

Eh ni yar duniya ce, kuma banzo da budurci na ba sai me, ai dama mazinaci saida mazinaciya kai kayi zaton kaci na wasu ka samu budurwa karya kake ba'a ma Allah wayau, fasiki kawai

Mari ya sakar mata tare da fadin ki dinga sanin kalman da zaki dinga fadamun

Murmushi tayi hannunta na rike da kumcinta tana hawaye tace dama iyakar abun kace zaka mareni, kuma wannan dabi'ar namijin da bai san darajan mace bane, kuma duk wanda bai daraja mace wulakantacce ne......

Daga hannu ya kumayi zai mareta ya kuma fasa tare da daura hannunsa biyu akan kugunsa ya juya baya yana huci tare da fitar numfashi mai zafi ta bakinsa lokaci daya kuma ya waigo ya kalleta tare da fadin wata rana wannan bakin naki saiya kashe ki, ke kin san darajan kanki ne? Ki fara sanin hakkin Allah akan ki kafin kisan darajan kanki domin wannan abun da kike na tabbata jahilci na damunki a kanki domin mace jahila ce bata daraja mijinta inda kin san hakkin aure bazan fada kina fada ba

Hawaye takeyi tare da tuna alkawarin da tama Mama, ai gabanta taji ya yanke ya fadi, lallai maganan As hakane inko taci gaba da biye mishi yana fada tana fada saiya kaita wuta..... Katseta yayi da fadin kina da aure kina tunanin wani gardi which mace mai ilimi bazata yiba har kina saka kayan daya baki, kuma kike fada shiya siya miki tun daga lokacin na tabbatar akwai jahilci a tattare dake ssnnan kuma inaso ki rubuta ki ajiye karki dauka abunda nake miki sonki nake ban taba sonki ba dede da second daya ban taba jin ina sonki ba, balle yanzu da najiki a empty inda kin san yanda na kara tsanarki...... Shuru yayi lokaci daya kuma ya kura mata ido yace Afrah na tsaneki na tsani kallonki ko kallon fuskanki bana kaunaryi ta sanadinki kinsa komai nawa ya canza I hate you dole inje inyi HIV test........ Yana fadin haka ya fita fuuuuuuuuuu

Ita kam kasa tayi tana rusga kuka mai cin rai tare da fadin dama nasan baka kaunata, koda baka fada ba na sani, muhd kam da yake shi yana kaunata yasan niba virgin bace still ya nuna yana kaunata kuma a hakan yace zai aure ni, kuma ya kamata ya mata uziri duk da ya jita a ba budurwa ba, itama inda badan kaddara ya fada mata ba aida ko giya tasha bazata iya aikata zina ba, hawaye mai zafi ke fitan mata a ido tare da kara yin data sanin rayuwarta ta baya, tabbas inda yau tana da budurcinta da ta samu bakin gaya mai magana amma ina bata da baki yanzu sai dai hakan bashi ne zaisa inya mata abu tayi shuru ba...... Wata zuciyar tace ke Afrah mijinki ne kiji tsoran Allah komai zai fada miki ki dinga banza dashi Allah yana tare damai hakuri, yayin da wata zuciyar ke kara zugata akan karta raga masa Koda wasa domin inta raga mai sai yayi mugun takata ta yanda taso, tunanin alkawarin da tayi ma mama ne ya kara fado mata inda take cewa zatai biyayya ga aurenta domin raya sunnan ma'aiki ai tuni ta saki sabon kuka tana fadin Allah na tuba kalmomin da nake fada mishi sunyi muni a matsayinsa na mijina basu dace dashi ba, tabbas in ban kiyaye harshe na ba toh zasu kaini ga halaka ya kamata in amshi rayuwa a duk yanda tazo mun aure an daura bani da wani mafita face hakuri, zuciyarta ce ta jefo mata tambaya da yaya zakiyi da son muhd dinki??

Lumshe ido tayi tare da fadin muhd har gobe ina sonsa, sai dai bani da wani mafita a yanzu face in amshi gaskiya da kuma kaddara ta a yanda ta fado mun, daga hannunta tayi sama tana kuka tare da fadin ya ubangiji mai sammai da kassai ya Allahu ya rahmanu, ya gafuru, ya malikul diljalalu Wal ikram, na rokeka badan niba badan kuma na isa ba, Allah yanda na amshi wannan auren na kuma yi imani da kaddara Allah ka bani juriya da hakurin cin wannan jarabawa, kaba muhd macen data fini a komai ka bashi mace saliha albarkacin shigarsa musulunci ya Allah ka bashi mace hafiza da zata koyar dashi ilimin addini, wacce zata haifa masa yara hafizai, Allah Ameen, Allah ka bani juriya sannan Allah ina mai kara neman alfarma a gareka kace mu kiraka zaka amsa, Allah yau ga baiwarka giwowina a kasa ina mai rokanka da kar kasa inyi rayuwa mai zurfi Allah kasa bani da sauran shekaru masu yawa a gaba, ya Allah ka amsa mun wannan addu'a tawa Allah ka dauki raina in huta da wannan duniyar, wlh zuciya ta da tunani na sunyi karamin daukar wannan abubuwa da suke ta tunkaro ni, ya ubangiji bawai banyi imani da tawa kaddarar bane nayi, ya Allah kaine masanin abunda ke boye da kuma wanda ke bayyane, kasan yanda nakeji ya ubangiji ka amsa mun addu'a ta. Lokaci daya zazzabi ya rufeta a wajan inda ta samu dakyar ta lallaba tayi gadon dakin ta rufe jikinta tare da rawar sanyi har hakoranta hadewa suke suna bugawa saboda sanyi

Shi kam As bayan ya gama wanka kwanciya yayi tare da lumshe ido amma me? Fuskan Afrah ke mishi yawo a idonsa da sauri ya bude ido tare da fadin maike damuna bana son ganinta, bana son koda ganin fuskanta, wani irin mugun kishi yakeji yana ratsashi inya tuna fanko ce an gama kwakwuleta tun a waje sai yaji ranshi yana baci tare da suka, yanzu raguwar wasu ya aura?? Dama dole idonta ya bude irin wannan fitsaran da take nunawa a gaban kowa, shuru yayi yana nazari lokaci daya ya tashi tare da fadin tabbas hakane dama in baka auri wacce ka lalata ba zaka auri wacce wani ya lalata, lallai Allah yayi gaskiya fasiki sai da fasika, haka zalika saliha saida salihi, tabbas yayi sex da mata daban daban toh amma duk matan da nayi sex dasu ba virgin bane na samesu suna abunsu bani bane silan lalacewarsu ba, mai yasa zan auri fasika...... Uhm As kenan kai kana nufin kayi zina da yaran wasu duk da kana ikirarin ka samesu suna yi, Allah ba'a masa wayau, duk abunda kayi saika girbi dai dai da abunda ka aikata, matasa yanzu sun maida yin zina a matsayin ado, idan mutum yayi zina yanzu baya jin kunyan fada in mace ce haka zata dinga bama kawayenta labari ai da mukaje ya cini kai iya iya sex, ko kuma kuji kai burarsa karama ce sai iyayi, haka suma maza suke fadi kai yarinyar tayi taji ruwa ai nasha dadi, ko kuma kai yarinyar so dry bata da ruwa duk taban wuya

Wannan wani irin zubda mutunci ne, manzon Allah yace a lokacin da mazinata ke aikata zina duka ana cire musu imaninsu, yanzu idan kanayi Allah ya dauki rayuwarka fah?? Wa iyazubillah mai zaka fadi ma Allah, ko mai zaki fadi ma Allah, sai yasa bala'oi keta faman yaduwa a kasa saboda zinace zinace madigo, luwadi sunyi yawa, kashe ran mumini, mai yasa Allah bazai jarabce mu ba??

Allah kasa mu dace

As duk yanda ya motsa fuskan Afrah ce a idonsa falo ya koma shima still ita yake kallo, dan haka ya nufi dakinta kai tsaye kunna wutar dakin yayi tare da fadin akan wani dalili kike mun gizau ki fita daga tunani na tun...... Ganin tana rawar sanyi yasa ya karasa gareta tare da fadin maike damunki bayan ya taba jikinta yaji zafi sosai, aida sauri ya tashi yaje ya dibo ruwa a roba da towel ya cire blanket din dake jikinta tare da cire yar karamar rigar baccinta tana kokarin rike mai hannu amma ta kasa harya cire dan kura ma jikinta ido yayi wani irin abu yaji yana sukarshi a zuciyarsa nan da nan idonshi ya kade tare da mikewa lokaci daya kuma ya zauna tare da daukar towel din yana daddana mata jikinta, abunda yake mata yasa zafin jikin nata ya fara sauka harta dan fara jin zafi, As kam yi mata kawai yake amma ranshi a jagule yake domin babu komai a ransa sai tsabaragen tsananta yi mata yake amma hankalinsa baya kanta har bacci ya dauketa bai sani ba, ajiye towel din yayi tare da kallonta yaga tana bacci dan gajeran tsaki yaja tare da barin dakin bayan ya rufeta da bargo ya kunna mata ac

Dakinsa ya nufa sai dai koda yaje ya kasa nutsuwa tunaninta yai tayi, Dan haka yaja gajeran tsaki tare da tashi ya koma dakin nata inda yaga duk ta yaye bargon daga jikinta, kuma still baccinta take, kusa da ita yaje ya kwanta tare da Kara rufeta da blanket din, yana Kwance yaji hannunta akanshi a zatonshi ta farka ne, Amma sai yaga sabanin haka baccinta takeyi Bai cire hannun nata daga jikinsa ba, Saima hannunta daya Kara matsewa a jikinsa, shida kanshi yana mamakin yanda zuciyarshi take mishi sauki Akanta duk da irin kullatanta da yayi, sai dai ya Alakanta hakan da tana bashi tausayi ne duba da yanda Bata da lafiya



David ne zaune cikin kananan kaya hannunsa, dauke da glass cup cikin cup din alcohol ne a cikinsa yana Sha, gefe guda kuma wata baturiya ce tana ta Faman shafa Mai jiki, lokaci daya ya tsayar da ita, domin bawai yana Jin dadin Yanda take mishi bane, ganin ya dakatar da ita yasa tayi Lau Lau da ido kaman zatai kuka, shi kam koh a jikinsa, Karan wayarsa yasa ya tashi tare da dauka, sunan Dad dinshi ya gani Dan haka ya dauka

Dad din yace my son how are you, da fatan kana lafiya

David yace eh Dad, ya mum

Tana lafiya muna ma tare na kira inma wani labari mai dadi, mun samar Maka Mata, kuma family dinta sun baka and she is beautiful zaka so ta sosai

David yace look Dad ka ajiye maganan nan a gefe Dad ina son in dawo gida wannan Yarinyar nan ta hospital da take cewa ta sanni Dad ina son ganinta ina yawan tunaninta dad ina tunanin ina sonta jiki na yana bani mun taba rayuwa nida ita a baya duk da banda tabbacin hakan wani irin ihu ya saka mai firgitarwa..........

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now