23

1.8K 111 34
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 23*

Dare ya tsala a lokacin da ko wani bawa yake bacci, cikin salama baka jin karan komai saina kukan tsintsaye Amma a wannan dare gaba daya zuciyoyi da dama sun kasa rintsawa, yayinda kowa yake ta saka da warwara a cikin ransa.....

AS ba komai bane cikin ranshi saina tunanin Afrah wacce gobe za'a daura musu aure, Yana tunanin wani irin rayuwa za suyi, musamman yanda yake shirin yin auren domin wulakanta ta, ya nuna mata kuskurenta tabbas saiya nuna mata shi yafi karfin ta kirashi driver, lumshe Ido yayi tare da fadin ita Bata ga irin haduwan da nayi ba har take kirana da driver ba?? Wani irin Ido gareta? Kodai tana da matsalan ido ne??? Haka yaita jero ma kanshi tambayoyi wanda bashi da amsarsu, lokaci daya ya bude idon nashi tare da furzar da iska mai zaifi, sai juyi yake akan makeken gadon dakinshi Amma ya kasa bacci gaba, lokaci daya ya tashi ya zauna Yana wani irin murmushi tare da ganin dare yayi mishi nisa domin burinshi yaga gari ya waye domin yaga an daura auren yaga yanda zata kasance.... Duk da wani gefe na zuciyarshi na fargaban auren da zaiyi tare da kuma gargadinshi akan kar yayi auren tunda bawai sonta yake ba, sai dai kuma yafi karkata akan ya aureta inya mata abunda yake bukata sai ya rabu da ita, wani irin dariya ya saki tare da fadin Yes dole in haiyu da ita zata haiyu da wanda ta Kira driver........

David Mohd kenan shi kam babu komai a ransa sai farin ciki wanda ya haddasa masa rashin bacci, sai juyi yake Yana murna tare da fadin wai yau nine musulmi lallai Allah abun godiya, tabbas gaskiya gaskiya ce komin dadewa, sai dai abu daya da yake tunawa shine yanda zai kaya da Dad dinshi idan yaji wai yau shi musulmi ne ya tabbata a ranan ba karamin tashin hankali zai biyo baya ba, inda ma zai tsaya a tashin hankali toh da yafi kowa murna Amma yasan dole zai hadu da alot of challenging wato kalu bale, duba da yadda mahaifinshi yake a cikin addinin daya bari, idi ya lumshe tare da fadin komai zai faru zan jure Koda kuwa hakan zaiyi barazana da rayuwata zan jure domin kuwa na riga na gane addinin muslinci shine haske kuma gaskiya........ Ta gefe data kuma Yana farin cikin zai samu Afrah tabbas yafi ko wani namiji sa'a samun mace kamar Afrah a rayuwarsa ba karamin nasara bane sosai, ya kosa gobe yayi yaje yaga danginta duk da zuciyarshi bai kwanta dayin tafiyar ba, domin Yana ganin kaman baza'a bashi itaba yadai yanke koma dai miye zasu kuma Yana fatan samun nasara....

Ta gefen uwar gayyar kuma wato Fatima Afrah, gaba daya a zaune take akan gadon dakin hotel din, ta kasa bacci tun Aysha na tambaya lafiya Bata kwanta ba har ta gaji ta barta tayi bacci abunta, Afrah na nan zaune, bini bini ta kalli agogon wayarta taga karfe nawa, a dubawan da tayi na karshe taga biyu saura mintuna, dan tsaki taja tare da fadin kai yau dare baya sauri, tashi tayi inda ta nufi toilet tayi alwala tazo ta fara Sallah saida tayi raka'a goma sannan ta fara addu'a sosai take addu'a kuma duk akan Allah ya mallaka mata David ne wato Mohd, ta dade tana addu'a tare da nema mishi tsari da kuma dauriya akan komai kafin ta kwanta a wajan Bata dadeba bacci yayi awon gaba da ita a wajan.......

Ta gefen Mas'ud kuwa shima dai juyi yake tayi akan gadon, gaba daya wannan dare ji yake yayi mishi tsawo, tabbas yau Yana cikin farin ciki domin yaga yarinyar da yake burin gani, wacce saboda tunanin ta hanyar da zai ganta ya shiga wani irin hali, tabbas Yana cikin farin ciki, burinshi a yanzu shine ya nemi afuwarta dana iyayenta sannan ya nemi aurenta, Bazai taba samun salama ba a yanda yake ji cikin ranshi ba har sai ya aureta, wani irin son Afrah dinne yake fusganshi bai taba jin son wata mace ba kaman yanda yake jin son Afrah a cikin ranshi ba, koh matarshi daya Aura baya tunanin ya mata irin wannan son, wacce a lokacin aurenta akai rigima sosai kafin ya aureta domin a lokacin tana da wanda take so, shi kuma daya ganta Sai yaje wajan mahaifinta hakan da yayi yasa mahaifinta ya gane dan gidan mutunci ne harya bashi izinin ya turo manya

GIDAN KASHE AHUΌπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα