15

2.6K 107 9
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*KHADIJA SULAIMAN JAGINDI*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 15*

Dad din David kam kaman an kafa dutse domin ya kame kyam ya kasa Koda motsi balle ya iya furta Koda wata kalma

Yayin da Dr din suka cire Mai Abun numfashin a hanci domin Rai yayi halinsa tunda oxygen ya tsaya cak, alaman ya mutu kenan, inda akai Kan mahaifiyar David din domin a ceci rayuwarta itama, Nan akai kan gado da ita inda aka Fara dubata cikin gaggawa hankalin kowa yayi kanta domin a ceci ranta, an saka mata itama abun numfashi domin ya dai daita mata duba da yanda numfashin nata ke barazanar saukewa daga gangan jikinta, lokaci daya ta fara Nishi sama sama gaba d'aya kallo daya zaka mata kasan tana cikin wani Hali duk da Bata San inda kanta yake ba, mutuwar d'a akwai ciwo musamman ma wanda shine babban D'an da mutum ya haifa, ace yau gashi kwance Babu Rai a tare dashi, Ya Salam Allah kasa mu dace...... Faduwar mahaifin David dinne shima ya Kuma rud'a wajan gaba daya inda shima akayi kanshi likitocin suka rabu biyu wasu nakan mum din wasu nakan Dad din, haka akayi caaa akansu domin ceto su...... Mahaifiyar David lokaci daya ta Fara barazanar tashi yayinda take Kiran sunan David tana ihu da kuka tana fadin d'anta Bai mutu ba, David will not die young..... I know my son will not leave me now, I have pray for his long life, why Jesus why my son........ Kuka yaci karfinta sosai Wanda yasa dole tayi shuru Amma gaba daya ta kasa daina kukan yayinda zuciyarta take ganin d'anta Bai mutu ba kawai dai wasa ake Mata

Shi kam Dad din David din gaba daya komai nashi ya saki na jikinsa, andai mishi allura da saka mishi drip

Gaba daya duk Wanda suke wajan sun tausaya musu sosai, sai dai Babu yanda suka iya sai hakuri duba da yanda mutuwa ta zama dole akan kowa, Kuma Babu Mai tsallake ranarsa

Mahaifiyar David yanzu ta daina kuka sai zuciyarta dake faman bugawa da karfi, gaba daya Bata gane komai, inda take ganin Taya d'anta namiji guda d'aya zai mutu haka? Taya d'anta zai mutu Yana matashi? Taya zai mutu so young? Mai yasa haka ya faru dasu, wani zunubi suka aikata haka da har hakan zai kasance da d'ansu na cikin su??

Shi kam David din kokarin daukansa akayi domin a kaishi inda ake ajiye gawawwaki idan sun mutu kafin a tafi dasu, tunda shidai ga iyayenshi duka a kwance dole sai sun tashi zasu tafi da gawar tashi...........



Yau tunda Afrah ta tashi take jinta wani iri, gaba daya duniyar juyi take Mata, Bata Jin dadin komai, har Mama ta lura da yanayin Afrah din inda take tambayanta Mai ya faru taga ta canza haka?

Afrah ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin Babu komai Mamana, tare da tashi tabar wajan inda ta koma dakinsu da suke kwana ita da kanwarta Zainab

Da Ido mama ta bita harta bar wajan ta girgiza Kai tare da fadin Allah ya kyauta

Koda Afrah ta Isa dakin kwanciya tayi Akan gadon dakin inda ta lumshe Ido, ba tunanin komai take ba saina David da tun jiya da daddare take tayi tare da burin ganinshi, wani hawaye Mai zafi ne ya zubo mata, tabbas David ya na Sonta, inama zai musulunta da tafi kowa farin ciki, sai dai inta tuna ko a magananshi in yanayi baya kawo mata maganan zai musulunta sai dai yace kowa yayi addininshi, share hawayen dake zuba daga idanunta tayi inda ta tashi ta bude kayanta dake akwati ta dauko wata Riga da David din ya siya Mata a cikin kayan daya Bata Wanda yace in zasu club tare, kallon rigan tayi gaba daya inta saka komai na jikinta ana gani, lokaci d'aya tayi dariya tare da fadin kai David sai a hankali Taya zan saka wannan kayan haka? Kaita girgiza tare da tuna magananshi da yayi mata inda take cewa nasan jiki na kake so, gashi kayi duk abunda kake so, inda yace mata haka kike tunani? Toh Bari kiji daga yau nayi alkawarin bazan Kara Bari wani Abu ya Shiga tsakanina dake ba har sai na Aureki...... Wani hawaye ya Kuma zubo Mata Mai zafi tare da fadin Oh David burinka bazai taba cika ba, dangin mahaifinna basa son duk wani farin cikin mu, basa barin muna zaban abunda muke so a rayuwa sai nasu zabin na rasa laifin da iyayena suka aikata suka tsanesu tare damu, musamman ma ni....... Dan shuru tayi domin jin muryan Hjy Fatima a gidansu yayar mahaifinta kenan, gabanta taji ya fadi tare da fadin maiya kawo ta Nan gidan yau, zata iya cewa Rabon Hjy Fatima da gidansu tun wani zuwa da tayi ta zage mahaifinta inda take cewa ya zama Wawa Mara wayau sai abunda mace tace mishi, ya auri makiran Mata, yayi wajan shekara biyar da akayi abun, tun daga wannan Rana Bata zuwa gidan sai dai su suje inda take, inma sunje toh hantara za susha da zagi Hadi da gori, sai yasa na tsani zuwa inda suke Dan Naga kaman sunfi nuna min tsana........ Shigowan Zainab yasa Afrah ta dawo daga duniyar tunanin da takeyi inda take cewa Sister kinji aunty a gidan mu yau

Afrah ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin eh maiya kawo ta??

Zainab tace Ina na sani....

Muryan Hjy fatima sukaji tana fadin ke yanzu hafsat Dan turaren wutan da Zaki saka a cikin dakin Nan naki shine ya gagara Kika bar daki na warin datti? Tsaki taja tare da fadin matsalata dake kazanta wlh, na rasa Mai wannan Mara zuciyar ya gani ya like Miki wlh.....

Mama dai Bata ce Mata komai ba domin ta Saba da irin cin fuskan da hjy Fatima keyi Maya

Su Afrah dake daki Suna Jin komai in ran Afrah yayi dubu toh ya baci, ta tabbata cin fuska ne kawai irin na Hjy Fatima, inba cin fuska ba Taya zata ce falon na wari, bayan ko Mai mura ya shigo ciki zaiji kamshi, duk da Basu da karfi Mama Bata wasa da turare tana kokari wajan ganin ta tsaftace gida dama jikinta, komai na mama Kal Kal gwanin ban Sha'awa, tsaki taja Mai sauti

Zainab ta kalleta tare da fadin lafiya?

Banza da Zainab tayi ba tare da tace Mata komai ba, inda ta tashi ta fita daga dakin Kai tsaye falon ta nufa, Hjy Fatima ganin Afrah ta fito yasa ta bita da kallo tana fadin ba shakka haka Kika zama? Zo Nan ya Naga komai naki ya cicciko Anya bakya bin maza kuwa? Zo Nan nace

Afrah gaba daya ranta a jagule yake Amma Jin kalman Hjy Fatima yasa gaba daya jikinta yayi mugun sanyi, da take cewa Anya bakya bin maza kuwa?

Kallon Mama tayi dake zaune tayi zugum tace kin gani Koh? Ai dama Hali zanan dutse Kuma dama barewa bazatai gudu ba d'anta ya rarrafa ba, gashi tun kafin aje ko Ina an Fara yada Hali, kalli nonuwan budurwa duk a ciccike kaman na babban mace......... Shigowan mahaifinsu ne yasa tai shuru tare da kallonshi tana fadin shanyar ta bushe kazo ka kwashe ne??

Abba shuru yayi inda yayi kasa dakai, Afrah na mamakin yanda iyayenta basa iya gayama wannan matar magana, Amma a juri zuwa Rafi wata rana saina wanketa tas, saina mata abunda harta mutu bazata manta dashi ba, saina nuna mata cewa kyaleta akeyi......

Abba ne ya katse ma Afrah tunani da yake fadin kiyi hakuri wlh Ina can rijiyan Zaki sanda Kika kirani kinzo, shine na juyo ga Hanya Babu kyau

Kallonshi tayi ta watsar tare da fadin kalli yanda duk ka fige, ka rame ka zaba ma kanka wannan rayuwa, Ina Mai baka shawara ka rabu da wannan matar domin ka inganta rayuwarka.......

Mama kuka ta Fara domin Dama tasan indai Hjy Fatima tazo gidan toh komai saiya sauya saita ruguza musu gidan ta kawo abunda zai haddasa fitina, da bacin Rai

Abba yace Yaya kiyi hakuri Ina son matata bazan iya rabuwa da itaba, ku.....

Ta daga mishi hannu tare da fadin saboda ta baka kasha ba? Ai dole kace haka, toh wlh Bari kaji Yusuf a haka zaka dauwama cikin kunci da talauci.......

Muryan Afrah sukaji tana fadin tunda kece Mai bayarwa ba? Ko Kuma kin San gaibu ai dole kice haka wlh cin kashin ya Isa haka bazai yihuwa ba kizo har gida ki dinga fadawa iyaye na maga....... Tas Tas taji saukan Mari har guda biyu a fuskanta ba kowa bane ya sauke mata Mari ba sai Abba da idonshi ya kad'e saboda bacin ran abunda Afrah tayi inda cikin fushi ya fara magana kin San wa kike fadama magana kuwa??

Indai Zaki fadama Yaya magana toh Nima Zaki iya fadamun Ashe haka kike Baki da mutunci???

Hjy Fatima tace gwara daka gane Bata dashi Tasha nonon banza, toh Bari kaji Yusuf yau dinnan zan yanke abunda ya zama dole ayi shi ko Anki ko anso zan gwada Mata iko na.....

Afrah cikin kuka ta Fara magana da fadin Abba zan iya juran komai Amma Banda Inga ana ci muku fuska wai shin wani zunubi kuka aikata haka da zuri'arka suka tsanemu haka? Musamman Mani......

Hjy fatima ce ta katseta da fadin Sabo dakece silan fadawarsu wannan halin saboda kece yasa akayi wannan kaddararren auren duk kece sila, kece silan komai Amma Bari in fada Miki komai kisan matsayinki kisan koke wacece kisan abunda uwarki da ubanki suka aikata tun kafin kizo duniya yau zan bud'e Miki wannan sirrin...............








Maryam Obam

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now