6

4.1K 128 3
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*AYSHA A BAGUDU*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 6*

*Waye AS?*

Alhaji Muhammad Kura babban dan kasuwa ne, wanda yayi fice a kasheshen Africa, bama Africa ba harta duniya gaba daya, domin business dinshi ba'a gida Nigeria ya tsaya ba, harda international business, Alh muhammad yana da mata Hjy Binta wanda sukai Auren soyayya tun zamaninsu, Hjy binta yar boko ce takin karawa, macece wacce ta waye da boko tana da ilimi sosai, ga kirki da faran faran da mutane, sai dai bata daukan raini ko kadan

Shekaransu daya da aure suka haifi Abubakar Sadiq, wanda suka dauki son duniya suka daura mai, duk wani jin dadi na rayuwa suna kokarin bama Sadiq, sai dai Sadiq ya taso da shegen miskilanci uwa uba son girma, domin tun yana yaro ake rusuna mishi duk saboda fada, wanda wannan abun ne yabi jininshi, gashi da shegen son girma, Abubakar Sadeeq tun Yana yaro yake da rigima, bashi da hakuri ko kadan, komai akayi mishi sai yayi taking revenge yake samun nutsuwa mutum ne Mara yafiya, sai dai duk da wannan abun nashi Yana da ilimi sosai, uwa uba Yana da sa'a a rayuwa domin muddin yasa Abu a gaba Allah Yana bashi sa'a yayi nasara, wannan abun nashi tun Yana yaro, kasancewar iyayenshi Yan Boko ne yasa Dan nasu Shima sukai tsayin daka wajan bashi ilimi, yayi primary har zuwa matakin secondary a gida Nigeria daya kammala karatun secondary din shine ya fita kasar waje inda ya hada degree dinshi a can, inda a Nan ne gaba daya rayuwarshi ta canza daga bin Mata, Shan giya duk sanadin haduwa dasu Kamal Wanda suke karatu tare course daya, ECONOMIC, sai dai shi AS ba sosai yake neman matan ba, domin Yana da kyama sosai, classic baby's yake nema, Mata masu aji, sannan irin Shan giyan da yakeyi baya kwalewa sannan ba karaman giya yake shaba Mai saka maye, giya Mai tsada yake Sha, kafin tasa mutum maye sai yayi Mata mugun Sha, kasancewar sunanshi Yana ma turawa wahalan fada shine suke cemai AS, haka har sunan ya bishi

AS bayan ya kammala karatu ya dawo gida Nigeria inda iyayenshi suke zaune a garin Abuja, tunda ya dawo Dad dinshi yake ta fadin yaci gaba da kulan Mai da kasuwanci domin Yana bukatar hutu, Amma AS yaki domin a cewarshi yayi karami da kula da ragaman kasuwancin mahaifin nashi tare da fadama mahaifin nashi shi America zai koma yayi aiki a can baya bukatar zama a nan, a lokacin dad din nashi Bai damu ba domin son da suke ma tilon Dan nasu yasa komai ya kawo saisu amsa hannu bibbiyu, Amma ya nuna ma AS maganan aikinshi a America ya Bari Nan gaba, domin akwai wani company dinshi da yake kokarin rushewa a garin kaduna Yana bukatar wajen ya farfado a Kara zuba ingantattun kaya na zamani, AS ya nuna shi bazai iyaba Dan baya ra'ayi ko kadan, haka dad din nashi ya barshi

AS Yana zaune a gida Koda yaushe, indai ya fita toh club zasu shida su kamal, wata Ranan birthday dinshi sunje club aka kawo musu giya sukai tatil, musamman AS da ranan yayi mugun shahuwa Bai masan inda kanshi yake ba, duk da sunan Suna murna, da ranan zagayowan haihuwarsa, Koda suka tashi kamal ya tuka motar Wanda shi baiyi irin kwalewan da AS yayi ba, inda Kai tsaye ya Kaishi gida, ba tare da wani tunani da duba da irin yanayin da AS din ke ciki ba, duk da ko anje sau da yawa iyayenshi basa Nan, Kuma gefenshi daban, haka Kamal ya Kaishi har part inda AS yaita layi cikin maye damma giyar Mai tsada yake Sha Bata cika saka maye ba, Amma irin mugun Shan da yayi shine ya sakashi maye, bayan Kamal ya kwantar dashi Aiko ya Fara kwarara amai kaman zai fitar da hanjin cikinsa, Ai Kamal ganin haka Direct part din iyayenshi ya nufa inda yaita nocking Dad dinshi ne ya bude kofar inda yaga Kamal cikin tashin hankali yace Kamal lafiya?

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now