3

7.6K 139 8
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

Ku danna wannan shudin rubutun domin samun ci gaba, tare da samun maganin karin ni'ima

*GIDAN KASHE AHU*



*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*




*DEDICATED TO.....*
*AYSHA A BAGUDU*


*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*


*PAGE 3*






Kai tsaye cikin bedroom dinshi ya nufa wanda yayi bala'in haduwa da kuma tsaruwa, lallai duk wanda yaga wannan dakin yasan an kashe naira cikinsa, kayan jikinsa ya fara tubewa, tare da cire chain din dake makale a wuyarshi, inda ya ajiye kai tsaye ya shiga toilet

Yayi wajen 20mnt sai gashi ya fito daure da towel a kasan kugunshi, kirjinshi a bude, daka duka alama wanka yayi

Zama yayi akan gadon dakin, hango wayarshi na wuta yasa ya nufi wayar tare da dauka, number ya gani ana kiranshi dashi kaman bazai dauka ba, komai ya tuna kuma naga yayi tsaki tare da dannawa yasa wayar a kunnenshi tare da fadin yes.....

Daga can gefen naji ana cewa barka da wannan lokac......

Bata kai ga karasa maganan ba, AS yace waye plz???

A hankali tace sunana Deeja, mun hadu dakai a k and k boutique harna amshi number dinka h.....

Dan gajeran tsaki yaja mara sauti, tare da fadin baki da time din da zaki kirani sai at this time in the night???

Tana kokarin yin magana ya kashe wayar tare dayin jifa dashi yana fadin she is mad

Kwanciya yayi akan gadon ta bayanshi kanshi na kallon saman dakin, gaba daya ya rasa mai yake mishi dadi, bashi da wani buri face yau ya ganshi ya gama wannan aikin da yasa gaba, ya tabbata saiya gama Dad dinshi zai barshi ya sarara, tsaki ya saki tare da fadin i don't know why Dad yake son ganin na tsaya akan wannan aikin

Su kamal dake falo suma suka tashi tare da fadin tunda ya haura sama kuzo musan inda dare yayi mana, domin guy dinnan ba fitowa zaiyi ba

Tashi sukayi suka fita, inda ko wanne ya dauki motarshi yayi gaba, dama saboda zasu Club ne yasa suka bar motarsu a gidan AS, suka shiga mota daya

AS yana jin karan bude gate yasan abokanan nashi ne suka fita, ido ya lumshe cikin wani irin yanayi mai wuyan misaltuwa, lokaci daya ya fara tunanin kalubalan  dake gabanshi, tabbas saiya tashi tsaye kafin ya iya magance wannan matsalan, tsaki ya saki tare da tashi ya cire towel din dake manne a jikinsa, ya saka wata jallabiya fara sol tare da kwashe kayan daya cire yakai cikin basket din da yake saka kayan wanki, sannan yazo ya kwanta abunshi

Deeja kam bayan AS ya kashe mata waya, sakan baki tayi tana mamaki tare da kallon wayar cikin cikin mamaki, lokaci d'aya kuma ta hura wani irin iska daga bakinta mai zafi, tare da fadin wlh tunda na ganka Na kyasa Dole inyi harka dakai koda kuwa baka so......

Kawarta dake kwance kusa da ita a cikin dakin hotel din da suka sauka, tace Beb lafiya kuwa??

Ajiyan zuciya deeja ta saki tare da kallon Sadiya tace Sady kalleni dan Allah dakyau

Sady tace miye wai???

Deeja tace Sady guy din da nake baki labari mun hadu a boutique shina kira yake kashe min waya

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now