Final

524 20 8
                                    

As Jin zantukan bakin Afrah yake kaman a mafarki domin baiyi zatonsu daga gareta ba a dai dai wannan lokaci ba, tabbas mahakurci mawadaci, a hankali ya furta kalman Alhmdlh tsarki ya tabbata ga Allah, lallai yau nafi kowa sa'a Afrah ban taba tunanin Jin kalman so a bakin kiba, kullum da wannan tunanin nake kwana nake tashi ashe zaki furta min rungume ta yayi sosai a jikinsa Yana sauke wani irin ajiyan zuciya tare da fadin zan zame miki gata zan nuna miki cewa lallai kin zaba masoyi mai kaunarki........ Tun daga wannan rana Afrah da As suka Killa sabuwar rayuwa, yayin da suka kara shakuwa da junansu sosai, tabbas duk wanda ya gansu yasan suna cikin kwanciyar hankali da Kuma kaunar junansu abun su gwanin sha'awa hutun Afrah ya kare sun koma America, inda As yake Shirin sama ma Zainab gurbin karatu itama a can domin ta dawo gurinsu da zama

Ta gefen Zainab kuwa ta rame tabbas sai yanzu take ganin laifin kanta na saurin fadawa soyayyar Mohd, ta tabbata Afrah yake so ba ita ba, kuma duk abunda yakeyi tasan yana biye mata ne soboda Afrah din, a yanzu ta burinta ya cika na ganin ta hada kan yar uwarta da mijinta sai gashi ita kuma tana kokarin rasa farin cikinta, Mai aikin gidansu ce ta bude dakin inda ta gaida Zainab tare da fadin mama tace in fada miki kina da bako a waje

Dan Bata fuska tayi sannan tace sau nawa nace miki in zaki shigo mun daki ki fara Neman izinina kafin ki shigo mun?? Cikin rawar murya mai aikin tace kiyi hakuri insha Allah Hakan bazai kara faruwa ba, Zainab Bata kulata ba sai tashi da tayi domin taga waye bakon da yazo wajanta har kuma mama ta amince akan taje, hijab kawai ta daura akan doguwar rigan dake jikinta ya fita kai tsaye Dan karamin bukkan dake gidan ta nufa tana Isa ta ganshi wani irin murmushi ne ya bayyana akan fuskanta Shima sakar mata murmushin yayi tare da tashi tsaye kuma karasawa tayi har inda yake inda take mishi sannu da zuwa tare da fadin Bismillah ka zauna mana duka cikin harshen turanci take maganan

Zama yayi bayan itama ta zauna yace Zainab maiya sameki haka? Naga kin rame sosai

Dan murmushi tayi wanda ake cema yafi kuka ciwo, sannan tace babu komai

Kura mata ido yayi lokaci daya Kuma ya sauke ajiyan zuciya sannan yace nasan akwai wani abu dake damunki, inaga zuwa yanzu mun kai matakin da ni dake babu boye boye

Magana ta fara da fadin ba komai bane yake damu naba sai tunaninka, tunda ka tafi kullum Ina cikin zullumi ko zaka dawo ko ba zaka dawo ba, zuciyata ta kamu da sonka da kuma kaunarka, tabbas nayi rashin hankali da har na bari nayi mugun kamuwa da sonka, nasan ba zaka taba sona ba domin ka bama yar uwata zuciyarka Kuma...... Dakatar da ita yayi da hannunsa tare da fadin karki kara fadin haka, Zainab karki manta Afrah matar aure ce taya zanci gaba da sonta bayan Hakan haramun ne

Inaso ki sani da farko naso Afrah son da ban taba tunanin zanyi ma wani irinsa ba, sai dai kuma Allah yayi ba matata bace ita, matar wani ce, tun zuciyata tana ganin kaman zan sameta wani rana harna cire rai da Hakan na mika duka lamura na ga uban gijina Kuma Alhmdlh wlh yanzu babu kowa a zuciyata sai ke, ke kadai kawai nake kallo baki da maraba da Afrah sai dai kawai ta nuna miki haske, Zainab na dade da kamuwa da sonki abunda yasa kike tunanin kaman bana sonki nasan kina da kikayi shuru kuma waya ban cika kira ba abubuwa ne suka faru....... Nan ya bata labarin komai harda musuluntar mahaifiyarsa

Zainab tace Allahu akbar, wlh nayi matukar farin ciki dajin wannan labari, Allah ya kara haskaka addinin musulunci da musulmai a duk inda suke, Mohd ya amsa da Allahumma Ameen

Shuru ne ya biyo baya inda yayi ajiyan zuciya sannan yace mata yana son ya koma America, Kuma yana tunanin yanda zai barta a nan, tace karya damu itama zata dawo nan da zama domin a yanzu ana shirye shiryen komawanta ne, yaji dadin wannan labarin inda ta tashi tace bari ta kawo mishi abun motsa baki, yace mata a'a baya bukatar komai domin kafin tazo mama ta bashi yaci abinci bayan na gama ne na dawo nan yanda zan samu Daman yin magana dake sosai, sannan na fadama mama komai harda musuluntar mahaifiyata Kuma tace zata fadama Abba inya dawo munyi magana da ita sosai, yanzu abunda ya rage shine muji wani hukunci Abba zai yanke a kanmu

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 05, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now