30

610 29 7
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 30*





Mama iya tashin hankali tana cikinsa sosai tabbas duniya tayi mata duhu hadi da daci, bata jin dadin komai a halin yanzu, sai dai duk da irin halin da take ciki akwai sunan Allah a bakinta tare da kira yaba ma yarta lafiya, ya kuma yaye mata damuwarta ya bata dangana akan abunda ya sameta haka taita sintiri tana jiran fitowan likita domin ya fada mata abun dake damun yar tata.......

AS kam tunda suka koma gida yayi part dinshi kai tsaye toilet ya fada yayi wanka sannan yazo yabi lafiyar gado, sai de me?? Bacci yaki daukar sa babu abunda yake sai tunanin Afrah tare da abubuwan da suka faru, wani irin gajeran tsaki ya saki tare da furzar da wata irin iska mai zafin gaske hadi da fadin taya zata fada soyayya da wanda ba musulmi ba?? Wani irin so take mishi haka?? Anya bata da tabun kwakwalwa kuwa? Inko bata da tabun kwakwalwa toh tabbas tana da aljanu masu sata aikata haka, wani uban tsaki ya kuma ja hadi tashi ya zauna akan gadon fuskan Afrah yake gani a cikin idanunsa tana mishi yawo, ta gefe daya kuma jin zuciyarshi yake tana mishi radadi hadi da zafi, shi dai yasan baya son Afrah kuma bai taba tunanin zai sota toh amma taya zai zauna da ita a haka tana cike da soyayyar wanda ba musulmi ba? Anya hakan zaiyuhu kuwa? Anya bazan rabu da ita in huta ba kowa ma ya huta? Lokaci daya ya girgiza kai hadi da fadin no kawai ka zauna da ita ta haka zakai hurting dinta tunda ka shiga tsakiya ka rabata da wanda takeso, inko ka rabu da ita ka bata daman samun masoyinta ne..... Kalmar Yes ya furta tare da sakin wani kayataccen murmushi hadi da kwanciya yana juyi cikin nishad'i akan makeken gadon Nasa.

Ita kam Zainab gidan hjy Fatima suka nufa bayan sun ajiye Abba, kwance take amma ta kasa bacci, itama dai ba komai take tunani ba sai yanda yar uwarta ta fara soyayya mai zafi haka har take neman zautar da ita, kuma Abun takaici tace yaron ya musulunta amma ya musanta hakan ya kuma nuna bai santa ba, duk da likita yace ya mance wasu abubuwa na rayuwarshi, ido Zainab ta lumshe hadi da fadin Allah ya baki Lfya Afrah ya yaye miki damuwarki lallai ni nasan irin radadin da zafin da kike ji cikin ranki, ban taba soyayya ba amma ina karanta littafai musamman na soyyaya nasan irin yanda akeji, duk da ni ban taba jiba, amma nasan irin illar da soyyaya take haifarwa musammam idan mutum bai samu abunda yake soba, naga soyayyar wannan bawan Allah cikin kwayar idon Afrah...... Wani hawaye ne ya zubo ma Zainab hadi da tausayin yar uwar tata, shin ya zataci in ta tabbatar an daura mata aure da wani ba wanda take so ba? Wani irin hali zata shiga In taji haka? Kuka Zainab ta fara sosai ganin kaman kukan bashi bane mafita a tare da ita yasa ta tashi taje tayi alwala inda ta fara Sallah hadi da nema ma yar uwarta lafiya tare da rokan Allah ya bata dangana.......

Ta gefen Abba kuwa shima haka yai kwanan tunani hadi da takaicin irin abubuwan da suka faru, yasan sun bama yarsu tarbiya ta gari sun kuma yi duk wani abu wajen ganin sun kare musu hakkin su, toh mai yasa Afrah zata fara soyayya da wanda ba musulmi ba? Shin taya ma suka fara mu'amala da har soyyaya ta shiga tsakaninsu mai karfi haka? Bai taba tunanin Afrah zata iya soyayya da tubabbe ba balle har soyayyar tasu tayi zurfi haka, dan ajiyan zuciya yayi tare da fadin bai zama ma tubabbe ba tunda gashi yace bai musulunta ba, wannan wani irin rayuwa ne? Yau karo na farko yaji yana dana sanin tura yarsa mace karatu wani gari, tabbas yau yaji ya aikata babban kuskure mace tana da rauni sosai, abu kadan zai iya canza mata tunani tabbas ya dauki abunda Afrah ta aikata a matsayin sakacinsu..... Uhm nikam nace in mahaifin Afrah yasan yarshi ba budurwa bace ya zai dauki abun ya kuma zaiji......


GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now