32

796 28 5
                                    

Afrah jin sun fita yasa ta sauke wani irin Ajiyan zuciya, hadi da fara zubar da hawayen dake makale a cikin idonta, ba komai take tunani ba sai David dinta wato Muhd, mai yasa David ya juya mata baya? Mai yasa ya nuna bai santa ba kuka mai karfin gaske ya kubce mata dama zai iyayi mata haka? Kai ta fara girgizawa alaman ina bazai taba mata haka ba domin tasan yana matukar sonta so kuma na hakika, ya sadaukar da abubuwa da dama a kanta tuna sanda ta taba zamewa a toilet tayi yanda duk ya rude a kanta yabi ya gigice yanda yakeji a lokacin kaman ya cire ciwon dake jikinta ya dawo jikinsa da dan karfi kadan ta furta no bazai taba bari na ba, tabbas nasan akwai wani abu ba haka iyayensa suka barshi ba ta tabbata iyayensa sun masa sihiri ne domin ya rabu da ita........ jin an tabata yasa tayi firgit Zainab ce ta gani a tsaye itama idonta tana zubar da hawayen magana ta fara mata cikin danuwa tare da fadin Haba Afrah yaushe zaki daina wannan kukan?

Yaushe zaki cire wannan damuwar? Haba Afrah kefa musulma ce karki manta ana son musulmi yayi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau

Afrah tace Zainab ba zaki fahimci abunda nake jiba, ba zaki gane irin radadin da zuciyata take mun ba nasan baki san mainene so ba sai yasa kike fadamun haka, amma daga ranar da kika fahimci mainene so zaki gane abunda nake fada miki, shin kin san yaya nakeji a cikin zuciya ta kuwa? Ji nake kaman ana watsa mun garwashin wuta, kuka ta kuma kubcewa dashi tare da rike kirjinta tana fadin Zainab kirjina zai fashe Zan mutu zainab.....,,

Cikin tashin hankali Zainab ta fara mata Addu'a tana tofa mata a kirjin bata dade ba bacci yayi awon gaba da ita, ganin haka yasa zainab ta kwantar da ita da kyau tare da rufe mata jiki da blanket

Zama tayi tana kallon Afrah cikin tausayi fuskanta duk ta wani rame tayi fayau, ga bakinta ya bushe alaman babu ruwa a jikinsa saboda tsabagen damuwa da take ciki, shafa lips din Afrah tayi tare da fadin insha Allah sister komai zai wuce za kuma kiyi alfahari nan gaba indai kika daure kika ci wannan jarabawar da Allah yayi miki, ba komai bawa yake soba yake samu a rayuwa..... kana naka Allah na nashi zabin Allah shine dai dai dan haka ake so koda yaushe bawa ya nemi zabin Allah

AS ne ya fito daga toilet kugunsa daure da towel hannunsa rike da wani towel din yana goge ruwan dake kansa alaman dai wanka yayi , tsayawa yayi lokaci daya tare da jefar da towel din hannunsa yana fadin why why mai yasa na aureta ido ya lumshe tare da sakin wani murmushi yace yes

Kai tsaye wajan kayansa ya nufa yasa wata jallabiya tare da kwanciya domin a matukar gajiyr yake yana matukar bukatar Bacci sosai, koda ya kwanta baccin ya gagare shi domin tunanin da yasa a gaba wanda yayi iya kokarinsa ya cire amma abun yaki ba tunanin komai yake ba saina yanda zai zauna da wannan yarinyar shida gaba daya rayuwarsa baya son hayaniya, gajeran tsaki yaja domin ya tabbata yarinyar kalan yaran nanne marasa kunya wani irin ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin in tace zatai mun wani madness I will teach her a lesson that she will never forget in her life tsaki ya kuma ja tare da fadin let me sleep in cire tunanin wannan mad girl din,...... karan wayanshi ne yasa ya tashi domin yaga wake kiranshi a dai dai wannan lokacin number ne babu suna ya dan kura ma number din ido kaman karya dauka lokaci daya kuma ya danna tare da saka wayar a speaker koda ya dauka baiyi magana ba, jin an dauka yasa ta fara magana kamar haka haba AS taya zaka mun haka? Mai yasa kake son guduna bayan ka lasa mun zumarka sannan kake kokarin barina

Wani irin ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin hold on wake magana

Tace Dija ce

Dan shuru yayi yana tunaninta kafin daga baya yace okey, ke baki da time din kiran mutum saida daddare time din da mutane ke bukatar bacci, tana ko Karin yin magana ya dakatar da ita da fadin last warning karki kara kirana so late at night komai kike bukata indai dare yayi ki bari da safe, yana gama fadin hakan ya kashe wayarshi alaman baya bukatar jin wani abu daga Gareta

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now