18

2.4K 113 8
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*K
MARYAM DAUDA ABDUL''AZIZ*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 18*





Su Afrah washe gari suka koma gidansu, inda Afrah farin ciki ya cikata domin tabar gidan hjy Fatima Dan gaba D'aya zamanta a gidan ji take kaman a gidan yari take wato prison, inda badan Mama ba da tuni tabar gidan

Afrah taba ma zainab kyaututtuka irinsu Turare masu kamshi, da waya mai kyau, Android, inda iyayenta sukai mata caaaa akai, akan a Ina ta samu kudi haka har tayi wannan hidiman

Afrah tace ta Dade tana Tara kudin saboda wannan ranan, inda tace da zata tawo Kuma kawayenta sun Bata kudi, shine ta siya tun a can, ta Bari ta Bata yau a Matsayin gudun mawa

Mama dai kallon Afrah kawai take toh sai dai Kuma ance y'a da uwa, lokaci Daya Mama ta kawar da tunanin dake ranta ,tare da furta Allah yayi ma Afrah albarka sannan ta Kara da cewar ta dinga tattali duk da tasan tana hakuri Dan basa wani wada tata, tare da fadin Afrah kaman dai kullum bazan gaji da furta Miki wannan kalman ba, na kiyi hakuri akan duk inda Kika tsinci kanki, a kullum burin dangin ubanku shine suga wani abu ya sameku su goranta Mana, Dan Allah Afrah karku Basu Daman fad'a Mana magana duk da muma kaddara ne ya fad'a mana,

Afrah wani hawaye ne ya zubo mata Mai zaifi, Wanda Bata San ya fito ba, gaba D'aya ta kasa magana, lallai ta cuci kanta ta Bata rayuwarta, innalillahi wa Inna ilaihira jiun, maina aikata haka? Shin Allah zai yafemun kuwa? Naci amanar iyayena saboda wani banzan manufa dake kaina, Kai na shiga uku.......

Mama ce ta katse mata tunani da take fadin, Afrah rayuwar mace kalilin ne, karku Bari rudin duniya ya dibeku, mutuncinku shine darajanku, wlh Afrah Ina Mai tabbatar Miki duk Wanda Kika Aura indai yaji kin zubar da kimarki toh babu ke babu daraja a tare dake, sai yasa kullum nake tunatar daku akan rike kima da daraja

Afrah rungume Mama tayi tana kuka tare da fadin hakane Mama, hakane, tabbas darajan mace shine ta rike kimarta, lallai rayuwar mace karama ce Kuma........ Kuka yaci karfinta inda take ta sheshekar kuka, Mama na shafa mata baya, inda zainab itama idonta ya ciko da kwalla.......



AS ne kwance akan makeken gadon dakinshi da yaji kayan more rayuwa, lallai duk Wanda yaga wannan d'akin yasan an kashe naira wajan kayata d'akin, kallo Daya zaka mai ka Gane tunani yake, Wanda daga gani yayi nisa cikin tunanin, kwance yake Amma idonshi na sama Yana kallon POP din d'akin, tunanin Afrah yake inda take cemai Driver, a hankali ya furta how dare her....... Lokaci Daya Kuma ya juya tare da fadin ita Bata gani na like sauran mata ne, da suke rushing akai na?? Ban taba ganin macen data ganni Bata nuna tana Sona ba, just saboda am handsome rich....... But this stupid girl call me a Driver....... Hannunshi yasa a Kai tare da furta kalman oh my God, I promise to humiliated this girl, inko ba haka ba am not Abubakar Sadiq, I will marry you just to teach you a lesson that I will never ever Forget in your life........ Ido ya lumshe lokaci D'aya Kuma ya Fara girgiza Kai, why why Mai yasa zan aureta??? Wata zuciyarshi tace just to take revenge Mana.

Kai ya girgiza tare da fadin no there is so many way of taking revenge basai na aureta ba, Dan shuru yayi Yana nazari akan wannan maganan, lokaci Daya Kuma ya tashi tare da Fara zagaye a d'akin Yana buga hannunshi Daya akan tafin hannunshi, aurenta shine babban abunda zanyi in koya mata hankali sai in saketa daga baya, yes haka zanyi, I will tell mum ayi bikin da wuri......



GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now