34

293 15 0
                                    

Afrah dakin da aka ware na Zainab tayi wanda duka komai nata ke ciki, kai tsaye tayi toilet tare da kunna shower domin duk wanda ya shigo yasan wanka takeyi amma ba wankan takeyi ba kuka ta fashe dashi mai cin rai tana fadin shikenan Muhd shikenan inaji a raina naci amanarka tabbas ban maka adalci ba kuka takeyi sosai tare da tuna irin abubuwan da suka faru a tsakaninsu irin kulawan da yake nuna mata da irin son da yake bayyana mata yake mata, irin rayuwar da yake nuna mata zaiyi mata inya mallaketa....... Zaman dirshan tayi a kasa tana ci gaba da kuka tare da tuna sanda yake ce mata karta dauka jikinta yake so ita yake so in kuma tana tunanin haka ne daga yau nayi miki alkawarin bazan kara tabaki ba har sai na aureki....., kuka mai cin rai ta kuma fashewa dashi hadi da fadin mai yasa kaddarata tazo mun a haka? Mai yasa na hadu da irin wannan mummunan kaddarar tuna sanda ta karye a hannu tayi a gidansa inda ake mata gyara yasa bakinshi cikin nata yana kissing dinta wanda hakan yasa gaba daya ta manta da irin radadin da takeji..... wani hawaye mai dumi ta matse tare da kara tunawa sanda suka dawo daka asibitin mahaifiyarta ta kirata ta fara fushi dashi yanda ya rude a kanta yana tatambaya koshi yayi mata laifi kaita girgiza da sauri tare da fadin no nasan akwai abunda akayi maka domin na tabbata bazaka taba gudu naba sonda kake mun nasan bazaka taba gudu naba I knw that....... Kara tuna sanda yazo skul dinsu yayi na farko data fito yazo yayi hugging dinta a gaban mutane inda take ce mishi ana kallon mu fah yace so what tare da kara rungumeta wani hawayen ne ya kuma zuban mata mai radadin gaske, irin yanda ya dinga mata kallon kauna hadi da tsantsar so tare da tuna washe garin ranar da zasu zo kano kafin su hadu da wannan mummunan hatsarin da yayi sanadiyar rushewar farin cikinta tuna sanda ta fito daga dakin mas'ud tayi da kudi a hannunta yanda idonshi ya canza daya ganta tare da fadin dan Allah Afrah karkiyi abunda zaisa in fara zarginki........

Aida sauri ta mike tare da fadin ni nasan kana sona kana kaunata kaman yanda nake kaunarkia...... toh amma mai yasa ka nuna baka sanni ba har kake kiran sunan wata budurwa a matsayin ita kake son aure a gaba na...,,, kirjinta ta rike da karfi tana fadin idan kai ka gujeni bazan taba gudunka ba am so angry with you muhd ban taba tunanin koda sihiri aka maka ba zaka manta da soyayyar mu ba ina sonka kai daya nake so sonka zai kasheshi ni taka ce har abada ji...... bakinta ta kama cikin furgici daga duka alama ta tuna yanzu ita matar wani ce bata muhd ba kalmar innalillahi wa Inna ilaihira jiun ta furta tare da kara zama dirshan a kasan toilet din, yayin da ruwa yake ta dukanta na shower shikenan burinta farin cikinta jin dadinta duk sun rushe kenan??

Na tabbata bazanyi rayuwa mai tsawo ba a duniya son muhd yayi mun mummunan kamu, ido ta lumshe yayin da wani bangare na zuciyarta yake ingiza mata cewar ta gudu shine hanyar da zata gujewa wannan auren

Wani murmushi ta saki tare da cije kasan lips dinta tana girgiza kai nayi ma mahaifiyata alkawari zanyi biyayya ga mijina da aure na am not that weak da zan gudu inbar gidan iyaye na saboda farin cikin zuciya ta zan zauna a gidan auren kafin lokaci na ya cika, share hawayen idonta tayi inda ta tashi dakyar tayi wanka jiki babu kwari ta fito ta saka wata doguwar riga ba tare data shafa koda mai bane ta kwanta a gado domin yanda take jin wani irin azababben ciwon kai da kuma radadin da idonta yake mata yasa taji tana bukatar tayi bacci koda zai daina mata ciwo........

Ta gefen AS kuwa zaune yake a falo mum dinshi ta shigo tana fadin wai ina kamal ne??

Kallon Mum din yayi tare da fadin ya shiga cikin gari yawo

Mum tace ok toh ina fatan dai kun gama shiri koh? Domin gobe zamu koma

As yace eh mun gama goben kawai muke jira insha Allah

Mum tace ok sannan ka shirya anjima dakai zamu gidan su Afrah mu dauko ta naso ma kuje kaida kamal ku dauko ta amma tunda bata tare ba tare zamu

Annurin fuskanshi ne ya dauke tare da fadin mum kaman ya bata tare ba?? Indai haka ne a barta a gidansu mana zaifi har lokacin da zata tare I think it be better

Mum tayi shuru kana daga bisani tace a'a mun riga mun gama magana bai kamata kuma mu canza ba dan haka ka shirya anjima wajan karfe biyar zamu

Yace ok badan yaso ba

Shuru yayi yana dan nazari da farko ya kosa a daura auren badan komai ba sai dan ya dauki fansa a kanta akan kiransa da tayi driver, domin shi baya yafiya komai akai masa saiya rama ta hanyar da zai hukunta wanda yayi masa laifin ninkin baninkin abunda yayi masa toh amma tunda aka daura auren sai yaji gaba daya abun ya fitar mishi daga rai, dan murmushi yayi, a kuma yayin da zuciyarsa ke fada masa cewa ai maganan fansa ka riga ka dauka tunda ka aureta ka rabata da wanda takeso aika gama daukan babban fansa a kanta ranshi kuma yaji ya dan baci lokaci daya yaja tsaki mara sauti amma duk da haka saida mum taji tare da fadin lafiya kuwa

Dan zabura yayi tare da fadin lafiya Mum kaina ke dan min ciwo

Cikin damuwa tace aiko ka kira dr tana nufin ya kira family's doctor dinsu a Waya

Ya amsa da okey Mum

A tun lokacin da iyayen David sukaji labarin dansu ya samu ciwon mantuwa na dan wasu lokuta a rayuwarsa wato yayi losing memory hakan yasa suka shiga cikin tashin hankali musamman ma mahaifiyar David din da take ganin babban illa ne ga dan nata

Mahaifin David hakan ko zan iya cewa yayi masa dadi domin koda aka kai David wani private hospital ya farfado still dai bai tuna komai ba sai ma tambayan Dad dinshi da yayi ina wannan mahaukaciyar yarinyar??

Dad dinshi tace saboda ita suka bar hospital din tare da cemai tana da tabun hankali ne karya damu da abunda take fadi, yace Dad but she call my name?? I think she know me??

Dad dinshi yace No David taji muna fada ne bakaji tana cewa muhd ba am sure sunan nata kenan da taji munce David shine take cewa kaine, haka dai mahaifin David yaita fadama dan nasa zancen kanzon kurege akan Afrah har saida ya tabbatar David ya gamsu tana da tabun hankali ne kafin ya rabu dashi inda ya canza maganan daya samu ya kwanta ya huta

David bai dade ba ya koma gida domin mahaifinshi baya bukatar wani abu da zai saka dan nasa ya tuna abunda ya manta a cewarsa tare da fadin yana son bujire ma Jehovah ne shine ya saukar mai da wannan cuta lallai ya kara gasgata addininsa na Christian tunda gashi yaga ishara a yanzu haka daga hannu yayi tare da fadin thanks you father lord for everything

Mahaifiyar David ce zaune ita daya a daki ta zabga tagumi saiga Dad dinshi ya shigo inda ya Kura mata ido tare da fadin maike damunki haka kikayi tagumi

Ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin dole inyi tagumi ba komai bane ya sani haka ba sai irin halin da David yake ciki I need my son to remember everything daya manta ina ganin kaman he is incomplete now

Dad din David yace what? Don't you ever think of that taya zaki dinga irin wannan tunanin? Kamata yayi ki godema our father daya saka ya manta wasu abubuwa ciki harda bangaren yarinyar nan, inda ba haka ba only God knw what will happen am a pastor sai aji yarona ya musulunta...... mahaifiyar David tace what

Dad din David yace yes bakiji tana fada ba, har suna ya canza inda badan hakan ya faru ba ya zan kalli duniya da wannan abun kunya

Mahaifiyar David tace tabbas jesus yana tare damu daya saka hakan ya faru toh yanzu miye abun yi.

Dad din ya numfasa tare da fadin na riga na yanke hukunci akan yanda zamu shawo kan matsalar

Mahaifiyar David tace mai kenan maika yanke

Yace zan tura David America ya karo karatu ta hakanne zai bar kasar ya kuma manta da yarinyar yanda ba zasu sake haduwa ba.

Mahaifiyar David tace aiko baka turashi ba bazai tunata ba tunda ya mance da ita

Dad din David yace no bazanyi wannan kasadar ba kin san irin karfin sihirin musulmai kuwa? Bazan bar hakan ya faru ba kuma yarinyar zata iya nemanshi taita bibiyarsa har sai taga ya tuna ta kinga in hakan ya faru da matsala

Mahaifiyar david tace hakane mu turashi can hankalin mu kwance maganan ka gaskiya ne in yana nan dole wata rana zasu hadu maganin kar ayi kar a fara

Wannan shawarar suka yanke na tura David America yin karatu koda aka tuntubeshi akai bayyi musu ba yayi na'am da batun inda aka fara cuku cukun ya samu admission domin yin masters dinshi cikin ikon Allah an samu kuma ya wuce ba tare da wani wuya ba duba da mahaifinshi babban mutum ne sai yasa basu sha wahala ba......

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now