45

297 52 3
                                    

Yau dai na samu Maa ta barni in fita, da'di kawai nake ta ji, Asabe ma izinin fita ta nema ta ce zata je ta ga wata qawar ta, shima me gadi an bashi izini yaje ya sada zumunci, Noorie kuma ta tafi makaranta, Maa ce ka'dai a cikin gidan sabida yau ba aiki, Ina fitowa na nufi gidan mu, Ina isa na samu tana ta shiryawa tana sauri sauri, ce mata nayi

"Umma se ina kuma?"

Cewa tayi

"Ke dai bari kawai, wallahi Ameerah ce bata da lafia, ciwon ciki wasa wasa yanzu abun ya zama babba"

"Subhanallah tun yaushe?"

"Ta 'dan jima yanzu bata da lafia ai, zaki bini muje?"

"Eh bari in kira Jabeer"

Kiran Jabeer nayi na fa'da mishi sannan muka tafi.

Muna isa asibitin muka iske Ummi tana ta safa da marwa, tambayar ta ya jikin Ameerahn mukayi, kuka ta fashe da shi tana cewa

"Yaya na rasa me ke damun Ameerah, ciwon ciki yaqi ci ya qi cinyewa, Yanzu dai tana can likitoci suna kanta"

Wata nurse ce ta zo ta ce likita ya ce Ummi tazo, muma bin ta mukayi a baya, muna shiga 'dakin mu ka ga Ameerah a kwance se likitoci guda biyu 'daya mace 'daya namiji, macen ta riqe ma Ameerahn hannu, da ka ga Ameerah kasan cewa tana cikin ciwo sosai, sannu mukayi ta mata, Umma taje kusa da ita tana ta yi mata sannu, likitan namiji ne yace ma Ummi

"Mun yi bincike mun gano akwai abunda ta sha wanda a sanadiyar shi mahaifarta ta samu matsala"

Salati Umma da Ummi suka fara yi, likitan ne ya cigaba da cewa

"Munyi munyi da ita ta fa'da muna me ne ne amma tace ita ba abunda ta sha, To qila ku zaku iya tambayar ta"

Ummi ce ta isa gurin Amerahn tace mata

"Ameerah me kika sha?"

"Babu komai " Ameerah tace qasa qasa

Ran Ummi 'baci yayi se ta fara masifa tana cewa

"Dan ubanki bazaki fa'da muna ba, se wahala kawai kike yi muma bamu huta ba"

Umma ce tace

"To wai a hakan zata fa'da miki kina ta masifa?"

Likitocin ne suka ce a bi a hankali, fita sukayi suka bamu wuri, Umma ce tace ma Ameerah

"Ameerori nah, bakya so kiji sauqi ne?"

Cewa tayi

"Ina so Umma"

Hawaye ta fara yi, Umma nata share mata hawaye tace mata

"To kiyi haquri ki fa'da muna dan Allah"

"Umma wani magani ne wanda Salma ta bani"

Ummi ce tace

"Maganin me ne ne?"

Kuka take ta yi tana cewa

"Ummi maganin mallaka ne tace mun, tace mun kayan mata ne wanda wata mata take siyarwa, tun ina gidan Maheer ta bani shi, cewa tayi in ina shan shi kullum kafin in kwanta Maheer ze ji duk duniya babu wadda yake so se ni"

Kallon juna muka fara yi ni da su Umma sannan Ameerah ta cigaba da cewa

"Kullum da daddare se na sha shi saboda ina so in mallake Maheer, sanda nayi miscarriage na daina shan shi, da Salma tazo na fa'da mata kamar maganin ne ya sani miscarriage se tace mun ai bashi bane, sannan ta qara ha'da mun da wani ta ce in cigaba da shan su, sanda Maheer ya sake ni se da mukayi fa'da da ita sosai se tace mun ai sakaci na ne sabida bana sha sosai, ce mun tayi inyi qoqari in cigaba da sha hakan ne ze sa Maheer ya maida ni, duk nasha maganin se ciki na ya mur'da, wasa wasa se ya fara saka mun ciwon ciki shine har abun yayi yawa yanzu, wallahi Ummi ban san maganin yana da illa ba"

Tana gama fa'din haka ta sake fashewa da kuka, jikin mu duk se yayi sanyi, qarfin hali nayi nace

"To yanzu ya za'a yi Salma tazo nan? So nake yi tazo ta fa'da muna dalilin da yasa maganin ya cutar da ke"

Ummi ce tace

"To wai Salman ma uwarta ce da zata dinga bata magani tana sha, in maganin mallaka ya akayi baki mallake Maheer 'din ba, 'yar uwar ki ta yarda kin auran mata miji amma da yake ke muguwa ce shine zaki mallake shi ke ka'dai, To yanzu wa gari ya waya? kin cuci kanki Ameerah"

Kuka Ameerah take yi sosai, ce mun tayi

"Tasneem dan Allah ki yafe mun, haqiqa na cutar da ke cutarwa me girma, na rabaki da mijin ki, na raba ki da farin ciki, ki yafe mun Tasneem, ni ce silar rugujewar farin cikin ki"

Ummi tace

"Au wai banda maganin mallakan da kike sha kina nufin ke ce silar da Tasneem ta bar gidan ta?"

Ameerah ta sake fashewa da kuka  tace

"Dan Allah ku yafe mun, wallahi Ummi duk magungunan da Salma take ansowa a zuba ma Maheer a abinci ban ta'ba zubawa ba, na zubar da su gaba 'daya, da munafurci da kisisina na fitar da ita a gidan ta, na dai amsa maganin amma ban zuba ba wallahi, na mallakan ka'dai nake sha wallahi"

Cewa nayi

"Ameerah kenan, To ai ko munafurcin ma da kisisinan ba shi ya fitar dani ba"

Umma ta kuwa tana jin hakan ta kalle ni tace

"To me ya fitar dake?"

Cewa nayi

"Maheer ne ka'dai ze iya yi muku bayani Umma"

Umma tace

"Ke me yaci bakin ki?"

Kafin kace me magana ta fara zama babba, kiran Abba da Maheer akayi a waya suka zo, sannan aka kira Mama mahaifiyar Maheer itama tazo, Maheer ne yayi musu bayani kamar yadda ya mun bayani shi da su Fadeelah, babu wanda be yi mamakin abunda ya faru ba hatta da ita Ameerahn.

Hadarin da ya ha'du ne da na gani yasa nace zan koma gida, kuma nasan cewa Noorie ta kusa dawowa, Abba ne yace dole za'a kira Salma tazo ta yi bayani amma se ina nan saboda maganar ta shafe ni, ce musu nayi zan tambayi izini zuwa gobe se inzo duk da nasan da qyar Maa ta bari in fita, da sauri na fito daga asibitin na shiga mota na kama hanyar gida.

Anjo wajan, Lallai Ameerah tana cikin tsaka me wuya, Allah dai ya bata lafia.

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now