29

354 51 13
                                    

Yau ko da naje gidan iyaye na na samu su Abba, Umma, Ummi, Maheer da Ameerah ana ta shari'a, se bayan la'asar suka gama case 'din kuma tinda na zo ake yin shi, Ameerah ce tayi yaji ta zo gida shine Ummi ta sa ta a gaba suka zo gidan mu wurin Abba tinda su mahaifin su ya rasu, qarar Maheer ta kawo akan ya daina kula da ita, kullum wulakanci yake mata, shi kuma Maheer 'din yace Ameerahn bata da aiki se na yawo kullum tana tare da qawayen ta kuma ta cika qazanta, fa'da sosai Abba ya musu sannan ya bashi haquri akan yayi haquri da irin halin da Ameerah ta ke yi mai, Abba na dattijon arziki ne saboda na ga qoqarin shi na tsaya sasanta su bayan dik irin abubuwan da su ka yi mun, ni tuni na manta da abunda sukayi mun saboda na da'de da yafe masu, tinda Ameerah ta yi 'bari har yau bata qara samun ciki ba, tausayin Maheer nake ji saboda yadda yake son yara har yau bai samu ba, a lissafe yanzu mun kai shekara 3 da yin aure ni da Maheer, wannan shine abunda nake fa'da mai na komai lokaci ne.

******Zazzabi me zafi ya rufe ni, Tin jiya nake ta fama da zazzabi da amai, yanzu haka ina cikin bayi na zauna gefen Bath Tub, amai na gama wanda ya galabaitar dani, Adeel ne ya shigo toilet 'din ya iba ruwa ya wanke mun fuska sannan ya zuba mun ruwa a baki na kuskure shi, 'dauka na yayi cak be aje ni ko ina ba se a kan gado, lullube ni yayi saboda irin sanyin da nake ji, zama yayi akan gadon sannan ya 'dauki kai na ya 'daura a kan cinyar shi, cewa yayi dani

"Sweetheart ciki gare ki fa"

'Dago kai na nayi na kalle shi sannan nace

"Ciki fa kace?"

"Eh ciki, na da'de ina kallon ki ai, ni likita ne kuma dole in gane kina da ciki, Allah ya sauke ki lafia Baby nah"

Hawaye na fara yi sannan nace

"Ashe ina da rabon haihuwa a duniya, Allah Nagode maka "

"Me ne ne abun kuka kuma sweetheart, ai farin ciki za muyi, zan kai ki asibiti anjima in sa ayi miki test se ki qara ganin tabbaci kinji"

"Toh Darling Nagode, sannu da dawainiya tin 'dazu kake ta kula dani"

Murmushi yayi ya rungume ni sannan yace

"In ban kula da ke ba da wa zan kula, Baby na ne ke wahalar da ke ai"

____________________________
Na rasa me ke damu na saboda yau tinda na tashi hankali na ba a kwance yake ba, jiki na yana ta bani wani abu ze faru, ko da na gaya ma Adeel se yace inyi ta addua, tinda na shigo wata na 9 da haihuwan nan se gaba na yayi ta fa'di, jiya ko da naje yi ma Zahrah barka se da Umma ta lura da yanayin da nake ciki, cewa tayi tin last month ranar sunan Siyama da muka ha'du take lura dani, addua kawai nake yi a cikin zuciya ta na Allah ya kare mun zuri'a ta, can dai se na 'dauki waya ta, Haajarah na kira dan ta 'debe mun kewa saboda Adeel ya fita, waya mukayi ta yi da Hajarah muna ta hirar duniya nan take fa'da mun Hafsah zata yi aure amma ba a riga an sa rana ba, da'di naji mata sosai saboda dik ita ce bata yi aure ba a cikin mu.

Adeel be dawo ba se da yamma, bayan ya ci abinci yayi wanka se muka je waje shan iska, kiran shi aka yi a waya inji wani a asibitin su, bayan ya gama wayar se yace

"Sweetheart, tafiya ta kama ni, gobe zan je Abuja amma a goben zan dawo"

'Bata fuska nayi nace

"Ni gaskia bana so kayi tafiyar nan, yanzu in ka tafi ya ka ke so inyi"

"Karki damu ai a goben zan dawo"

"In kuma baka dawo ba fa?"

Dariya yayi yace

"In ban dawo ba ki kula mun da kanki da baby na kuma ki fa'da mai ina son shi"

Dariya nima nayi nace

"Zaka dawo ma ai Inn Sha Allah "

Shiru mukayi gaba 'daya can kuma se yace

"In kika haifi namiji Al-Amin nake so a sa ma babyn?"

Ce mishi nayi

"In kuma mace ce fa?"

Se ya tsaya yayi tinani se kuma yace

"Ke zaki zaba da kanki"

Cewa nayi

"Hafsah za'a sa mata se a kira ta Noorie"

Dariya yayi yace

"Lallai dai kam wato irin suna na kenan"

____________________________
Da safe na taya shi ya shirya sannan na rako shi bakin mota, sallama nayi mai sannan nace

"Ka kula da kanka darling, zanyi missing 'dinka"

"Qila kafin in dawo ma se dai a kira ni ace kin haihu"

Dariya nayi nace

"A'a nafi so kana nan, nasan in kana nan bazan ji zafin haihuwar ba"

Cewa yayi

"Ke dai kin cika tsoro, Baby bari inje nayi latti"

Rungume shi nayi shima ya rungume ni, mun kai minti 2 a haka sannan ya sake ni, cewa yayi

"Wannan qaton cikin naki ai se ki ture ni qasa in fa'di"

Dukan shi nayi a kirji sannan muka kwashe da dariya, Haka dai mukayi ta tsokanar juna har ya tafi.

*****Cikin bacci naji waya ta tana ringing, Ina 'dauka se muryar naji Umma ta ce mun

"Kizo ki bu'de mun qofa ina waje"

Da mamaki na je na bu'de mata qofa, ni dai nasan ba muyi da ita zata zo ba, bayan na gama dafa ma Noor abinci ne bacci ya kwashe ni, Ina bu'de mata qofar se na ganta a tsaye, cewa tayi dani

"Saka hijab 'dinki ki zo muje, tare muke da Abban ki"

Ce mata nayi

"Lafiya Umma?"

"Asibiti zamuje a duba ki"

Da mamaki nace

"A duba ni kuma? Ai lafiya ta qalau ni"

Nan dai naje na 'dakko hijabi na amma ina ta tinani a rai na, a haka dai na bi su amma dik banji da'din yadda na fita ba ban tambayi izini ba.

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah ❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now