19

370 53 11
                                    

Kwanan mu 3 a asibiti sannan aka sallame ni, Abba na ne yayi komai da komai, yanzu haka muna cikin motar Abba ni da Umma muna jira Abba ya amso sauran magani na se mu tafi, bayan 'dan lokaci ka'dan se ga Abba yazo, shiga gurin zaman driver yayi ya zauna, yau shi ke jan mu be zo da driver 'din shi ba, yana zama ya ce ma Umma

"Ga maganin nata dan Allah ta daure ta dinga sha"

"Toh Inn Sha Allah " ta amsa mishi da shi sannan ya rufe qofar motar ya fara tuqi, Bamu tsaya a ko ina ba se a qofar gidan mu, nayi missing zuwa gida saboda rabo na da gida ya kai 2 month, kullum inna tambaya Maheer se yace na cika yawo, muna shiga cikin harabar gidan bayan me gadi ya bu'de muna gate se ga Zahrah da Siyamah sun fito da saurin su, Ummin Ameerah kuma na biye da su a baya, bayan sun rungume ni suna ta jinda'din gani na se Zahrah tayi saurin shigewa ciki, can se ta fito ta tsaya a bakin qofa ita ma Siyama ta tsaya a 'dayan bangaren qofar, ha'da baki sukayi a tare suka ce

"Welcome Home Ukhtieey"

Mamaki abun ya bani se na fara dariyar abun, su Umma da Abba ko se murmushi suke yi, muna shiga parlor se muka ga sunyi decorating 'dinshi da candles da balloons, A tare duka Umma da su Zahrah suka fara cewa

"Welcome Home!!!!!"

Hawayen jinda'di kawai na fara yi, Zahrah tazo tayi sauri ta goge mun hawaye sannan tace

"No Ukhtieey, This is not the time please"

Jana sukayi su kai ni wurin dining, kallon table 'din nayi na ga su samosa, spring rolls, shawarma, cupcakes, meat pie, fruit juices, ice cream, da dai sauran su, sannan zahrah ta bu'de mun warmers na ga su fried rice, party jollof rice, shredded meat sauce, crispy chicken, coleslaw, macaroni salad, onion soup da dai sauran su, suna cikin nuna mun ne kawai muka ji muryar su Mama da Fadeelah suna cewa "Welcome Home dear" waigowa nayi na kalle su, Fadeelah ce dauke da cake a hannun ta,cake 'din ya ha'du u, Sky Blue ne se akayi mishi sprinkling abubuwa a saman shi, wurin dining 'din su ka zo suka same su, baki na ya kasa rufuwa saboda da'di, yau ina cikin farin ciki wallahi, qara kallon birthday cake 'din nayi na ga an rubuta "Welcome Home Tasneem" wani irin da'di naji da baya misaltuwa,
Fadeelah ce tace

"Someone needs to shower!!"

Kwashewa mukayi da dariya sannan na tuna cewa daga asibiti na dawo kuma nasan definitely dole inyi warin asibiti, 'dakin su Zahrah na nufa dan inyi wanka, a jikin qofar 'dakin na ga an rubuta

"Dear Tasneem, kindly go to your former room please"

Abun mamaki da dariya ya bani, wai me mutanen gidan suke shiryawa haka ne, jinda'din ai yayi mun yawa, sun sa na manta duk damuwa ta, 'daki na da nake kafin inyi aure na nufa, ina shiga naga abunda ya tada mun da hankali, mamaki ne ya kusa kashe ni, cewa nayi

"Hafsah!! Hajarah!! , Innalillahi, wai dama kuna cikin gidan nan"

Dariya suka fara yi sannan su ka ce "Welcome Home Our Besty"

baki na ya kasa rufuwa saboda mamaki, cewa na qara yi

"Hajarah ba Kano a ka kai ki ba, ke kuma Hafsah ba kinje wurin Hajia a Zamfara ba, To how comes na ganku anan"

Dariya suka fara yi nan suka shaida mun jiya suka zo saboda Zahrah ta gaya masu komai, su ma sunzo saka ni farin cikin da na dade ina buqata ne, still ban gamsu ba dik da abun yayi mun da'di, sake cewa nayi

"Alright Alright naji , Hafsah kin dawo naki me sauqi ne amma ke kuma Hajara ya aka yi mijin ki ya bar ki bayan kwanan ku uku da aure"

Dariya sukayi ta yi sannan suka ce inje inyi wanka inna fito in aka gama celebration din zasu fa'da mun, toilet na shiga dan yin wanka, bayan na fito se na ga basa cikin 'dakin, kayan da aka aje mun a kan gado na 'dauka na saka, gyara fuska ta nayi ka'dan, ban rame sosai ba gaskia amma na chanja, kallon madubi nayi na ga yadda rigar ta mun kyau, Sky Blue ce Amma tana da zane royal blue, rigar se walqiya take yi tayi kyau sosai MashaAllah, sauri nayi na gama shiryawa sannan na fita na je na same su a parlor, duk sun zauna suna ta jira na, nan dai akayi ta shagali, Lallai yau naji da'di sosai, bayan an gama komai su Mama da Ummi sun tafi gida, gidan ya rage da ga en gidan mu se Hafsah da Hajarah, ce mun sukayi ai sleepover suka zo yi, da'di na dinga ji, bayan anyi sallar isha'i, Muna zaune akan gado a 'daki na ana ta hira ne Hafsah tace hajiya wato kakar ta da kanta tace ta dawo Kaduna saboda ni, ita kuma Hajara tace mijin ta ya ga damuwar da ta shiga saboda bata san abunda ya faru ba se washe garin randa aka kaita, yau suka zo ya kawo ta amma gobe zasu juyo da safe, godia nayi ta musu sannan mukayi ta hirar mu cikin nisha'di, ba muyi bacci ba se qarfe 1 na dare, hatta da su Zahrah a 'dakin su ka kwana, wasu a akan gado wasu a qasa kan center carpet.

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah❤️❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon