17

346 56 0
                                    

A hankali nake bu'de ido na sakamakon dishi dishi da nake gani, can dai na bude idon gaba 'daya, inda nake na bi da ido ina ta kallo, wurin yayi kama da asibiti, muryar Zahrah naji tana cewa

"Sannu Ukhtieey, kin tashi bari in kira Umma"

Ido na bita dashi ita ma ina kallon ta, tashi tayi ta fita dan ta kira Umma, ba su dade ba se gata ta shigo ita da Umma da Ummi, a tare suka yi ta mun sannu, su ma kallon su kawai nake yi ina 'daga masu kai, samun guri Ummi da Zahrah su ka yi su ka zauna yayin da Umma ta matso kusa dani tana shafa kai na, ba'a jima ba se ga Mama da Fadeelah sun shigo, suna ta yi mun sannu, Maheer ma shigowa yayi kamar mara gaskia ya tsaya a baya yana kallo na, can dai ya bu'de baki yayi mun sannu inda ni kuma na bishi da ido, Mamar shi ta katse shirun tare da cewa

"A haka zaka gaida matar ka, ka matsa kusa da ita mana"

Cewa yayi da ita

"Ai na gaida ta Mama, Allah ya qara sauki"

Ummi Maman Ameerah tace

"Ai ba ze iya matsawa kusa da ita ba tinda ya san ya zalince ta"

Mama ce ta ce mata cikin mamaki

"Wani irin zalinci kuma?"

Se ta juya ta kalli Maheer ta ce mai

"Uban me kayi mata?"

Zahrah ce tayi saurin cewa

"Sakin ta yayi"

Mama ta juya ta kalli Maheer tace

"Saki? Wani irin saki? Ban gane ba fa"

Umma ce ta ce mata

"Gaskia ne Hajia Khadija, yanzu Tasneem ba matar Maheer ba ce ya sake ta, nima Ummin Ameerah ce ta zo ta same ni a gida ina zaune ta shaida mun wai Ameerah ta gaya mata Maheer ya saki Tasneem, hankalin ta a tashe tazo ta same ni, ana cikin haka se ga kiran waya wai Tasneem tayi hatsari shine na kira ki na shaida miki"

Salati Mama ta fara yi, baya baya tayi kamar zata fa'di, Fadeelah ce ta tashi ta kama ta ta zaunar da ita, cewa ta fara yi

"Maheer ka cuce ni, me yarinyar nan tayi maka ka sake ta, Haba Maheer Haba Maheer"

Hawaye ta fara yi, yayin da Maheer ya fara bata haquri, se a sannan naji hawaye sun fara zuba a ido na, Mama ta qara kallon Maheer tare da fa'din

"Na umurce ka da ka maida ta 'dakin ta yanzu yanzun nan"

Saurin cewa nayi

"A'a Mama ki barshi dan Allah, ni ce na ce ya sake ni "

Ummi ce tace

"Qarya kike yi wallahi Tasneem, Ameerah ta shaida mun fa'da kuka yi da ita har ya sake ki, ita ma munafukar da ta fa'da mun ta 'dauka zan goyi bayan ta ne, bata san cewa ni 'daya na 'dauke ku ba, yadda nake son ta haka nake son ki"

Nurse ce ta shigo 'dakin tare da cewa

"Dan Allah ku 'dan fita waje ku tsaya, kuna damun patient din mu da surutu gashi kuma kunyi yawa a 'dakin"

Maheer ne ya fara ficewa a 'dakin tun kafin nurse 'din ta gama magana, kowa fita yayi Ummi ka'dai aka bari a 'dakin ita da Zahrah, haquri ta dinga bani tana shafa kai na

Bayan kamar minute 10 se ga Doctor ya shigo, cewa yayi

"Sannu Malama Tasneem"

Amsa mai nayi da "yauwa" , gaisawa sukayi da Ummi da Zahrah sannan yace,

"Dan Allah ina so in ga mijin ta in da hali har da mahaifiyar ta domin ina so in basu haquri"

Ummi ta kalle shi sannan ta ce ma Zahrah taje ta kira su Maheer da Umma, bayan ta fita se kuma ta dawo tare da su Mama duka, Doctor ya kalle su duka sannan yace

"Duka wa'dannan zan iya magana a gaban su ko?

Mama ce tace

"Kayi maganar ka likita saboda ko shi mijin nata da ka aika kira tsohon mijin ta ne"

Maheer na kalla shi kuma sauri yayi ya duqar da kanshi qasa, Doctor ya fara magana tare da cewa

"Ina so in baku haquri game da buge 'yar ku da nayi da mota ta, na fito ina ta sauri kuma ina waya kasancewar ina da patient 'din da aka ce mun rai a hannun Allah yake, kafin in ankara kawai se naji na buge ta, ko da na kawo ta asibiti ta riga da ta suma, kuyi haquri dan Allah dan a sanadiyyar buge ta da nayi har cikin da ke jikin ta ya zube"

A tare duka en dakin suka ha'da baki ciki har da Maheer tare da fa'din

"Ciki!!!"

Tashi nayi da sauri nima ina zaro ido, Doctor ne ya ce

"Dama baku san ta na da ciki ba?"

Mama tace

"Wallahi likita ba mu sani ba"

Sannan ta kalle ni tace

"Tasneem dama ciki gare ki?"

Kuka na fara yi ina cewa

"Wallahi Mama ban san ina da shi ba"

Ummi ce ta riqe ni tana ta bani haquri, Maheer ne yace

"Nima ban san tana da ciki ba wallahi"

Wani mugun harara Mama ta watsa mai tare da fa'din

"Ko ka sani ko ba ka sani ba kai kayi sanadiyyar rasa shi tinda da baqin cikin ka ta fito har mota ta buge ta, da baka sake ta ba zata fito ne har tayi hatsarin munafiki kawai marar hankali"

Umma ta sa baki tana ta bata haquri dan Mama tayi fushi da Maheer sosai, dan qarshe ma cewa tayi ya wuce bata son ganin shi a cikin asibitin, jikin shi a sanyaye ya fita daga 'dakin, Doctor ma haquri ya qara bamu tare da fita.

Don't forget to vote, share and comment

Dedicated To Chuchujay ❤️

Ameerori❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora