24

382 54 16
                                    

Bayan an sallame mu da la'asar se Maheer ya aje ni a gida su kuma suka wuce, Ina shiga gida na samu su Zahrah da Siyamah da Abba a zaune a parlor, gaisawa mukayi da su sannan suka tambaye ni ya jikin ita Ameerahn, bayan dai mun gama gaisawa da su na shige 'daki, wanka nayi sannan nayi Sallah, kwanciya nayi akan gado dan in huta, Zahrah ta shigo ta same ni, tambayar ta nayi

"Wai ina Umma ne?"

Cewa tayi tana toilet, Amma dai tasan ya isa ace ta fito, a haka dai muka yi hira, Zahrah tace akwai abinci, da yake ban jin yunwa se nace mata se dai zuwa anjima saboda banjin yunwa yanzu.

_____________________________
A haka dai rayuwa ta cigaba, yau sati uku kenan da haihuwar Ameerah, Ina zuwa akai akai ina gaida ta, sallahn isha'i na idar sannan na shiga toilet nayi wanka na sa kayan bacci, yau nayi aiki sosai da rana na gaji sosai, har bacci ya fara kwashe ni se ga kiran Dr Adeel ya shigo waya ta, bayan mun gama gaisawa yace yau baze je hospital ba ze huta a gida, cewa nayi da shi na san cewa yau yana tare da su maman su kenan, shiru naji yayi sannan ya ce

"Ai mahaifiya ta bata da rai haka ma mahaifi na"

Da tausayi na ce

"Wayyo Allah Sarki, Allah ya musu rahama"

"Ameen" ya amsa mun da shi sannan na sake tambayan shi

"To da kai da wa ka ke zama?"

Cewa yayi

"Ni ka'dai nake zama a gida na"

Da mamaki nace

"Kai ka'dai kuma?"

Dariya yayi yace

"Kinyi mamaki ko?"

Sannan ya cigaba da cewa

"Ya kamata in baki labari na, kin cancanci kisan tarihi na"

Cewa nayi

"Eh in dai babu damuwa ina so in sani"

Gyaran murya yayi sannan ya fara da cewa

" Suna na Adeel Aminu Ismail, ni maraya ne ina da shekara uku mahaifi na ya rasu, en uwan mahaifiya ta basu da qarfi talakawa ne, su kuma en uwan mahaifi na se suka danne dukiyar da mahaifi na ya bari, en uwan mahaifi na ba sa son mahaifiya ta saboda sun so ya auri er uwa shi shi kuma yaqi, a Adamawa ya ha'du da mahaifiya ta sanda ya je karatu, har sukayi aure en uwan shi ba sa son ta, bayan ya rasu se qiyayyar da suke mata ya qaru, gidan da muke ciki ka'dai suka bar mata, lokacin da na isa shiga makaranta mahaifiya ta ba ta ku'di, nan ta je ta same en uwan mahaifi na ta kai kukan ta gare su, wulaqanta ta sukayi sannan suka koreta, nan mahaifiya ta ta je ta 'dinga yawon neman inda zata samu aikatau, a haka har tayi dace ta samu wani gidan masu ku'di, a matsayin me wanki suka 'dauke ta, nan ta dage ta dinga wanki har ta samu ku'din da zata sani a makarantar boko da islamiya.

Ni yaro ne me hazaqa haka yasa mahaifiya ta ta dage tana ta neman ku'di saboda ta cigaba da biya mun ku'din makaranta, wata lokaci in bamu da abincin ci mahaifiya ta ke haqura ta bar mun wanda muke da ita kuma ta haqura, in kuma ta samo abinci a gidan da take aiki se muci tare, mahaifiya ta ta sha kwana da yunwa saboda ni, dik irin talaucin da muke ciki ban taba kwana da yunwa ba, mahaifiya ta ta nuna mun gata sosai, sanda na kai shekara goma mahaifiya ta ta roqi wani me chemist da ya dinga bari ina zama a shagon shi ina taya shi wasu ayyukan, kullum in zan tafi se ya bani 300, da wannan ku'din muke samu muna cefane ita kuma mahaifiya ta ku'din da take samu shi take tarawa tana biya mun ku'din makaranta, sanda na kai matakin rubuta jarabawar gama primary hankalin mahaifiya ta ya tashi saboda ku'din da yake hannun ta ba ze isa ta biya mun ba, neman aiki ta dinga yi, a haka har ta samu wani aikin iban qasa a haura da shi sama a zuba ma masu gina gida, tayi aikin har na tsawon kwana uku, a rana na hu'du ne ta tashi da zazzabi amma a haka da daure ta ce zata je yin wannan aikin, ni na rakata sannan na tsaya ina jiran ta, ina kallon ta ta iba qasa ta haura saman bene, sawu biyu tayi tana qoqarin kai na uku kenan na ga jiri ya 'dibe ta ta fa'do qasa, da gudu na je na same ta, mutane suka zagaye ta ana duba lafiyar ta, ni ko kuka kawai nake ta yi saboda hankali na ya tashi sosai, mutane suka taimaka aka kai ta asibiti"

Kuka kawai nake yi saboda Dr Adeel ya matuqar bani tausayi, cewa yayi

"Haba My Love, ki daina kuka mana, bana so inji kina kuka, gaskia to zan daina baki labarin"

Cewa nayi

"Duk wanda ya ji labarin nan se ya tausaya maka wallahi, To bayan an kai ta asibiti se me ya faru"

Cewa yayi

"Se na auri Tasneem"

Dariya nayi shima se ya fara dariya sannan yace

"Dama dariyar ki nake so inji, ban so in ga kina kuka"

Murmushi nayi na share hawaye na sannan nace

"To ka cigaba da bani labarin mana"

Cewa yayi

"Wallahi na fara jin bacci Ukhtieey, amma gobe zan cigaba da baki labarin"

Banji da'din rashin jin qarshen labarin shi ba amma se nayi mai uzuri nace

"To Allah ya kaimu goben lafia Dr"

Se kuma yace

"Adeel dai, ki kirani Adeel"

Se nace mai

"A'a sai dai in ce Akhieey tinda ni ma Ukhtieey ka ke ce mun"

Dariya yayi yace

"Toh Shikenan Ukhtieeyn Akhieey"

Ni kuma se nace

"Yauwa Akhieeyn Ukhtieey"

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah ❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now